Kotu ta soke hukuncin da aka yanke wa tsohon shugaban Colombia
Asalin hoton, Getty Images
Wata babbar kotu a Bagota ta soke hukunce-hukunce biyu da aka yanke wa tsohon shugaban kasar Colombia Alvaro Uribe.
Tun da farko a wannan shekarar ne aka kama shi da laifin bai wa shaidu cin hanci da kuma yaudara, kuma aka yanke masa hukuncin daurin talala na tsawon shekara 12.
Wakiliyar BBC ta ce wannan ne karon farko da aka taba yankewa wani tsohon shugaban Colombia hukuncin aikata laifi a tarihi.
Dan siyasar mai tsattsauran ra'ayi wanda ya mulki kasar har zuwa shekarar 2010, ya yi fice wajen amfani da karfi kan yan tawayen FARC masu sassaucin ra'ayi.
Rikicin ƴandaba ya yi ajalin mutum a Afirka ta Kudu
Asalin hoton, South Africa Police Service
Ƴansanda a Afirka ta Kudu sun ce an kashe wasu matasa biyu, wasu mutum biyar kuma sun jikkata a yayin wani rikici da ake zargi na yan daba ne a Johannesburg.
wani mai magana da yawun ƴansanda ya ce rikici ne tsakanin kungiyoyi biyu, inda ƴan ƙungiya ɗaya suka yi wa dayan kwantar bauna a yankin Westbury.
Rahotanni sun bayyana cewa wadanda suka sami rauni na ciki mummunar yanayi.
Unguwar da lamarin ya faru ta sha fama da harbe-harben da ke da alaka da dabanci a tsawon shekaru.
An kama waɗanda ake zargi da aika ƙunshin bama-bamai Ukraine daga Romania
Asalin hoton, Getty Images
Masu shigar da kara a Romania sun ce sun kama mutum biyu da ake zargi da shirya aika kunshin sakonni masu dauke da abubuwan fashewa zuwa Ukraine.
Sun ce an aika kunshin sakonni masu dauke da abubuwan fashewa da kuma naurorin da ke tayar da su zuwa wani kamfanin sufuri na Ukraine da ke Bucharest, babban birnin Romania.
Mutanen biyu da aka kama, dukkaninsu ƴan asalin Ukraine ne.
Sun shiga Romania ne daga Poland, inda gwamnatin can ta sanar da kama mutum takwas da ta ke tuhuma da shirya ayyukan yi wa kasar zagon kasa.
Hukumomi a Romania sun ce har yanzu ba a tabbatar da ko an yi niyyar abubuwan su fashe a Bucharest ba ne, ko a kan hanya ko kuma idan sun isa Ukraine.
Yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza na nan daram - Mataimakin shugaban Amurka
Asalin hoton, Reuters
Mataimakin shugaban Amurka JD Vance ya ce ya yi ammana yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza na tafiya fiye da yadda aka yi tsammani, duk da mummunar tashin hankalin da aka samu a karshen makon jiya.
Mista Vance kenan da ya ke magana a Isra'ila, ya ce akwai wasu lokutan da abubuwa ba za su tafi yadda ake so ba, amma idan aka yi la'akari da yadda rikici ya ke ya kamata kowa ya yi alfahari da matakin da ake kai a yanzu.
Sojojin Isra'ila biyu da Falasdinawa fiye da arbain ne suka mutu a ranar Lahadi, bayan Isra'ila da Hamas sun zargi juna da karya yarjejeniyar.
Juyin mulki 8 da aka yi a Najeriya
Asalin hoton, AFP via Getty Images
Rahotannin da ke nuna cewa ana binciken wasu manyan sojoji su 16 dangane da zargin juyin mulki na ci gaba da jan hankalin ƴan Najeriya a soshiyal midiya.
Hedikwatar tsaro ta Najeriya dai tuni ta fitar da sanarwa inda ta musanta faruwar juyin mulki a Najeriyar.
