Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 10/09/2025.

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 10/09/2025.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Daga Usman Minjibir, Aisha Babangida da Umar Mika'il

  1. Hotunan harin Rasha da jiragen yaƙi marasa matuƙa kan Kyiv

    Harin da Rasha ta kai da jiragen yaƙi marasa matuƙa a daren jiya kan Kyiv ya kai ga ketarewar iyakar sararin samaniya ta ƙasar Poland.

    Ga wasu hotuna daga Kyiv a daren, inda aka ga fashe-fashe a sararin samaniya yayin da sojojin Ukraine ke harba wuta kan jiragen

  2. NUPENG ta dakatar da yajin aiki bayan cimma matsaya da kamfanin Dangote

    Ƙungiyar ƙwadago ta ma'aikatan dakon man fetur da iskar gas a Najeriya, NUPENG ta dakatar da yajin aikin da ta shirya bayan cimma matsaya da kamfanin Dangote Refinery kan ’yancin mutane na kafa ƙungiya.

    Wanne na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da NUPENG ɗin ta fitar a shafinta na X.

    Cimma matsayar ya biyo bayan ganawa ta musamman da hukumar DSS ta kira, tare da halartar Ministan Kuɗi, Wale Edun, da shugabannin NLC da TUC.

    A cikin yarjejeniyar da aka sanya hannu, an amince cewa ma’aikatan kamfanin da ke son shiga ƙungiya za su samu damar yin hakan, tare da fara tsarin nan take da kuma kammala shi cikin makonni biyu.

    a cewar yarjejeniya, babu wani ma'aikacin Dangote da za zalunta saboda sanarwar yajin aikin.

    Da wannan matsaya, NUPENG ta dakatar da yajin aikin da ta shirya gudanarwa, yayin da ɓangarorin biyu za su koma wurin Ministan Ƙwadago bayan mako guda domin bayar da rahoto

  3. Yadda wani gungu ke yaɗa ƙiyayya ga musulunci a Gaza - Binciken BBC

    Wani bincike da BBC ta gudanar ya gano cewa kamfanin da ke samar da tsaro da kariya ga wuraren da ake raba kayan agaji a Gaza na amfani da wasu 'yan kungiyar yan daba ta Amurka da ke da tarihin kiyayya ga musulunci.

    BBC ta tabbatar da cewa mutanen biyu na aiki ne da cibiyar raba kayan agaji ta Gaza da ake kira GHF, wadda Isra'ila da Amurka ke daukar nauyi.

    Wakilin BBC ya ce yanzu haka akwai saƙwnani iri-iri na nuna ƙyamar musulunci da musulmai a shafin kungiyar yan daban na Facebook, kuma mun iya gano mutum goma daga cikin 'ya'yan kungiyar da ke aiki da GHF.

    GHF dai ta ce ba ta tantance wadanda take dauka aiki kan ragowar bangarorin rayuwarsu, sabanin abun da aka ɗauke su aiki su yi.

    Ta ce ba ta lamuntar duk wani ra'ayi na nuna kiyayya ga wani bangare.

  4. Spain ta hana wasu ministocin Isra’ila biyu shiga ƙasar bisa rikicin Gaza

    Gwamnatin Spaniya ta haramtawa wasu ministocin Isra'ila biyu masu tsatsauran ra'ayi shiga Spain a wani ɓangare na matakan kawo ƙarshen yaƙin Gaza.

    Madrid ta yi imanin Isra'ila na aikata kisan kiyashi a Gaza, wani abu da Isra'ilar ta sha musantawa.

    Ministan harkokin wajen Spaniya ya ce, za a kuma sanya wa ministan tsaron kasar Isra'ila biyu, Itamar Ben-Gvir, da ministan kudi, Bezalel Smotrich takunkumi.

  5. Trump ya soki harin Isra’ila a Qatar, ya ce ya lalata tattaunawar tsagaita wuta

    Shugaban Amurka Donald Trump ya jaddada cewa ko kaɗan bai ji dadin harin da Isra'ila ta kai wa shugabannin Hamas a Qatar ba.

    Ya bayyana hakan ne yayin wani jawabi a taƙaice ga yan jarida a birnin Washington.

    Tun da farko, ya dage cewa Isra'ila ba ta sanar da shi a kan lokaci don gargadin Qatar kafin lokaci ya kure ba.

    A yanzu, duk wata dama da Amurka ke da ita ta cimma yarjejeniyar tsagaita wuta ta kuɓuce, wannan hari ne da Isra'ila ta kai don maida martani kan abun da ya faru a ranar bakwai ga watan Oktoba.

    Firaiministan Qatar Sheikh Mohammed bin Abdulrahman Al-Thani, ya bayyana abin da Isra'ila ta yi a matsayin yaudara tsagwaronta.

    Ya ce manufar ita ce yin zagon kasa ga tattaunawar tsagaita bude wuta a Gaza.

  6. Assalamu Alaikum

    Barkanmu da sake saduwa a shafin labarai kai-tsaye na BBC Hausa a hantsin Laraba

    Shafin na yau zai fi mayar da hankali ne kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da maƙwabtanta, da kuma sauran sassa na duniya.

    Za ku iya leƙawa shafukan sada zumuntanmu na intanet, da facebook da X da kuma whatsapp domin karanta sauran labarai da kallon bidiyo.

    Ku kasance da mu.