Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 10/09/2025.

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 10/09/2025.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Daga Usman Minjibir, Aisha Babangida da Umar Mika'il

  1. Ƴansandan Faransa sun kama masu zanga-zangar adawa da gwamnati 500

    Ƴansanda sun kama aƙalla mutum 500, a zanga-zangar ƙin jinin gwamnati da ake yi a wasu sassan Faransa, ciki har da birnin Paris.

    Ƴansandan sun harba barkonon tsohuwa da feshin ruwan zafi a birnin Montpellier da ke kudancin ƙasar, yayin da aka ƙona wata motar bas a Rennes da ke yammaci.

    Wata sabuwar ƙungiya mai suna ''Lets Block Everything'', ma'ana ''mu datse komai'' ce ta shirya zanga-zangar.

    Ɗaya daga cikin masu zanga-zangar ta bayyana cewa tana son gwamnati ta saurare su don ɗaukar matakan taimaka wa Falasɗinawa da ƴan kongo.

    Ta ƙara da cewa masu zanga-zangar na kuma son kawo ƙarshen wariyar launin fata.

  2. Yara miliyan 80 ne ke amfana da shirin ciyarwa a makarantu a duniya - WFP

    Majalisar Dinkin Duniya ta ce ƙananan yara miliyan 80 ne ke cin gajiyar shirin ciyar daɗalibai a makarantu da ake yi a sassa daban-daban na duniya.

    Shirin Samar da Abinci na Majalisar Dinkin Duniya, WFP ya ce hakan na nufin an samu ci gaba a ƙoƙarin da ake yi na yaƙi da yunwa da ke addabar ƙananan yara, da inganta abinci mai gina jiki da suke ci, da samun damar zuwa makaranta musamman a ƙasashe matalauta.

    Nazarin da hukumar ta yi kan yanayin yadda ciyarwa a makarantu take a duk faɗin duniya ya nuna cewa an fi samun ci gaba a ƙasashe matalauta inda yawan makarantun da ke ciyarwar ya ƙaru da kashi 60% cikin shekaru biyu kawai.

    Wannan ne ya kawo adadin yaran da ake ciyarwa a makarantu a duk faɗin duniya zuwa miliyan 466.

    Nahiyar Afirka ce kan gaba wajen samun wannan gagarumin ci gaba inda aka samu ƙarin yara miliyan 20 da suka samu shiga jerin masu amfana daga shirin ciyarwa a makarantu da gwamnatocin ƙasashensu suka fito da shi musamman a ƙasashen Kenya, da Madagascar da Ethiopia da kuma Ruwanda.

    Rahoton ya nuna cewa samar da kuɗaɗe domin ciyarwa a makarantu ya ninka cikin shekaru huɗu daga Dala Biliyan 43 a shekarar 2020 zuwa Biliyan 84 a wannan shekara ta 2025, kuma kusan dukkanin kuɗaɗen sun fitowa ne daga hannun gwamnatoci a maimakon ƙungiyoyin bayar da agaji.

  3. Poland ta yi gargaɗin faɗawa yaƙi bayan jiragen Rasha sun keta samaniyarta

    Firaministan Poland Donald Tusk ya ce ƙasar na dab da fara yaƙin gaba da gaba a yanzu, fiye da kowane lokaci tun bayan yaƙin duniya na biyu.

    Poland ta ce jirage marasa matuƙa na Rasha sun keta sararin samaniyar ta a lokacin da ta ke kai hare-hare kan Ukraine cikin dare.

    Jirajen yaƙin ƙungiyar tsaro ta NATO da na Poland sun kakkaɓo wasu daga cikinsu.

    Ma'aikatar tsaron Rasha ta ce ba ta yi niyyar kai hari kan Poland ba, sai dai ba ta musanta cewa jiragenta sun shiga sararin samaniyar Poland ba.

    Ministan harkokin wajen Poland ya ce babu shakka harin da gangan ne ba kuskure ba, saboda jirage 19 ne suka keta sararin samaniyar ƙasar.

  4. Muna tattaunawa da ƙawayenmu kan martanin harin Isra'ila - Qatar

    Firaministan Qatar Sheikh Mohammed bin Abdulrahman al-Thani ya ce ƙasar na tattaunawa da ƙawayenta a yankin Gabas ta Tsakiya game da matakin da za ta ɗauka kan harin da Isra'ila ta kai wa jagororin Hamas a birnin Doha.

    Yayin wata hira da kafar yaɗa labarai ta CNN, Sheikh Abdulrahman al-Thani ya ce a yanzu Qatar na sake nazarin komai game da matsayinta na mai shiga tsakani, da kuma makomar ƙungiyar Hamas a ƙasarta.

    A baya-bayan na Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce dole ne Qatar da wasu ƙasashe da ya bayyana da zama mafakar ƴan'ta'adda su kore su daga ƙasashensu ko su gurfanar da su a gaban shari'a.