Hedikwatar ta kuma faɗi cewa "binciken da ake yi da ya shafi manyan sojoji 16 wani abu ne da aka saba yi lokaci zuwa lokaci a cikin gida domin tabbatar da ɗa'a da ƙwarewar aiki a tsakanin sojojin."
Ƴanbiniga sun yi garkuwa da aƙalla mutum 73 a ƙauyuka biyu da ke ƙaramar hukumar Bukkuyum na jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriy.
Jaridar Premium Times mai zaman kanta ne ta ruwaito daga wani masanin harkokin tsaro a Najeriya, Zagazola Makama.
Jaridar ta ce ƴanbindigar sun kai farmakin ne a ƙauyukan Buzugu da Rayau, inda suka yi awon gaba da mutanen a tsakanin ƙauyukan biyu.
Jihar Zamfara na cikin jihohin da suka daɗe suna fama da matsalolin tsaro a arewacin Najeriya, musamman matsalar hare-haren ƴanbindiga.
Gwamnan Kano ya buƙaci NBC ta sa ido kan kafofin yaɗa labarai na intanet
Asalin hoton, FACEBOOK
Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya yi kira ga hukumar kula da kafafen yaɗa labarai a Najeriya NBC ta da fara kula da ayyukan kafofin rediyo da talabijin na intanet.
Gwamnan ya ce sanya ido kan abubuwan da kafofin suke yaɗawa a intanet zai taimaka wajen daƙile yaɗa labaran bogi da ma abubuwan da za su iya tayar da zaune tsaye.
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren watsa labaran gwamnan, Mustapha Muhammad ya fitar daga cikin tsakuren jawabin da gwamnan ya gabatar a taron ƙara wa juna sani da Hukumar NBC ta shirya a jihar Legas.
A jawabinsa, gwamnan wanda ya samu wakilcin darakta-janar harkokin watsa labarai da hulɗa da jama'a, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya nuna takaicinsa kan yadda ake abin da aka ga dama a amfani da intanet wajen yaɗa abubuwan da ba su dace, "wajen yaɗa abubuwan da suke jawo rarrabuwar kai musamman na addini da siyasa. Yanzu saboda rashin sa ido, intanet ya zama wajen baje-kolin labaran bogi da kalaman ɓatanci."
Ya ce lokaci ya yi da NBC za ta fara kula da ayyukan kafofin da suke yaɗa labarai ta intanet domin tsabtace abubuwan da suke yaɗawa.
Hazo ya lullube sararin samaniyar Delhi bayan bikin Diwali
Wani hazo mai guba ya lullube sararin samaniyar Delhi, babban birnin Indiya kwana guda bayan miliyoyin mabiya addinin Hindu sun gudanar da bikin Diwali, inda suka yi ta wasan tartsatin wuta wanda ya gurbata iska a wani mataki mai matukar hadari.
A farkon makon nan ne kotun Kolin Kasar ta sassauta haramcin yin amfani da tartsatsin wutar lokacin bikin, inda ta amince da yin amfani da wadanda ba su da illa sosai ga muhalli.
Matakin gurbacewar muhallin a yanzu a birnin ya ninka sau 16 kan yadda hukumar lafiya ta duniya ta amince ya kai a kullum.
A makwafciyar kasar Pakistan, hukumomi sun aiwatar da wani shiri na gaggawa na inganta yanayin iska a kasar, kuma sun daura alhakin ta'azzarar hazon kan Indiya.
Hare-haren Rasha sun raba dubban ƴan Ukraine da lantarki
Asalin hoton, Reuters
A Ukraine, dubban mazauna birnin Chernihiv da ke arewaci sun tsinci kansu cikin duhu da rashin ruwa bayan zafafan hare-hare ta sama da Rasha ta kai yankin cikin dare.
Rasha ta yi amfani da makamai masu linzami da jirage marasa matuka wajen kai hari kan cibiyoyin lantarkin da ke samar da lantarki a birnin da yankunan da ke kusa.
