Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 20/08/2025.

Rahoto kai-tsaye

Usman Minjibir da Ahmad Bawage da Ibrahim Yusuf Mohammed

  1. Ana tuhumar tsohon Firaministan Mali da wawushe duƙiyar al'umma

    Mali PM

    Asalin hoton, AFP

    Masu gabatar da ƙara a Mali na tuhumar tsohon Firaministan ƙasar, Choguel Kokalla Maiga, da wawushe duƙiyar al'umma.

    Mista Maiga na tsare a gidan yari zuwa lokacin kammala yi masa shari'a.

    Akwai kuma tsoffin abokan aikinsa tara da su ma suka gurfana a gaban kotun koli, inda aka gabatar da tuhuma kan mutum biyu, wasu kuma an wanke su.

    A makon da ya gabata aka kama Mista Maiga, kwanaki bayan gwamnatin soji ta kama gwamman mutane da ake zargi da yunkurin juyin-mulki a cikin sojoji.

    A watan Nuwamba aka soke shi daga mukaminsa bayan ya soki lokacin da aka tsara na mayar da mulki hannun farar-hula.

  2. Wane ne ɗan tsohon shugaban Boko Haram da aka kama a Chadi?

    Muslim Muhammad Yusuf

    Asalin hoton, Zagazola Makama/X

    Bayanai na ci gaba da fitowa kan kamun da jami'an tsaron Chadi suka yi wa Muslim Muhammad Yusuf, ƙaramin ɗan marigayi tsohon shugaban ƙungiyar Jama'atu Ahlis-Sunna Lidda'Awati Wal-Jihad, wadda aka fi sani da Boko Haram a Najeriya

    An kama Muslim Yusuf ne tare da wasu mutum huɗu da ake zargi da kasancewa mambobin ƙungiyar, a cewar Zagazola Makama, wani mai bincike kan ayyukan ƙungiyar Boko Haram a Tafkin Chadi.

    Makama ya ce hukumomin Chadi sun kama Muslim Mohammed Yusuf, ba tare da sanin ainihin wane ne shi ba, har sai da hukumomin leƙen asirin Najeriya suka sanar da su ta hanyar rundunar haɗin gwiwar ƙasashen Tafkin Chadi da ke yaƙi da Boko Haram, (MNJTF).

    Latsa nan don karanta cikakken labarin...

  3. Isra'ila na ci gaba da shirinta na mamaye Gaza

    Sojojin Isra'ila

    Asalin hoton, Reuters

    Kafar yaɗa labaran Isra'ila na cewa ƙasar na shirin gayyatar sojojin jiran ko-ta-kwana nan da makonni, gabanin shirinsu na kaddamar da cikakkiyar mamaya a zirin Gaza.

    Falasɗinawa miliyan guda ake sa ran an umarce su su fice da zaran an kammala shirya sabon matsugunai a nesa da kudancin Gaza.

    Ƙawayen Isra'ila da dama sun yi Alla-wadai da shirin na ta.

    Falasɗinawa sun ce ana cigaba da yi musu ruwan bama-bamai a yankunan birnin Gaza, yayin da iyalai da dama ke ta tserewa, wasu kuma sun maƙale.

  4. Buɗewa

    Masu bibiyar mu barkan mu da safiyar Laraba.

    Ku kasance da mu a wannan shafi domin samun labarai kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da makwaɓtanta da kuma sauran sassan duniya.