    Yana mai cewa matsawar ba su yi haka ba, to Isra'ila za ta yi hakan da kanta.

  5. Isra'ila ta ƙaddamar da ƙarin hare-hare kan mayaƙan Houthi a Yeman

    Rundunar sojin Isra'ila, IDF ta ce kai hare-hare kan sansanonin mayaƙan Houthi a Sana'a, babban birnin Yemen da kuma Al-Jawf, ciki har da sansanonin sojin ƙungiyar da kuma shalkwatar abin da Isra'ila ta kira sashen yaɗa farfagandar sojin Houthi da kuma rumbunan ajiyar man fetur.

    Ma'aikatar lafiyar Houthi ta ce aƙalla mutum 35 aka kashe yayin da wasu fiye da 130 suka jikkata.

    Bidiyoyin da aka yaɗa a shafukan sada zumunta sun nuna yadda aka samu mummunar fashewa a Sana'a.

    Hare-haren na zuwa ne bayan da a ƴan kwanakin nan ƙungiyar Houthi ta harba makamai masu linzami masu yawa da jirage marasa matuƙa kan Isra'ila.

    A watan da ya gabata kuma Isra'ila ta ƙaddamar da hare-hare ta sama kan manyan jagororin ƙungiyar Houthi, tare da kashe wasu daga cikinsu, ciki har da wanda ya ayyana kansa a matsayin firaministan gwamnatin ƙungiyar.

  6. Ghana ta yi Allah wadai da jharin Isra'ila a Qatar

    Gwamnatin ƙasar Ghana ta yi Allah wadai da hare-haren da Isra'ila ta ƙaddamar kan Qatar a jiya Talata.

    Cikin wata sanarwa da ma'aikatar harkokin wajen ƙasar ta fitar, gwamnatin ta ce hare-haren sun saɓa wa dokokin duniya, kuma keta keta alfarmar Qatar ne.

    ''Gwamnatin Ghana ta damu matuƙa game da tasirin da harin zai iya yi kan yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin Isra'ila da Falasɗinawa'', in ji shi.

    Gwamnatin Ghanar ta kuma yi kiran fifita tattaunawa wajen magance yaƙin da ake yi tsakanin Isra'ila da Hamas.

    Sanarwar ta kuma yaba wa hukumomin Qatar bisa jajirwar da ta ce ƙasar na yi wajen ganin an kawo ƙarshen yaƙin, tare da nanata kira ga Qatar cewa kada ta bari wannan hari ya sanyaya mata gwiwa kan ƙoƙarin da take yi wajen ganin an cimma yarjejeniyar tsagaitawa ta hanyar diplomasiyya.

    ''Muna kuma kiran amfani da diplomasiyya don sakin duka Isra'ilawan da Hamas ke garkuwa da su, tare da jaddada daɗaɗɗen goyo bayanta ga shirin samar da ƙasashe biyu'', in ji sanarwar.

    Wannan matsayi da Ghana ta ɗauka na zuwa ne bayan da a watan da ya gabata ƙasar ta tallafa wa Falasɗinawa da alewar cakuleti da wasu abubuwan da aka samar daga cocoa da nauyinsu ya kai metric tan 40 ta hannun jakadan Falasɗinawa a Ghana, Abdul Fattah Ahmed Khalil al-Sattari.

  7. INEC ta amince da David Mark a matsayin shugaban jam'iyyar ADC na ƙasa

    Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Najeriya ta amince da jagorancin jam'iyyar ƴan haɗaka ta ADC, ƙarƙashin shugabancin tsohon shugaban Majalisar Dattijan Najeriya, David Mark

    Hakan na zuwa ne bayan fafutikar da haɗakar ƴan'adawa na ƙasar ke yi wajen ganin sun yi abin da suka kira "inganta jam'iyyar" domin tunkarar babban zaɓen ƙasar na shekara ta 2027.

    A ranar 2 ga watan Yulin wannan shekara ne haɗakar ƴan hamayyar siyasa na Najeriya suka ayyana ADC a matsayin jam'iyyar da za su yi amfani da ita, tare da bayyana Sanata David Mark da Rauf Aregbesola a matsayin shugaba da kuma sakataren jam'iyyar na ƙasa.

    Sai dai duk da haka an shafe tsawon lokaci babu sunan sabbin shugabannin da aka ayyana a shafin na hukumar Inec.

    Sauran waɗanda sunayensu suka bayyana a shafin intanet ɗin na Inec a matsayin shugabannin ADC su ne:

    Ibrahim Ahmad Mani a matsayin ma'aji, Akibu Dalhatu a matsayin sakataren kuɗi da kuma Oserheimen Aigberaodion Osunbor a matsayin mai bayar da shawara kan harkokin shari'a.