Hakazalika rashin wuta a wasu cibiyoyin samar da ruwa ya shafi ruwan da ake samarwa a birnin.
A yanzu haka inginiyoyi sun soma aiki domin gyara barnar da aka yi.
Rasha dai ta kwashe watanni ta na zafafa hare hare kan ababen more rayuwa na Ukraine.
Fashewar tankar man fetur ta yi ajalin gomman mutane a Neja
Asalin hoton, Getty Images
Rahotanni na cewa gomman mutane sun rasu, sannan wasu da dama suka jikkata bayan wata tankar man fetur ta fashe, sannan ta kama da wuta a ranar Talata a jihar Neja.
Haɗarin ya auku ne da misalin ƙarfe 11 na safiya a tsakanin garin Essan da Badeggi a kan titin Bida zuwa Agaie a ƙaramar hukumar Katcha da ke jihar.
Shugaban hukumar kiyaye haɗura ta Najeriya reshen jihar Neja, Hajiya Aishatu Sa'adu ta tabbatar da aukuwar haɗarin a zantawarta da jaridar Daily Trust mai zaman kanta, amma ta ce zuwa yanzu ba su iya tantance adadin waɗanda suka rasu ba.
Shaidun gani da ido sun masu rububin ɗibar fetur ne gobarar ta rutsa da su bayan tankar ta fashe, sannan sun ce wasu waɗanda suka rasu sun ƙone ƙurmus, sannan an kai wasu asibiti.
An kai hari a kusa da babban filin jirgin Khartoum sa’o’i kaɗan kafin buɗe shi
Asalin hoton, Anadolu via Getty Images
An kai hari da jiragen yaƙi marasa matuƙa a kusa da babban filin jirgin sama na birnin Khartoum a Sudan, 'yan sa’o’i kaɗan kafin a buɗe shi don dawo da zirga-zirgar kasuwanci na farko cikin watanni 30, tun bayan barkewar yaƙin 2023.
Shaidu sun bayyana cewa an ji jerin fashe-fashe kusa da filin jirgin a safiyar yau.
Hukumomin sufurin jiragen sama na Sudan sun sanar a jiya cewa filin jirgin zai buɗe a yau Talata domin cigaba da ayyukan zirga-zirgar cikin gida.
An sake gina filin jirgin saman ne bayan rundunar sojojin ƙasar ta ƙwace shi a watan Afrilu, bayan shekaru biyu a hannun dakarun RSF.
Ba a tabbatar ko filin jirgin zai bude ba kamar yadda aka tsara ba.
Harin ranar Talata shi ne na uku a babban birnin a cikin mako guda, bayan harin da aka kai wasu sansanonin soji guda biyu a arewa maso yammacin Khartoum a jere a ranakun makon da ya gabata.
Masu gangami kan sakamakon zaɓe sun yi arangama da ƴansanda a Kamaru
Asalin hoton, Getty Images
Masu gangani sun bazama a titunan biranen Garoua da Yaounde na ƙasar Kamaru, inda suke neman hukumar zaɓe ta fitar da sakamakon zaɓen shugaban ƙasar daidai da yadda suka kaɗa ƙuri'unsu.
A ranar 12 ga watan Oktoba ne al'ummar Kamaru suka je rumfunan zaɓe domin kaɗa ƙuri'a a zaɓen shugaban ƙasa, karo na farko da aka samu zazzafar adawa a tsawon shekaru.
Sai dai tun bayan zaɓen ake ci gaba da zaman ɗarɗar, bayan artabun da aka samu tsakanin magoya bayan ɗan takarar adawa Issa Tchiroma Bakary da jami'an tsaro a ranar zaɓe da kuma ikirarin nasar da ɗan takarar na adawa ya yi.
