An kafa kwamitin da zai laluɓo hanyar gudanar da zaɓe a Libya

Asalin hoton, Getty Images
Shirin tallafawa ƙasar Libya na Majalisar Ɗinkin Duniya ya ce ya kafa kwamitin da zai nemi hanyoyin warware takaddamar da ke kawo tsaiko wajen gudanar da zaɓukan da aka daɗe ana jira.
A shekarar 2021 ne ya kamata a ce an gudanar da zaɓukan ƙasar, sai dai an yi watsi da shirin saboda takaddamar da aka riƙa yi a kan cancantar ƴan takara.
Ana dai fatan zaɓen zai taimaka wajen kawo karshen rikicin da aka shafe fiye da shekaru 10 ana yi a ƙasar, wanda gwamnatoci da ke gaba da juna a gabashi da yammaci ke ruruta wa.
A makon gobe ne kwamitin zai yi ganawarsa ta farko a birnin Tripoli.


















