Argentina tana korafin ta samu fenariti, Argentina 1-1 Cape Verde
Amma dai alkalin wasa ya tuntubi masu kula da VAR sun tabbatar masa da laifi a wajen, an kuma ci gaba da wasan.
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Mohammed Abdu tare da taimakon A1
Amma dai alkalin wasa ya tuntubi masu kula da VAR sun tabbatar masa da laifi a wajen, an kuma ci gaba da wasan.
An maye gurbin Facundo Medina da Nicolas Tagliafico.
Yan wasan Argentina biyu suna kwance, Facundo Medina da Enzo Fernandez, amma dai kamai Medina ba zai iya ci gaba da wasan ba.
Rodrigo De Paul ya fita an maye gurbinsa da Leandro Paredes.
Ta saka Willy Semedo da Hélio Varela sun maye gurbin Ryan Mendes da kuma Jovane Cabral.
Bugun tazara da Messi ya yi, kwallon ya bugi katangar da yan wasa suka yi, magoya bayan Cape Verde su 560,000 sun nunfasa, sun san cewar da ta wuce komai zai iya faruwa.
Ta fitar da Laros Duarte da Nuno da Costa ta maye gurbinsu da Jamiro Monteiro da kuma Dailon Livramento.
An kammala hutun shan ruwa, an kuma ci gaba da wasan.
Za a karasa shi, idan ba ci mu je karin lokaci na minti 30, kowanne zango minti 11.
Idan sakamakon bai canja ba muje bugun fenariti.
Tawagar Ingila za ta kara da ta Mexico a wasan zagaye na yan 16 da karfe 01:00 BST a ranar Litinin kamar yadda Fifa ta bukaci dage wasan,
Fifa ta tattauna da tawagogin kwallon kafa na Ingila dana Mexico a ranar Juma'a bayan da ta ba da shawarar a dage wasan zuwa 19:00 BST a ranar Lahadi (12:00 agogon gida).
Hasashen yanayi ya nuna cewa za a iya samun tsawa a wannan lokacin, kodayake Fifa ba ta bayar da wani bayani game da canjin da ta gabatar ba.
Majiyoyi sun shaida wa BBC Sport cewa Fifa ta shirya don yin canjin lokacin wasan da kuma tabbatar da sake tsara hakan a cikin wata sanarwa, amma labarin shawarar ya fusata jami'an Ingila da Mexico.
A sakamakon haka, yanzu za a buga wasan a Mexico City da karfe 18:00 agogon gida a ranar Lahadi.
Canji biyu ga Argentina - Lautaro Martinez da Thiago Almada sun fita an maye su da Julian Alvarez da Nico Gonzalez
Messi ne ya samu kwallo a cikin gidan Cape Verde ya kuma zura da ita a guje ya buga amma ta taba jikin gola, sannan yan baya suka fitar da ita,
Dama ce mai kyau da Messi ya samu.
Ƙwallo ce mai kyau ya ci, bayan da aka bashi daga gefen dama, yana daga cikin gidan Argentina ya buga da karfi da kafarsa ta dama ta kuma fada raga.
Wasan ya koma sabo kuma ana 1-1.
Mai tsaron ragar Agentina, Emi Martinez sai da ya kwanta ya samu damar tare kwallon da Laros Duarte ya buga masa mai hadari a cikin gidan Argentina.
Dama ce mai kyau da Cape Verde ta samu..
Nahuel Molina ya yi gudu sosai, amma bai samu isa ga doguwar ƙwallon da aka aika masa ba, domin ta yi masa yawa.
An kawar da kwallon da aka bugo daga bugun kusurwa na Cape Verde zuwa ga Jovane Cabral a bakin cikin gida, wanda ya gwada sa'arsa da buga kwallon da karfi, amma an karkatar da ita ta fita saman fili, an kuma bayar da bugun kusurwa, wanda Argentina ta sake fitarwa.
Cabral ya faɗi ƙasa bayan wani mummunan faɗuwa, amma da alama yana cikin ƙoshin lafiya.
Tun da aka koma wasan Argentina ke rike kwallon tana wasa tun daga baya zuwa gaba da gefen hagu da dama, amma ta kasa ratsa bayan Cape Verde, wadda ke buga wasan ba tare da tashin hankali ba ko kuma fargaba ba, duk da karon farko kenan da suke buga gasar kofin duniya a tarihii.
Kuma sun yi kokari a matakin karon farko da shiga gasar, amma tana buga wasa na hudu idan aka kirga da uku daga cikin rukuni.
Za a buga minti 45 sannan za a yi hutun shan ruwa daga nan a kammala karawar zagaye na biyu.
Idan Cape Verde za ta farke sai a je karin lokaci idan sakamakon bai canja ba mu je bugun fenariti.
Wasa uku ne ta kai ga bugun fenariti.
Messi ya kara kafa wani sabon tarihin.
Ya zama mai shekaru da yawa daga Kudancin Amurka da ya ci kwallo a zagayen ziri daya kwale a gasar cin kofin duniya mai shekara 39 da kwana tara.
Ya kara wannan tarihin da dan wasan tawagar Uruguay keda shi tun daga 1954 mai shekara 36.