Wani mai goyon bayan ƙungiyar kwallon kafa ta Asante Kotoko, ɗaya daga cikin manyan ƙungiyoyin ƙwallon kafa a Ghana, ya mutu bayan daɓa masa wuƙa da aka yi a wani wasa da ƙungiyarsa ta buga da ƙungiyar Nsoatreman.
An kashe Francis Yaw Frimpong, wanda aka fi sani da Pooley, ne bayan wata zazzafar gardama ta kaure tsakanin shi da wani mutum da ba a san ko wane ne ba a lokacin da ake buga ƙwallon, a cewar sanarwar da Nsoatreman ta fitar.
''Asarar rai ba gaira ba dalili abu ne maras daɗi,'' in ji ƙungiyarsa ta Asante Kotoko.
Rikice-rikice a filayen ƙwallon ƙafa batu ne da ke cigaba da zama matsala a Ghana inda a 2001, wata tarzoma da aka samu a Accra, babban birnin ƙasar ta yi sanadiyyar kashe mutane aƙalla 120.
A wasan ranar Lahadi a birnin Nsoatre ma an samu rikicin magoya baya inda mutane ke ta jefa abubuwa cikin filin.
Lamarin ya tsananta a lokacin da ƴan kallo suka kutsa cikin filin suka kai hari kan ƴan wasa da jam'ai.
Ƙungiyar ƙwallon kafa ta Asante Kotoko ta ce mai tsaron gidanta, Mohammed Camara ya fuskanci cin zarafi daga mutanen da suka kutsa cikin filin wasan lokacin da ake rikicin.
An cigaba da wasan bayan zuwa hutun gajeren lokaci inda ƙugiyar Asante Kotoko ta yi rashin nasara a hannun Nsoatreman bayan da aka tashi 1-0.
Ƙungiyoyin biyu sun yi allawadai da rikicin da aka samu.