Masu gangani sun bazama a titunan biranen Garoua da Yaounde na ƙasar Kamaru, inda suke neman hukumar zaɓe ta fitar da sakamakon zaɓen shugaban ƙasar daidai da yadda suka kaɗa ƙuri'unsu.
A ranar 12 ga watan Oktoba ne al'ummar Kamaru suka je rumfunan zaɓe domin kaɗa ƙuri'a a zaɓen shugaban ƙasa, karo na farko da aka samu zazzafar adawa a tsawon shekaru.
Sai dai tun bayan zaɓen ake ci gaba da zaman ɗarɗar, bayan artabun da aka samu tsakanin magoya bayan ɗan takarar adawa Issa Tchiroma Bakary da jami'an tsaro a ranar zaɓe da kuma ikirarin nasar da ɗan takarar na adawa ya yi.
Bidiyon da ke yawo a kafafen sada zumunta sun nuna yadda ɗaruruwan mutane ke tarwatsewa yayin da ‘yansanda ke watsa musu barkono mai sa hawaye domin tarwatsa masu gangamin.
Wasu rahotanni sun ce lamarin ya faru ne a biranen Younde da kuma Garoua.
Wani matashi da ke zaune a lardin Darka a arewacin Kamaru ya bayyana wa BBC cewa lamarin na da alaƙa da yanayin tashin hankali da ake fuskanta a wasu yankunan Kamaru.
“Tun kafin a fitar da sakamakon zaɓe ma, rikici ya fara ɓarkewa. Ana kona gidaje da motoci, kuma ana kawo ma’aikatan tsaro daga ƙasashen makwabta kamar Chadi domin taimakawa ƙasar samun ƙarin ƙarfin soji da na tsaro,” in ji shi.
"Hankalin talakawa da yawa ya juya a kan canji, gani suke yi kamar so ake yi a yi maguɗi," in ji shi.
Sai dai majalisar tattara sakamakon zaɓe ta ƙasar ta nanata cewa za ta gudanar da aikin cikin gaskiya da rikon amana, tana kuma kira ga dukkan ɓangarori da su guji tayar da hankali.
Amma wasu daga cikin magoya-bayan Tchiroma sun nuna rashin yarda da wannan magana, inda suka ce "duk sakamakon da ya fito, su dai Tchiroma ne shugabansu na gaskiya."
Yanzu haka, rahotanni sun nuna cewa jami’an tsaro sun ƙara tsaurara matakan tsaro a manyan birane, musamman a yankin arewa mai nisa, inda ake tsoron ɓarkewar rikice-rikice kafin ko bayan sanar da sakamakon zaɓen.