Labarin wasanni daga 27 ga Satumba zuwa 3 ga watan Oktoban 2025

Wannan shafi ne da ke kawo muku muhimman abubuwan da ke faruwa a duniyar wasanni daga Asabar 27 ga Satumba zuwa 3 ga watan Oktoban 2025

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu

  1. Osimhen ya tara wa Liverpool gajiya a Champions League

    Victor Osimhen

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, Victor Osimhen

    Liverpool ta sha kashi sau biyu a jere bayan da Galatasary ta yi mata kancal a karawa ta biyu a gasar zakarun Turai da aka yi a Istanbul.

    Dan wasan Galatasary Victor Osimhen ne ya zura kwallo a ragar Liverpool bayan minti 16 da fara wasa

    Bayan komawa daga hutun rabin lokaci mai horas da Liverpool Arne Slot ya sako ‘yan wasansa da yake ji da su Mohammed Sallah da kuma Alexander Isak domin ganin ko zai ceto kungiyar tasa daga nutsewa to amma bakin alkalami ya riga ya bushe.

    A can cikin wasa har Liverpool ta sa ran farkewa a lokacin da lafari ya hura fanareti lokacin da Ibrahima Konate ya fadi a gaban raga, sai dai bayan dubawa da kyau a VAR, lafari ya sauya matsayarsa ya ce babu fawul.

    Osimhen ne aka ba dan wasa mafi hazaka a karshen wasan.

    Real Madrid ta sauke fushinta kan Almaty

    Bayan kwasan kashinta a hannu cikin karshen mako, Real Madrid ta bi kungiyar Almaty ta kasar Kazakhstan har gida ta huce haushi a kanta da ci 5 da babu.

    Dan wasa Kylian Mbape ne ya barje guminsa a wasan inda ya zura kwallo daidai har uku.

    Mbape ya zura ta farko a minti na 25 ta hanyar bugun fanareti, sannan ya kara zura wata a minti na 52 kafin ya ci ta karshe a minti na 73.

    Camavinga ya zura tasa kwallon a minti na 83 yayin da Brahim Diaz ya cike ta biyar a minti ma 93, dab da hura tashi.

    Mourinho bai sha da dadi ba a Stamford Bridge

    Chelsea ba su yi wa Mourinho kara ba a wannan karo inda suka yi nasara kan Benfica, kungiyar da Mourinho ya fara horaswa a kwanan nan bayan ya baro Turkiyya.

    Ita ma Chelsea din ta sha ne da kyar bayan da dan wasan Benfica Richard Rios ya zura kwallo a ragar kungiyarsa

    A sauran wasannin:

    Pafos 1-5 Bayern Munich

    Bodo/Glimt 2-2 Tottenham

    Atalanta 2-1 Club Brugge

    Atletico Madrid 5-1 Eintracht Frankfurt

    Inter 3-0 Slavia Prague

    Marseille 4-0 Ajax

  2. Ni da Chelsea mun zama hanta da jini - Mourinho

    Jose

    Asalin hoton, Getty Images

    Tsohon kocin ƙungiyar Chelsea ta Ingila, Jose Mourinho wanda yanzu yake horar da ƙungiyar Benfica ya ce shi da ƙungiyar ta Stanford Bridge sun zama hanta da jini.

    Mourinho ya bayyana haka ne a ganawarsa da manema labarai kan shirye-shiryen da yake yi na jagorantar ƙungiyar Benfica ta ƙasar Portugal a wasan da za ta fafata da Chelsea na gasar zakarun turai a Ingila a yau Talata.

    Sai dai ya ce a lokacin da ake tsaka da wasan, "zan jingine ƙaunar da yake yi wa Chelsea na minti 90 domin in fuskanci aikin da nake yi wa ƙungiyar Benfica."

