Ƴantawayen M23 sun tsagaita wuta a Congo
Ƴan tawayen M23 da ke samun goyon bayan Rwanda da suka ƙwace iko da birnin Goma na Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo sun sanar da tsagaita wuta daga yau Talata.
Ƴan tawayen sun ce za su tsagaita buɗe wutar ne saboda dalilai na jin ƙai.
Sun kuma bayyana cewa ba su da shirin ƙwace wani yanki nan gaba a Congo.
Majalisar ɗinkin duniya ta ce gawarwaki 900 aka tattaro a kan tituna Goma a makon da ya gabata.
Ƙungiyoyin kare haƙƙin dan'adam sun dade suna kira ga Rwanda da ta janye goyon bayan da take bai wa ƴantawayen, suna masu cewa dubun dubatar mutane ne suka rasa muhallansu.