Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Labarin wasanni daga 27 ga Satumba zuwa 3 ga watan Oktoban 2025

Wannan shafi ne da ke kawo muku muhimman abubuwan da ke faruwa a duniyar wasanni daga Asabar 27 ga Satumba zuwa 3 ga watan Oktoban 2025

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu

  1. Lamine Yamal zai sake yin jinyar mako uku

    Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Barcelona ta ce ɗanwasan gabanta Lamine Yamal zai yi jinyar mako uku sakamakon raunin da ya ji a mararsa.

    Wata sanarwa da ƙungiyar ta wallafa a shafukanta na sada zumunta ta ce matashin ɗanwasan mai shekara 18 ya ji raunin ne yayin wasansu da PSG a gasar zakarun Turai ta Champions League.

    "Rashin jin daɗin da Lamin e Yamal ya ce yana fuskanta ya sake dawowa bayan wasa da PSG," in ji sanarwar.

    "Ba zai buga wasa da Sevilla ba, kuma ana sa ran zai yi jinyar mako biyu zuwa uku."

    Kazalika, akwai fargabar ko Yamal zai yi murmurewar da za ta ba shi damar buga wasan hamayya na El Clasico ranar 26 ga watan Oktoba, wanda Real Madrid za ta yi wa Barca masauki a filin wasa na Santiago Bernebeu.

    A ranar 28 ga watan Satumba ne Yamal ya koma taka wa Barca leda bayan jinyar da ya yi.

  2. Tuchel ya bayyana dalilin rashin gayyatar Bellingham da Foden da Grealish wasannin Ingila

    Kocin Ingila Thomas Tuchel ya ce babu wata matsala a tsakaninsa da ƴanwasan tawagar ƙasar Ingila Jude Bellingham da Phil Foden ko Jack Grealish baya an fara tofa albarkacin baki kan rashin ganin su a cikin ƴanwasan da za su fafata a wasannin da Ingila za ta buga da ƙasashen Wales da Latvia.

    Bellingham bai samu shiga cikin ƴanwasan ba, duk da cewa ya warware daga jinyar da ya yi, shi kuma Foden da Grealish suna ci gaba a buga wasani a ƙungiyoyinsu waso Manchester City da Everton.

    Kocin ya ce ya yi magana da Bellingham, inda ya buƙaci a saka shi a cikin jerin ƴanwasan. "Babu wata matsala a tsakaninmu. Mu yi magan da shi ta waya, duk da cewa a farkon wannan shekarar ya ƙalubalanci ɗanwasan da ya ƙara ƙaimi.

    Kocin ya ƙara da cewa ba ma Bellingham ba kaɗai, "har da Phil Foden da Jack Grealish duk babu wata a tsakaninmu," in ji Tuchel.

    "Na yanke hukunci ne a kan ƴanwasan da zan gayyata, ko da ya musu daɗi, ko bai musu daɗi ba. Amma sun san ina girmama ƙoƙarinsu, kuma na san irin rawar da suke takawa a ƙungiyoyin da suke wakilta a yanzu."

  3. Jamus na fatan lashe wasa biyu don zuwa gasar kofin duniya

    Tawagar Jamus na sa ran lashe wasa biyu a karawar neman shiga gasar cin kofin duniya da za ta yi da Luxembourg da Ireland ta Arewa, domin ta koma kan turbar hangen zuwa Amurka da Canada da Mexico a baɗi in ji kociya Julian Nagelsmann.

    Jamus za ta karɓi bakuncin Luxembourg ranar 10 ga watan Oktoba daga nan ta ziyarci Ireland ta Arewa kwana uku tsakani.

    Tawagar da Nagelsman ke jan ragama ta ci wasa ɗaya da rashin nasara ɗaya a rukunin farko.

    Kenan tana ta uku a kan teburi da maki uku biye da Ireland ta Arewa da tazarar rarar ƙwallaye, yayin da Luxembourg ce ke jan ragama.