Bidiyon da ke yawo a kafafen sada zumunta sun nuna yadda ɗaruruwan mutane ke tarwatsewa yayin da ‘yansanda ke watsa musu barkono mai sa hawaye domin tarwatsa masu gangamin.
Asalin hoton, Getty Images
Wasu rahotanni sun ce lamarin ya faru ne a biranen Younde da kuma Garoua.
Wani matashi da ke zaune a lardin Darka a arewacin Kamaru ya bayyana wa BBC cewa lamarin na da alaƙa da yanayin tashin hankali da ake fuskanta a wasu yankunan Kamaru.
“Tun kafin a fitar da sakamakon zaɓe ma, rikici ya fara ɓarkewa. Ana kona gidaje da motoci, kuma ana kawo ma’aikatan tsaro daga ƙasashen makwabta kamar Chadi domin taimakawa ƙasar samun ƙarin ƙarfin soji da na tsaro,” in ji shi.
"Hankalin talakawa da yawa ya juya a kan canji, gani suke yi kamar so ake yi a yi maguɗi," in ji shi.
Sai dai majalisar tattara sakamakon zaɓe ta ƙasar ta nanata cewa za ta gudanar da aikin cikin gaskiya da rikon amana, tana kuma kira ga dukkan ɓangarori da su guji tayar da hankali.
Amma wasu daga cikin magoya-bayan Tchiroma sun nuna rashin yarda da wannan magana, inda suka ce "duk sakamakon da ya fito, su dai Tchiroma ne shugabansu na gaskiya."
Yanzu haka, rahotanni sun nuna cewa jami’an tsaro sun ƙara tsaurara matakan tsaro a manyan birane, musamman a yankin arewa mai nisa, inda ake tsoron ɓarkewar rikice-rikice kafin ko bayan sanar da sakamakon zaɓen.
ADC ta gargaɗi gwamnati kan amfani da zargin juyin mulki don murƙushe ƴan Adawa
Asalin hoton, x/ADC
Jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ta gargaɗi gwamnatin Najeriya da kada ta yi amfani da zargin yunkurin juyin mulkin da ya shafi wasu sojoji da aka kama a matsayin hujja don murkushe ‘yan adawa ko masu sukar gwamnati.
Jam'iyyar dai ta nemi gwamnati ta fito fili ta bayyana gaskiyar labarin da ake yadawa game da zargin yunkurin juyin mulkin .
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun jam’iyyar na ƙasa, Bolaji Abdullahi, ya fitar, ADC ta ce tana ɗaukar duk wani barazana ga tsarin dimokuradiyyar ƙasar da muhimmanci sosai, amma ta nuna damuwa kan yadda ake amfani da irin waɗannan zarge-zarge wajen cimma manufofin siyasa.
Jam’iyyar ta bayyana cewa tana bibiyar rahotannin da ke alaƙanta wasu sojoji da aka kama da zargin yunkurin juyin mulki, da kuma jita-jitar cewa wani tsohon gwamna daga kudancin ƙasar yana fuskantar bincike bisa zargin tallafa wa waɗanda ake zargi.
“Ko da yake muna adawa da duk wani yunƙuri da zai rushe tsarin mulki, abin damuwa shi ne yadda ake iya amfani da irin wannan labari wajen farautar ‘yan adawa da masu sukar gwamnati,” in ji sanarwar.
ADC ta kuma soki gwamnatin bisa yin shiru kan batun, tana mai cewa "hakan na iya zama wata dabara ta barin labarin ya ci gaba da yaɗuwa domin karkatar da hankalin jama’a daga matsalolin da ake fuskanta a fannin mulki da tattalin arziki.
Ana fargabar rikici a Kamaru yayin da ake shirin sanar da sakamakon zaɓe
Asalin hoton, Getty Images
Ana zaman ɗarɗar a Kamaru yayin da kwamitin tsarin mulkin ƙasar ke shirin sanar da sakamakon ƙarshe na zaben shugaban ƙasa a ƙarshen wannan mako.
