Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 21/10/2025.

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 21/10/2025.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Daga Aisha Babangida

  1. Nicolas Sarkozy ya fara zaman gidan yari na shekara biyar

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Tsohon shugaban ƙasar Faransa, Nicolas Sarkozy, ya fara zaman gidan yari na shekara biyar a gidan yarin La Santé da ke tsakiyar birnin Paris.

    An same shi da aikata laifin haɗa baki wajen samun kuɗaɗen yaƙin neman zaɓensa na shekarar 2007 daga tsohon shugaban Libiya, Muammar Gaddafi.

    Sarkozy ya musanta aikata laifin, kuma ya nemi a sake shi daga gidan yari yayin da yake neman ɗaukaka ƙara.

    Wani rahoton BBC daga Paris ya ce tsohon shugaban ƙasar ya shiga gidan yari yana mai alfahari, yana ganin wannan dama ce da zai yi amfani da ita don sake samun goyon bayan ‘yan ƙasa.

    Za a tsare Sarkozy, wanda yake da shekaru 70 a sashen keɓantattun fursunoni.

    A tarihin Faransa, shugabanni biyu ne kawai suka taɓa zuwa gidan yari kafin shi da suka haɗa da Philippe Pétain, wanda ya yi haɗin baki da Jamusawa a lokacin Yaƙin Duniya na Biyu, da kuma Sarki Louis na Sha Shida, kafin a kashe shi.

  2. NLC na barazanar shiga yajin aiki kan buƙatun ASUU

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Ƙungiyar ƙwadago ta Najeriya NLC ta bai wa gwamnatin Najeriya wa’adin makonni huɗu domin cika bukatun ƙungiyar malaman jami’a ta ƙasa ASUU, in ba haka ba, ƙungiyoyin kwadago su ma za su shiga yajin aiki na ƙasa baki ɗaya.

    Shugaban NLC, Joe Ajaero, ne ya bayyana haka a Abuja a jiya ranar Litinin, bayan ganawar da aka yi tsakanin shugabannin ƙungiyar da na ƙungiyoyin ma’aikatan jami’o’i da sauran manyan makarantu.

    Ajaero ya ce makonni huɗun da aka bayar na nufin bai wa gwamnatin ƙasar damar warware duk matsalolin da suka shafi ƙungiyoyin, ciki har da aiwatar da yarjejeniyar shekarar 2009 da aka yi da ASUU.

    Yayin da yake jawabi tare da sauran shugabannin ƙungiyoyin ilimi, Ajaero ya ce idan gwamnati ta gaza cika buƙatunsu, za su fara yajin aikin sai baba ta gani.

    Ya bayyana cewa wannan yajin aiki zai zama na haɗin kai da ƙungiyoyin ma’aikatan ilimi.

    A cewar Ajaero, idan gwamnati tana da gaskiya da niyya mai kyau, ana iya kawo ƙarshen duk wata matsala ta yajin aiki nan da nan.

    Sai dai ya gargadi cewa idan gwamnati ta ci gaba da raina ƙungiyar kwadago, to babu wani zaɓi illa su dakatar da ayyukan ƙasa baki ɗaya.

  3. An zaɓi Takaichi a matsayin mace firaminista ta farko a Japan

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayan zagaye na biyu na zaɓe, majalisar dattawan kasar Japan ta zaɓi Sanae Takaichi a matsayin Firaministar ƙasar, lamarin da ya tabbatar da samun nasararta a matsayin mace ta farko da ta hau wannan mukami a tarihin ƙasar.

    Takaichi ta samu ƙuri’u 125 a majalisar dattawa, abin da ake buƙata don samun rinjaye. Tun da farko kuma, ta samu ƙuri’u 237 a majalisar wakilai sama da adadin da ake buƙata na 233.

    Ana kiranta “Iron Lady” ta Japan saboda tsattsauran ra’ayinta na kishin ƙasa da goyon bayanta ga ra’ayoyin mazan jiya.

    Wannan rana ce mai tarihi ga wakilcin mata a siyasar Japan, inda ake ganin sauyi a hankali wajen bai wa mata dama a manyan mukamai.

  4. Yawan matan da ake kashewa a rikice-rikice ya ninka sau uku - MDD

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Wani rahoton Majalisar Ɗinkin Duniya ya ce dumbin mata ne aka fi ake kashewa a rikice-rikicen da ake fama da su a duniya.

    Rahoton na Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniyar kan Mata, ya ce yayin da duniya ke fuskantar tashe-tashen hankula mafi girma tun shekara ta 1946, lamarin yana haifar da hadari da wahalar da ba a taba ganin irinta ba ga mata.

    Sarah Doughlas, mai magana da yawun mata ta MDD ta ce adadin matan da aka kashe a yaƙe-yake ya ninka har sau uku a shekaru biyu da suka gabata, idan aka kwatanta da shekaru biyu kafin wannan lokaci.

    Sannan kuma cin zarafinsu ya ƙaru da kashi 87 cikin 100.

    Rahoton ya ce a yanzu mata ba wai suna buƙatar ƙarin wasu alkawura bane, face samun iko da kariya, da damar damawa da su.

  5. Assalamu Alaikum

    Barkanmu da sake saduwa a shafin labarai kai-tsaye na BBC Hausa a yau Talata.

    Shafin na yau zai fi mayar da hankali ne kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da maƙwabtanta, da kuma sauran sassan duniya.

    Za ku iya leƙawa shafukan sada zumuntanmu na intanet, da facebook da X da kuma whatsapp domin karanta sauran labarai da kuma kallon bidiyo.

    Ku kasance da mu.