Lamine Yamal zai sake yin jinyar mako uku

Asalin hoton, EPA
Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Barcelona ta ce ɗanwasan gabanta Lamine Yamal zai yi jinyar mako uku sakamakon raunin da ya ji a mararsa.
Wata sanarwa da ƙungiyar ta wallafa a shafukanta na sada zumunta ta ce matashin ɗanwasan mai shekara 18 ya ji raunin ne yayin wasansu da PSG a gasar zakarun Turai ta Champions League.
"Rashin jin daɗin da Lamin e Yamal ya ce yana fuskanta ya sake dawowa bayan wasa da PSG," in ji sanarwar.
"Ba zai buga wasa da Sevilla ba, kuma ana sa ran zai yi jinyar mako biyu zuwa uku."
Kazalika, akwai fargabar ko Yamal zai yi murmurewar da za ta ba shi damar buga wasan hamayya na El Clasico ranar 26 ga watan Oktoba, wanda Real Madrid za ta yi wa Barca masauki a filin wasa na Santiago Bernebeu.
A ranar 28 ga watan Satumba ne Yamal ya koma taka wa Barca leda bayan jinyar da ya yi.















