Giggs: Carrick ya mayar da farin ciki ga magoya bayan Man United, Manchester United

Asalin hoton, Getty Images
Tsohon ɗan wasan Manchester United, Ryan Giggs, ya bayyana cewa magoya bayan ƙungiyar sun sake samun farin ciki da sha’awar kallon wasanni a Old Trafford tun bayan da Michael Carrick ya karɓi ragamar horaswar a kungiyar. .
Giggs ya ce duk da sallamar da aka yi wa dan kasar Portugal, Ruben Amorim, ya bar ƙungiyar a wani matsayi mai kyau da ya ba Carrick damar ci gaba da gina nasara a kai.
Manchester United ta samu sauyi sosai cikin mako 15 da suka gabata bayan ficewar Amorim. Matakin da shugabannin kungiyar suka bai Michael Carrick aikin rikon kwarya zuwa karshen kakar nan.
A ƙarƙashin Carrick, Red Devils ta haura zuwa matsayi na uku a jadawalin gasar Firimiya, inda nasarar da suka samu ta 1–0 a kan Chelsea a ranar Asabar ta ƙara ƙarfafa damar ƙungiyar na samun tikitin shiga gasar Champions Leaguea badi.
Rahotanni sun nuna cewa ƙungiyoyi biyar na farkon teburi a gasar za su wakilci Ingila a manyan wasannin zakarun Turai a kakar wasa mai zuwa.
Giggs, wanda shi ma ya taɓa zama kocin riko na Manchester United a ƙarshen kakar 2013/2014 bayan sallamar David Moyes, ya yaba da tasirin da Carrick ke yi cikin ɗan gajeren lokaci.
Ya bayyana fatan Carrick zai samu cikakkiyar dama a gaba, musamman ta fuskar shirin kakar wasa ta gaba da kuma zaɓen ’yan wasan da suka dace da salon wasansa.
Tun bayan barin Moyes, Manchester United ta sauya koci biyar. Amma Giggs ya jaddada cewa ko da Amorim ya bar aikin a yayin da ƙungiyar ke matsayi na shida, ya bar tubalin da ya ba sabon koci damar gina ƙungiya mai ƙarfi.