    Ya ce, "a ƙungiyar Chelsea na zama abin da na zama, har ake magana, sannan ni ne na ɗaga darajar Chelsea ta zama babbar ƙungiyar da a yanzu ake ji da ita. Tarihina ba zai taɓa cika ba ba tare da ambaton Chelsea ba, haka kuma ba a taɓa raba tarihin ƙungiyar da ni ba."

    Jose ya ƙara da cewa yana matuƙar ƙaunar ƙungiyar, amma "a yau aikina shi ne jagorantar Benfica ta samu nasara."

  3. Arsenal ta ci gaba da zama ta biyu a Premier League

    Premier League

    Asalin hoton, Getty Images

    Arsenal ta je ta doke Newcastle United 2-1 a wasan mako na shida a Premier League ranar Lahadi.

    Newcastle ce ta fara cin ƙwallo ta hannun Nick Woltemade tun kan hutu a karawar da suka yi a St James Park.

    Bayan da suka sha ruwa suka koma zagaye na biyu ne Gunners ta farke ta hannun Mikel Merino daga baya Gabriel Magalhães ya ci na biyu daf a tashi.

    Da wannan sakamakon Arsenal tana mataki na biyu a teburin Premier League da tazarar maki biyu tsakani da Liverpool mai jan ragama.

    Ranar Asabar Liverpool ta i rashin nasara 2-1 a gidan Crystal Palace.

    A makon da za mu shiga Arsenal za ta fafata da Olympiacos a Champions League a Emirates, sannan ta karɓi bakuncin West Ham a Premier League.

  4. Barau FC ta ci wasa a karon farko a Premier ta Najeriya

    bARAU

    Asalin hoton, Barau FC

    A karon farko ƙungiyar Barau FC ta ci wasa a Premier League ta Najeriya a bana, bayan da ta je ta ci Kun Khalifa 3-1 a wasan mako na shida.

    Da wannan sakamakon Barau FC ta bar gurbin karshe a teburi ta koma ta 18 da maki biyar da ƙwantan wasa.

    Wasu sakamakon wasannin da aka buga a jiyan:

    • Kun Khalifat 1-3 Barau FC
    • Nasarawa United United 2-0 Katsina United
    • Warri Wolves 1-2 Shooting Stars
    • Wikki Tourists 2-2 Enugu Rangers International

    Wasannin da suka zama ƙwantai

    • Rivers United da Niger Tornadoes
    • Abia Warriors da Remo Stars
    • Kano Pillars da Kwara United
  5. Ƙyaftin din Real Madrid, Carvajal zai yi jinyar mako huɗu

    Carbajal

    Asalin hoton, Getty Images

    Ƙyaftin ɗin Real Madrid, Dani Carvajal ya ji rauni ranar Asabar kamar yadda ƙungiyar ta sanar ranar Lahadi, wasu rahotanni daga Sifaniya na cewa zai yi jinyar mako huɗu.

    Ya buga wa Real Madrid wasa bakwai daga takwas da ta yi a dukkan karawa a bana, ya ji rauni ne a gasar La Liga da Atletico Madrid ta caskara Real 5-2.

    A watan Yuli mai shekara 33 ya koma taka leda lokacin da Real Madrid ke buga Club World Cup a Amurka, bayan jinyar wata tara da ya yi.

    Real Madrid ba ta fayyace ranar da zai kammala buga tamaula ba, sai dai wasu jaridun Sifaniya na cewa zai yi mako huɗu kafin ya koma taka leda, kenan da kyar idan zai buga El Clasico da Barcelona ranar 26 ga watan Oktoba.

    Haka shima Trent Alexander-Arnold da Antonio Ruediger na jinya, kenan mai horar wa Xabi Alonso na karancin gurbin masu tsaron baya.

    Ranar Talata Real Madrid za ta je Kazakhstan domin fuskantar Kairat Almaty a wasa na biyu a cikin rukuni a Champions League.

  6. An yaga ɓaraka a Chelsea

    Maresca

    Asalin hoton, Getty Images

    Tun bayan da Chelsea ta lashe Fifa Club World Cup a Amurka kan fara kakar bana, Enzo Maresca ya fara cin karo da koma baya a fannin tamaula.