Shugabannin cocin Katolika sun yi kira ga yanayi na lumana saboda tsoron ɓarkewar rikici sakamakon saɓani kan sakamakon.
Ana sa ran kwamitin tsarin mulkin ƙasar zai saurari hujjoji a ƙarshen wannan mako kan jerin ƙorafe-ƙorafe da ake yi na soke zaɓen saboda zargin rashin gaskiya.
Kashim Shettima ya bai wa matashiya aron kujerarsa na kwana ɗaya
Asalin hoton, Kashim Shettima
Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ya bai wa wata matashiyam mai suna Joy Ogah aron kujerarsa na kwana ɗaya.
Wannan lamari ya faru ne a fadar shugaban ƙasa, yayin da Shettima ya karɓi bakuncin wani tawagar PLAN International karkashin jagorancin shugabar tawagar, Helen Mfonobong Idiong.
A cikin jawabin sa, Shettima ya jaddada ƙudirin gwamnatin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu na inganta karatun yara mata a fadin Najeriya.
Ya bayyana cewa gwamnati za ta ci gaba da haɗin gwiwa da PLAN International domin ganin shawarwarin da suka bayar kan ilimin yara mata sun samu karɓuwa da aiwatarwa.
Ya bayyana cewa ci gaban yara mata babban ginshiƙi ne na cigaban ƙasa baki ɗaya.
A ɓangarenta, matashiyar Joy Ogah ta yi godiya da wannan damar, inda ta ce mata na iya zama shugabanni idan hukumomi da masu ruwa da tsaki suka aiwatar da matakan da suka dace.
Asalin hoton, Kashim Shettima
'Ana ci gaba da garkuwa da mutane duk da sakin wasu da ake yi ta hanyar sulhu'
Asalin hoton, Getty Images
Ana ci gaba da garkuwa da mutane duk da sakin wasu da ake yi ta hanyar sulhu a Arewacin Yammacin Najeriya, inda ƴan bindiga suka saki mutum fiye da 120 a jihohin Zamfara da Katsina, yayin da kuma aka sace sabbin mutane a wasu kauyuka na Zamfara.
Rahotannin PRNigeria sun nuna cewa shahararren shugaban ƴan bindiga, Bello Turji ya saki fiye da mutane 100 a Zamfara, yayin da wani shugaban ‘yan bindiga da ba a sani ba ya saki sama da mutum 20 da aka sace a Katsina.
Wannan sakin ya biyo bayan tattaunawar sulhi da aka gudanar ta hanyar tsarin sulhu na “North West Operation Safe Corridor.”
Duk da haka, wannan cigaba ya samu tangarda nan take sakamakon sabon harin ‘yan bindiga a garuruwan Buzugu da Rayau na karamar hukumar Bukkuyum a jihar Zamfara, inda rahotanni suka nuna cewa an sace fiye da mutum 70.
An kai waɗanda aka saki a Zamfara da Katsina asibitoci don kula da lafiyarsu kafin a mayar da su ga iyalansu.
Hukumomi sun tabbatar da cewa ana ci gaba da sa ido sosai kan tsarin sulhun don tabbatar da ingancinsa da hana kowanne rukuni amfani da tattaunawar wajen sake tattarawa ko sake daukar makamai.
Hisba ta ce ta fara shirye-shiryen auren Maiwushirya da Ƴarguda
Asalin hoton, FB/Maiwushirya
Hukumar Hisba a jihar Kano da ke Najeriya ta ce ta fara shirye-shiryen auren sanannun ƴan tiktok da ke jihar, Ashiru Idris wanda aka fi sani da Maiwushirya da Basira wadda ake yi wa laƙabi da Ƴarguda, bayan umarnin da kotu ta bayar na yin hakan.
A ranar Litinin ne wata kotun majistare a Kano ta bai wa Hisbah umarnin ɗaura aure tsakanin matasan biyu, bayan wasu bidiyoyi da suka riƙa wallafawa a shafukan sada zumunta da ke nuna kusanci a tsakaninsu.
Kotun ta yanke hukuncin ne bayan an gurfanar da matasan biyu a gabanta, bisa zargin su da yaɗa bidiyoyi na 'rashin ɗa'a' a shafin sada zumunta.
Kotun ƙarƙashin jagorancin mai shari'a Halima Wali ta ce rashin gudanar da auren a cikin lokacin da ta ayyana zai zama "saɓa umarnin da ta bayar".
Amazon ya magance babbar matsalar da ta janyo cikas ga shafukan intanet
Asalin hoton, Getty Images
Kamfanin Amazon ya ce an shawo kan babbar matsalar da aka samu da ta shafi naurorinsa, abun da ya haifar da gagarumin cikas a jiya Litinin.
Ɗaruruwan manyan shafukan Internet da wasu manhajoji kamar Snapchat, da Lyft, da Reddit ne matsalar ta shafa.
Ƙoƙarin da aka yi na farko na shawo kan matsalar ya sa an sake jangwalo wata sabuwar matsalar, abun da ya sake dagula komai.
FRSC za ta fara bayar da lasisin tuƙi nan take
Asalin hoton, @FRSCNigeria
Hukumar Kula da Hanyoyi ta Najeriya FRSC ta sanar cewa ta inganta cibiyar buga takardunta don samar da matsakaicin lasisin tuƙi guda 15,000 a kowace rana wanda hakan zai bayar da damar karɓar lasisin tuƙi nan take.
Wannan mataki na da nufin kawar da dukkan jinkirin da ake samu wajen karɓar lasisin tuƙin wajen ƙoƙarin ganin sun sallami duk masu neman ayi musu lasisin tuƙi kafin nan da tsakiyar watan Nuwamba
Kwamandan FRSC, Shehu Mohammed ne ya bayyana haka a Abuja bayan ziyartar cibiyar buga takardun, inda ya ce sabon tsarin zai magance matsalolin jinkirin da ake samu wajen sarrafa lasisin direba da lambobin motoci, kamar yadda jaridar Gaurdian ta ruwaito.
Mohammed ya ce FRSC zai fara amfani da tsarin ɗaukar bayanan yatsu hannun mutum daga nesa tare da buga lasisin nan take wanda zai kawar da lasisin wucin gadi.
Ya kara da cewa wannan ci gaba zai sa jinkiri da sauran matsalolin da suka shafi lasisin tuƙi na ƙasa su zama tarihi.
Mataimakin Shugaban Amurka zai ziyarci Isra’ila don inganta tsagaita wuta a Gaza
Asalin hoton, Getty Images
Nan gaba kadan a yau ake sa ran mataimakin shugaban Amurka JD Vance zai isa Isra'ila a wani ɓangare na ƙoƙarin ƙarfafa yarjejeniyar tsagaita buɗe wuta a Gaza.
Ana sa ran zuwansa zai sa firaministan Isra'ila Benyamin Natanyahu ya ba da himma ga tattaunawa kan sauran ɓangarorin yarjejenyar zaman lafiyar da aka cimma don kawo ƙarshen yaƙin na dindindin.
Abubuwan da za a tattauna sun hada da shirin tura dakarun ƙasa da ƙasa zuwa Gaza, da kuma kwance ɗamarar Hamas.
A baya dai Isra'ila ta ce ba za ta shiga irin wannan tattaunawar ba har sai Hamas ta mayar da dukkan gawarwakin mutanenta da suka mutu a hannun Hamas.
An sake mayar da gawa guda cikin dare, don haka har yanzu ba a gano gawarwakin mutane goma sha biyar ba.
Tuni wakilan Amurka na musamman guda biyu, Steve Witkoff da Jared Kushner, wadanda suka taimaka wajen tattaunawa da Hamas suka isa Isra'ila a jiya Litinin.