    Wadda ta ja ragama ce za ta je gasar kofin duniya kai tsaye a 2026, ta biyu ta je buga wasannin cike gurbi.

  4. Ana kokarin soke dokar kashe kudi daidai samu ta Premier League

    Za a yanke shawara kan ko za a soke dokar nan da ake takaddama ta cin ribar ungiya da dorewarta ta gasar Premier (PSR) da kuma yin amfani da wani tsarin madadinsa, in ji shugaban zartarwa, Richard Masters.

    An fara gabatar da dokar a cikin kakar 2015-2016 don hana ƙungiya kashe ƙudi fiye da kima, ba a yadda ƙungiya ta yi hasarar kasuwacin fam miliyan 105 ba a cikin shekara uku.

    Duk da haka, an soki mahukunta da cewar hakan yakan takaice fafutuka da yawa sannan yana takaita ikonsu na saka hannun jari.

    An shaida wa BBC za a yanke shawara kan duk wani sauye-sauye da za a yi a wani taro a watan Nuwamba.

    A cikin Fabrairu ƙungiyoyin suka zaɓi ci gaba da PSR don ci gaba da amfani da dokar a kakar nan.

  5. Bayern Munich na da niyyar mayar da zaman aro na ɗan wasan Chelsea da Senegal Nicolas Jackson mai shekara 24 zuwa na dindindin. (TBR Football)

    Arsenal na shirin biyan ɗan wasan ƙasar Ingila Bukayo Saka mai shekara 24, wanda kwantiraginsa zai ƙare a bazarar 2027, albashin sama da fam 250,000 a duk mako. (Talksport)

    Tottenham na shirin ƙulla sabuwar yarjejeniya da ɗan wasan tsakiya na Uruguay, Rodrigo Bentancur, mai shekara 28, wanda kwantiraginsa zai ƙare a bazarar 2026. (Athletic)

    Manchester City da Real Madrid suna sa ido kan ɗan wasan Faransa Michael Olise a yayin da Bayern Munich ke tunanin inganta kwantiragin ɗan wasan mai shekara 23. (Teamtalk)

  6. Birnin Landan zai karɓi bakuncin gasar ƙwallon mata ta Champions Cup da aka kirkira

    Birnin Landan zai karɓi bakuncin gasar ƙwallon kafar mata ta Champions Cup da aka kirkira da za a fara daga baɗi.

    Za a fafata ne tsakanin zakarun nahiyoyi, kamar yadda ake yi a Fifa Club World Cup na maza, amma ƙungiya huɗu za a fara da su.

    Kenan za a buga daf da karshe biyu da neman mataki na uku da wasan karshe da za a yi a Landan tsakanin 28 ga watan Janairu zuwa 1 ga watan Fabrairun 2026.

    Amma har yanzu ba a fayyace filin da za a buga wasannin ba.

    Ƙungiyar ƙwallon kafa ta mata ta Arsenal ce za ta wakilci Turai.

    Sai wasan cike gurbi daga Asia da Afirka da kuma Oceania.

  7. Watakila a kara yawan tawagogi a kofin duniya a 2030 zuwa 64

    Hukumar ƙwallon kafa ta duniya, Fifa ta gudanar da taro ranar Alhamis a birnin Zurich a Switzerland.

    Daga cikin batutuwan da aka tattauna har da shawara da hukumar ƙwallon kafar Kudancin Amurka ta bayar da a kara tawagar da za ta halarci gasar kofin duniya a 2030 da su koma 64.

    Argentina da Paraguay da Uruguay ne za su yi haɗakar karɓar baƙuncin wasannin tare da Sifaniya da Portugal da kuma Morocco a bikin cika shekara 100 da Fifa za ta gudanar da gasar.

    A baɗi ne za a buga gasar cin kofin dunuya a Amurka da Canada da kuma Mexico da tawaga 48 a karon farko a tarihi.

    To sai dai ana fargabar cewar idan aka kara tawagar ta koma 64, ingancin gasar zai samu tawaya.

  8. Chelsea na da ƙwarin gwiwa cewa za ta iya ɗaukar golan AC Milan da Faransa Mike Maignan mai shekara 30. (ASRomalive)

    Tottenham da West Ham da Nottingham Forest suna zawarcin ɗan wasan Parma ɗan ƙasar Argentina Mateo Pellegrino, mai shekara 23, amma kulob din na Italiya ba ya son sayar da shi kafin bazara mai zuwa. (TuttoSport)

    Liverpool za ta iya amincewa ta bar ɗan wasan bayan Ingila Joe Gomez ya tafi a watan Janairu - muddin za ta iya samun wanda zai maye gurbinsa - yayinda da AC Milan ke nuna sha'awa kan ɗan wasan mai shekara 28. (Caughtoffside)

    Porto ta na sa ido kan ɗan wasan Brighton da Ingila na ƴan ƙasa da shekara 21 Tommy Watson mai shekara 19. (Football Insider)

    AC Milan na zawarcin ɗan wasan gaban Barcelona da Poland Robert Lewandowski, mai shekara 37. (Sport)

    Ɗan wasan gaban Argentina Julian Alvarez, mai shekara 25, ya ce baya barin rade-radin da ake yi kan zawarcin da Barcelona ke yi masa ya shafe shi, kuma ya mai da hankali kan samun nasara a Atletico Madrid. (ESPN)

  9. Gyokeres ya yi wasa biyar bai ci wa Arsenal ƙwallo ba

    Kociyan Arsenal, Mikel Arteta ya ce yana da tabbacin cewar Viktor Gyokeres zai koma cin ƙwallaye, bayan wasa biyar ba tare da ya zira ƙwallo ba a raga.

    Rabon da ya ci ƙwallo tun 13 ga watan Satumba da Arsenal ta doke Nottingham Forest 3-0 a Premier League, wanda ya ci ɗaya daga ciki.

    Kuma kawo yanzu tun bayan da Gunners ta sayo ɗan wasan kan fara kakar bana, guda uku ya zura a raga har da biyun da ya ci Leeds United a Premier League da Arsenal ta sahara 5-0 ranar 23 ga watan Agusta.

    Jimilla wasa tara daga 11 da Gunners ta yi a dukkan kakar nan Gyokeres bai ci wa Arsenal ƙwallo ba.

    Sai dai kuma ranar Asabar 4 ga watan Oktoba, Arsenal za ta karɓi bakuncin West Ham a gasar Premier League, watakila ya zura ƙwallo a raga.

  10. PSG na fatan lashe dukkan kofuna a kakar bana

    Bayan da Paris St Germain ta je ta doke Barcelona 2-1 ranar Laraba a Champions League wasa na biyu a cikin rukuni.

    PSG, mai rike da kofin zakarun Turai na bara na fatan kara yin abin kirki a bana ciki da kara cin French league 1 da French Cup.

    Haka kuma ƙungiyar ta Sifaniya ta kai wasan karshe a Club World Cup, kofin da Chelsea ta lashe a watan Yuni a Amurka.

  11. Postecoglou ya bukaci magoya bayan Forest su kara hakuri

    Kociyan Nottingham Forest, Ange Postecoglou ya bukaci magoya baya su kara hakuri, bayan da har yanzu bai ci wasa ba.

    Ranar Alhamis Forest za ta karɓi bakuncin Midtjylland a Europa League a City Ground a karon farko tun bayan kusan shekara 30 rabon da ta shiga gasar zakarun Turai.

    Tsohon kociyan Celtic da Tottenham ya maye gurbin Nuno Espirito Santo a watan Satumba, amma har yanzu bai ci wasa ba.

    Ya fara da shan kashi 3-0 a gidan Arsenal, sannan Swansea ta yi waje da su daga Carabao Cup da yin canjaras a Burnley da kuma a Real Betis a Europa League na farko a bana.

    Sannan kuma Sunderland ta doke ta har gida 1-0 a Premier League a makon jiya.

    Tottenham ta kori Postecoglou kwana 16 da ya lashe Europa League.

  12. Van de Ven ya yi alfari da ya sa ƙyallen kaftin a Tottenham

    Micky van de Ven ya ce ya yi alfaharin da ya ɗauka ƙyallen kyaftin din Tottenham a karon farko a ranar Talata a Champions League.

    An tashi kunnen doki 2-2 a gidan Bodo/Glimt.

    An bai wa Van de Ven ƙyaftin ne a wasan sakamakon rashin Cristian Romero wanda da ya ji rauni .

  13. Waɗansu majiyoyi daga cikin Old Trafford na cewa mahukuntan Machester United na tunanin kocin ƙungiyar ɗan ƙasar Portugal Ruben Amorim, mai shekaru 40, zai iya yin murabus tun kafin a kai ga koran sa. (iPaper)

    Tottenham na cikin jerin ƙungiyoyin da ke neman ɗan wasan baya na Crystal Palace da Ingila Marc Guehi mai shekara 25. (CaughtOffside)

    Ɗan wasan tsakiya na Real Madrid ɗan ƙasar Uruguay Federico Valverde, mai shekara 27, ya kasance ɗaya daga cikin ƴan wasan da Manchester United za ta yi zawarci a bazara mai zuwa. (Fichajes)

    Kocin Tottenham Thomas Frank na sha'awar ɗaukar ɗan wasan bayan Jamhuriyar Ireland Nathan Collins, mai shekara 24, daga Brentford. (TBRFootball)

  14. An bayar da sammacin kama shugaban ƙungiyar Kasimpasa

    A ranar Laraba ne ƙungiyar da ke buga Super Lig a Turkiyya, Kasimpasa ya koma karkashin kulawar gwamnati bayan da masu gabatar da kara suka bayar da sammacin kama mai ƙungiyar a wani bincike da ake yi na zamba da karkatar da kudade.

    Matakin ya zo ne kwanaki bayan da masu gabatar da kara suka bayar da umarnin a tsare Turgay Ciner bisa laifukan da suka hada da halatta kudaden haram da zamba da kuma kafa wata kungiyar da ke aikata laifuka.

    Yanzu haka yana zaune a kasar waje kuma ba a tsare shi ba.

    Wasu kamfanoninsa da suka hada da Park Holding da Silopi Electric, an sanya su a karkashin kulawar asusun inshorar ajiya na jiha (TMSF).

    Kasimpasa mai hedkwata a Istanbul, ta samu maki takwas daga wasa bakwai a kakar bana, kuma tana matsayi na 11 a kan teburi.

    An fi sanin su da tawagar samarin shugaban kasar Turkiyya Tayyip Erdogan.

  15. ''Fifa ce mai alhakin sauya filin da za a buga kofin duniya 2026''

    Sauya wajen da za a yi wasanni daga biranen da za su karbi bakuncin gasar cin kofin duniya a 2026 ya zama hukunci FIFA, ba na Donald Trump ba, in ji mataimakin shugaba, Victor Montagliani.

    Shugaban Amurka ya yi magana a makon da ya gabata game da yiwuwar ɗauke wasanni daga garuruwan da ya dauka "masu hadari".

    Shugaban FIFA, Gianni Infantino ya kulla alaka da Trump, inda Amurka za ta yi haɗakar karɓar bakuncin kofin duniya tare da Canada da kuma Mexico.

    Filin Lumen na Seattle na shirin karbar bakuncin wasa shida tare da filin wasa na Levi a Santa Clara - awa ɗaya daga San Francisco - wanda zai karɓi bakuncin wani wasa shida.

  16. Tino Livramento zai yi jinyar mako takwas, Newcastle United

    Ɗan wasan Newcastle United, Tino Livramento zai yi jinyar mako takwas, bayan raunin da ya ji a wasa da Arsenal a Premier League ranar Lahadi a St James Park.

    Sai ɗaukar ɗan wasan tawagar Ingila mai shekara 22 aka yi a kan gadon marasa lafiya a karawar da Arsenal ta yi nasarar cin 2-1.

    Kociya, Eddie Howe ya ce gwajin girman raunin da aka yi, watakila mai tsaron bayan ya yi jinyar mako shida zuwa takwas.

    Kenan watakila ba zai buga wasa 11 ba daga ciki har da na Champions League da na Union Saint-Gilloise da na Benfica da na Athletic Bilbao da na Marseille da wanda tawagar Ingila za ta yi a neman shiga gasar kofin duniya da Latvia da Serbia da Albania da kuma na sada zumunta da Wales.

  17. Kungiya uku daga Premier za ta buga Champions League ranar Laraba, Champions League

    Za a ci gaba da gasar Champions League a daren Laraba, inda za a yi fafatawa tara daga ciki ungiyoyin Premier League uku za su yi wasa.

    Newcastle ta je Belgian domin karawa da Union St-Gilloise.

    Wannan shi ne karon farko da ƙungiyoyin za su fuskanci juna a gasar zakarun Turai.

    Manchester City ta ziyarci Monaco.

    Wannan shi ne karo na uku da za su kece raini a Champions League.

    2016/2017

    Champions League Laraba 15 ga watan Maris ɗin 2017

    • Monaco 3-1 Manchester City

    Champions League Talata 21 ga watan Fabrairun 2017

    • Manchester City 5-3 Monaco

    Arsenal za ta yi wa Olympiakos masauki a Emirates.

    Wannan shi ne karo na 13 da za su buga gasar zakarun Turai ko ta Europa a tsakaninsu.

    Arsenal da Olypiakos kowacce ta ci wasa shida ba canjaras a tsakaninsu.

  18. Ɗan wasan tsakiya na Tottenham da Uruguay Rodrigo Bentancur, mai shekara 27, ya gab da ƙulla sabuwar yarjejeniya da kulob ɗin na arewacin Landan (Football.London)

    Ɗan wasan tsakiya na Barcelona Dro Fernandez, mai shekara 17, ba shi da niyyar sauraron duk wani tayin da za a yi masa daga ƙasashen waje, duk da cewa Arsenal da Chelsea da Manchester City na zawarcin sa. (TBRFootball)

    Fulham na shirin zawarcin ɗan wasan Middlesbrough ɗan ƙasar Ingila Hayden Hackney, mai shekara 23. (Football League World)

  19. Wasannin Champions Leagye ranar Laraba

    Za a ci gaba da wasannin Champions League da za a yi tata burza tara ranar Laraba.

    Wasu daga wasanin da za a buga:

    • Arsenal da Olympiacos
    • Barcelona da Paris St German
    • Borussia Dortmund da Athletic Bilbao
    • Monaco da Manchester City -
    • Napoli da Sporting - Union Saint Gilloise da Newcastle
    • Villarrea da Juventus.
  20. Alisson ba zai buga wa Liverpool wasan da za ta yi da Chelsea ba

    Kociyan Liverpool, Arne Slot ya ce mai tsaron raga, Alisson ba zai buga wasa da Chelsea ba ranar Asabar a Premier League, ɗan kasar Brazil ya ji rauni a wasan Champions League da Galatasaray.

    An canja ɗan ƙwallon mai shekara 32 da Giorgi Mamardashvili a minti na 56 a wasan da aka doke Liverpool 1-0 a Instanbul ranar Talata.

    Alisson ya ji rauni lokacin da ya tare ƙwallon da Victor Osimhen ya buga masa, haka shima Hugo Ektike sai canja shi aka yi.

    Kenan watakila Mamardashvili ya fara tsare ragar Liverpool a karon farko a Premier League a Stamford Bridge.

    Golan ɗan kasar Georgia ya koma Anfield daga Valencia kan fara kakar bana.

    Alisson wanda ya sha jinya a bara, bai buga wasa 10 ba a Premier League.

    Ana kuma cewa da ƙyar ne idan Ekitike zai buga karawar.