    Magoya baya sun yi masa kuwwa ranar Asabar, bayan tashi wasan da Brighton ta je har Stamford Bridge ta dura 3-1 a wasan mako na shida a Premier League.

    Tun kafin karawar ta ranar Asabar, wasa biyu Chelsea ta ci a Premier League da canjaras biyu aka doke ta karawa ta yanzu yanzu haka.

    An kuma ci Chelsea a karon farko a gida, bayan wasa 12 a jere ba tare da rashin nasara ba, bayan canjaras uku da cin fafatawa tara.

    Tun kafin nan Chelsea ta yi rashin nasara 3-1 a wasan farko a Champions League da Bayern Munich da kuma wanda ta yi rashin nasara a gidan Manchester United 2-1 a Premier League.

    Koda yake Chelsea ta kai zagayen ƴan 16 a Carabao Cup, sakamakon yin waje da Lincoln da yin nasara 2-1.

    A makon gobe Chelsea za ta kara da Benfica, wadda Jose Mourinho ke jan ragama a Champions League a Stamford Bridge.

    Daga nan Chelsea za ta karɓi bakuncin Liverpool a wasan mako na bakwai a Premier League..

  7. Astron Villa ta ci wasa a karon farko a Premier League a bana

    Premier

    Asalin hoton, Getty Images

    A karon farko Aston Villa ta ci wasa a Premier League a bana, bayan doke Fulham 3-1 a wasan mako na shida ranar Lahadi.

    Fulham ce ta fara cin ƙwallo ta hannun Jimenez a minti na uku da take leda daga baya Watkins ya farke, kuma karon farko da ya ci ƙwallo a wasa na takwas, bayan ƙanfar zura ƙwallo a raga a lik a wasa bakwai a jere.

    Bayan da aka koma zagaye na biyu ne Villa ta karasa cin ƙwallo biyu ta hannun McGinn da kuma Buendia, hakan ya sa ta samu maki ukun da take bukata.

    Kenan Fulham ta yi nasara ɗaya daga wasa 22 da ta kai ziyara Villa Park da canjaras bakwai an doke ta karo na 14, tun bayan 2-1 da ta yi nasara a watan Afirilun 2014.

    Marco Silva ya yi rashin nasara bakwai daga wasa takwas a Premier League da ya fuskanci Villa, inda ya sha kashi a lokacin da yake Everton da rashin nasara shida a Fulham.

  8. Espirito Santos ya kwan da sanin ƙalubalen da ke gaban West Ham

    Nuno

    Asalin hoton, Getty Images

    Nuno Espirito Santo zai fara jan ragamar West Ham ranar Litinin a wasan Premier League mako na shida da Everton.

    An naɗa Santo mai shekara 51 kociyan West Ham ranar Asabar, sa'a huɗu tsakani da aka sallami Graham Potter, daga nan ya ja ragamar atisayen yammcin ranar.

    Nuno, wanda Nottingham Forest ta kora kasa da mako uku, ya gaji ƙungiyar da take mataki na 19 a kasan teburi da rashin nasara huɗu daga wasa biyar a lik, an kuma yi waje da ita a Carabao Cup a hannun Wolverhampton.

  9. Atletico ta ɗura wa Real Madrid ƙwallo biyar karon farko a shekara 75, Atletico Madrid 5-2 Real Madrid

    La Liga

    Asalin hoton, Getty Images

    Kociyan Real Madrid, Xabi Alonso ya ce ya kamata su ɗauki darasi, bayan da Atletico Madrid ta doke su 5-2 ranar Asabar a gasar La Liga, sakamakon da ya ƙwatanta mai raɗaɗi da takaici.

    Wannan shi ne karon farko da Real Madrid ta yi rashin nasara da fara kakar bana, kuma na farko da Atletico ta zura ƙwallo biyar a ragar Real a shekara 75.

    Alonso, wanda ya maye gurbin Carlo Ancelotti, wanda ya koma horar da tawagar Brazil, ya bukaci magoya baya suyi hakuri da sakamakon wasa da sa juriya.

    Da wannan sakamakon Real Madrid ta ci gaba da zama ta ɗaya a kan teburin La Liga da maki 18, yayin da Barcelona ta biyu za ta buga wasanta da Sociedad ranar Lahadi.

    Ita kuwa Atletico ta koma ta huɗun teburi da maki 12.

    Wasannin da aka ci ƙwallaye da yawa tsakanin Atletico da Real Madrid:

    Copa del Rey Alhamis 18 ga watan Janairun 2024

    • Atl Madrid 4 - 2 Real Madrid

    Spanish Super Cup Laraba 10 ga watan Janairun 2024

    • Real Madrid 5 - 3 Atl Madrid

    Spanish La Liga Asabar 7 ga watan Fabrairun 2015

    • Atl Madrid 4 - 0 Real Madrid

    Champions League Asabar 24 ga watan Mayun 2014

    • Real Madrid 4 - 1 Atl Madrid

    Spanish La Liga Lahadi 17 ga watan Janairun 1999

    • Real Madrid 4 - 2 Atl Madrid

    Spanish La Liga Asabar 18 ga watan Janairun 1997

    • Atl Madrid 1 - 4 Real Madrid

    Spanish La Liga Asabar 5 ga watan Nuwamba 1994

    • Real Madrid 4 - 2 Atl Madrid
  10. Amorim bai damu da tantance makomarsa ba a Manchester United, Brentford 3-1 Manchester United

    aMORIM

    Asalin hoton, Getty Images

    Kociyan Manchester United Ruben Amorim ya ce bai damu da tantance makomarsa a ƙungiyar Old Trafford ba, bayan da ya kara cin karo da koma baya ranar Asabar.

    United, wadda ta doke Chelsea a Premier League kwana bakwai da ya wuce, sai gashi ta yi rashin nasara 3-1 a gidan Brentford a wasan mako na shida a babbar gasar tamaula ta Ingila ranar Asabar.

    United ta samu maki 34 a wasa 33 a lik karkashin Amorim, kuma har yanzu ba ta ci karawa biyu ba a jere a gasar.

    A kakar da ta wuce United ta kare a mataki na 15 a kasan teburi ba tare da lashe kofi ba koda na shayi ne, kuma ba ta buga gasar zakarun Turai.

    The promised improvement after last season's woeful 15th-place finish is yet to materialise, and afterwards Amorim was forced to answer more questions about his future.

  11. Liverpool ta yi rashin nasara a karon farko a bana, Crystal Palace 2-1 Liverpool

    Liverpool

    Asalin hoton, Getty Images

    Crystal Palace ta doke Liverpool 2-1 a wasan mako na shida a Premier League da suka kara a Anfield ranar Asabar.

    Karon farko da ƙungiyar Anfield ta yi rashin nasara a Premier League, bayan da ta lashe dukkan karawa biyar da fara kakar nan.

    Tun farko Liverpool ta sa ran cin wasa na shida a jere da fara Premier League, kuma da ya zama karo na biyar tana wannan bajintar bayan 1978/79 da 1990/91 da 2018/19 da kuma 2019/20.

    Sai dai har yanzu Liverpool ce ta farko a teburin Premier League da maki 18.

    A makon da za mu shiga ƙungiyar da Arne Slot ke jan ragama za ta buga Champions League a gidan Galatasaray, daga nan ta je Stamford Bridge don fuskantar Chelsea da kuma Manchester United da za su yi tata ɓurza a Anfield duk a Premier League.

  12. Barkanmu da shiga sharhi da bayanan wasanni

    Jama'a barkanmu da shiga shirin sharhi da bayanan wasanni kai tsaye tare da ni Mohammed Abdu Mamman Skipper Tw.

    Za ku iya tafka muhawara a shirin ko bayar da gudunmuwa a BBCHausa Facebook.