    Gamayyar ƴan adawar ta Najeriya sun haɗe a jam'iyyar ne domin ƙalubalantar shugaban ƙasar mai ci Bola Tinubu wanda ya hau mulki a shekarar 2023 bayan lashe babban zaɓen ƙasar.

    Bayan hawa kan mulki, Tinubu ya ɗauki manyan matakai da dama wadanda suka sauya rayuwar al'ummar ƙasar, kamar cire tallafin man fetur da kuma sauye-sauye a fannin kuɗi.

    Kusan a yanzu ɗaukacin manyan jam'iyyun siyasa na ƙasar na fama da rikici na cikin gida, inda suke zargin jam'iyyar APC mai mulkin ƙasar da yi musu zagon ƙasa.

  8. Tinubu ya gana da shugaban Faransa Emmanuel Macron

    Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya gana da shugaban Faransa Emmanuel Macron a wani ɓangare na hutun aiki da yake yi a ƙasashen Turai.

    Nai magana da yawun shugaban Najeriya, Bayo Onanuga ya wallafa hotunan yadda Tinubu ya yi ganawar da Macron a yau Laraba.

    Sanarwar ta ce "Macron ya karɓi baƙuncin Tinubu domin cin abincin rana a fadar Elysee" da ke birnin Paris.

    A makon da ya gabata ne shugaban na Najeriya ya sanar da fara hutun kwana 10, daga cikin hutunsa na shekara, inda ya bar Najeriya a ranar Alhamis.

    Fadar shugaban ƙasar ta ce Tinubu zai yi hutun nasa ne a ƙasashen Birtaniya da kuma Faransa.

    Tun bayan hawan sa mulki, Tinubu ya yi tafiye-tafiye da dama zuwa Faransa, inda ya yi ganawa daban-daban da shugaban ƙasar Emmanuel Macron.

    Alaƙa ta yi tsami tsakanin Faransa da ƙasashen Afirka da dama waɗanda ta yi wa mulkin mallaka, inda tuni hulɗar diflomasiyya da ta soji ta tsinke tsakaninta da su.

    Cikin irin waɗannan ƙasashe har da maƙwafciyar Najeriya - Jamhuriyar Nijar - inda sojoji suka tuntsurar da gwamnatin farar hula a watan Yulin shekara ta 2023.

  9. Babban layin lantarkin Cuba ya faɗi karo na huɗu cikin shekara guda

    Ƙasar Cuba na fama da ɗaukewar wutar lantarki a faɗin ƙasar karo na huɗu cikin shekara guda.

    Ma'aikatar makamashin ƙasar ta ce lamarin ya faru ne sakamakon katsewar babban layin wutar lantarkin ƙasar.

    Ma'aitara ta ce yawaitar faɗuwar babban layin ba ya rasa nasaba da tsufansa da kuma rashin sabunta shi.

    Yawaitar faɗuwar babban layin ashekarar da ta gabata ya haifar da zanga-zangar adawa da gwamnati.

  10. Mutanen da Isra'ila ta kashe a Gaza sun kai 64,656, in ji ma'aikatar lafiya

    Ma'aikatar lafiya ta Gaza ta ce hare-haren Isra'ila sun sake kashe mutum 41 a zirin cikin awa 24 da suka gabata.

    Adadin ya sa jimillar mutanen da Isra'ila ta kashe sakamakon tun daga watan Oktoban 2023 zuwa aƙalla 64,656, a cewarta.

    Ta ce akwai mutane da dama a ƙarƙashin ɓaraguzai bayan harin na baya-bayan nan kuma ma'aikatan agaji sun kasa kaiwa gare su.

    Sai dai alƙaluman ba su bambance tsakanin mayaƙa da fararen hula ba.

  11. Huriwa ta caccaki gwamnatin Anambra kan harbin ƴan kasuwa a Onitsha

    Ƙungiyar kare haƙƙi ta Human Rights Writers Association of Nigeria (Huriwa) ta yi Allah wadai da abin da ta kira kisan gillar da jami’an tsaro na jihar Anambra suka yi wa ’yan'kasuwa a Onitsha.

    Cikin wata sanarwa, shugaban ƙungiyar Emmanuel Onwubiko ya ce gwamnatin Gwamna Charles Chukwuma Soludo "ta gaza wajen tabbatar da kariya ga ’yan ƙasa, maimakon haka ta bai wa wasu dakarun da ta kafa makamai da ake amfani da su wajen kashe talakawa".

    Rahotanni sun bayyana cewa dakarun Ocha Brigade, rundunar da gwamnatin jihar ta kafa domin aiwatar da dokokin muhalli, sun buɗe wuta a kasuwar Onitsha Main Market da ke kwaryar birnin jihar.

    Harin ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama, ciki har da wata mace mai juna biyu, tare da jikkata wasu da dama, a cewar rahotonnin.

    “Wannan abin takaici ne. