Osimhen ya tara wa Liverpool gajiya a Champions League
Liverpool ta sha kashi sau biyu a jere bayan da Galatasary ta yi mata kancal a karawa ta biyu a gasar zakarun Turai da aka yi a Istanbul.
Dan wasan Galatasary Victor Osimhen ne ya zura kwallo a ragar Liverpool bayan minti 16 da fara wasa
Bayan komawa daga hutun rabin lokaci mai horas da Liverpool Arne Slot ya sako ‘yan wasansa da yake ji da su Mohammed Sallah da kuma Alexander Isak domin ganin ko zai ceto kungiyar tasa daga nutsewa to amma bakin alkalami ya riga ya bushe.
A can cikin wasa har Liverpool ta sa ran farkewa a lokacin da lafari ya hura fanareti lokacin da Ibrahima Konate ya fadi a gaban raga, sai dai bayan dubawa da kyau a VAR, lafari ya sauya matsayarsa ya ce babu fawul.
Osimhen ne aka ba dan wasa mafi hazaka a karshen wasan.
Real Madrid ta sauke fushinta kan Almaty
Bayan kwasan kashinta a hannu cikin karshen mako, Real Madrid ta bi kungiyar Almaty ta kasar Kazakhstan har gida ta huce haushi a kanta da ci 5 da babu.
Dan wasa Kylian Mbape ne ya barje guminsa a wasan inda ya zura kwallo daidai har uku.
Mbape ya zura ta farko a minti na 25 ta hanyar bugun fanareti, sannan ya kara zura wata a minti na 52 kafin ya ci ta karshe a minti na 73.
Camavinga ya zura tasa kwallon a minti na 83 yayin da Brahim Diaz ya cike ta biyar a minti ma 93, dab da hura tashi.
Mourinho bai sha da dadi ba a Stamford Bridge
Chelsea ba su yi wa Mourinho kara ba a wannan karo inda suka yi nasara kan Benfica, kungiyar da Mourinho ya fara horaswa a kwanan nan bayan ya baro Turkiyya.
Ita ma Chelsea din ta sha ne da kyar bayan da dan wasan Benfica Richard Rios ya zura kwallo a ragar kungiyarsa
A sauran wasannin:
Pafos 1-5 Bayern Munich
Bodo/Glimt 2-2 Tottenham
Atalanta 2-1 Club Brugge
Atletico Madrid 5-1 Eintracht Frankfurt
Inter 3-0 Slavia Prague
Marseille 4-0 Ajax