Ƙungiyar NATO ta jinjinawa ƴan Ukraine bisa jajircewarsu

Asalin hoton, Getty Images
Ƙungiyar tsaro ta NATO ta jinjina wa abin da ta kira ƙarfin halin ƴan Ukraine wajen kare ƙasarsu, bayan wata tattaunawa ta intanet da gamayyar hafsoshin sojojin ƙasashen ƙungiyar suka yi.
Shugaban kwamitin hafsoshin sojojin NATO, ya ce sun yi tattaunawa mai muhimmanci kuma sun nuna haɗin kai a ƙoƙarin su na samar da zaman lafiya mai ɗorewa kuma bisa adalci.
Wakilin BBC ya ce har yanzu Rasha na bayyana cewa ba za ta amince da aika dakaru daga ƙasashen NATO zuwa Ukraine ta kowace fuska ba.
Rashan ta kuma bayyana duk wata tattaunawa da ba a sanya ta ciki ba a matsayin 'taron shan shayi'

















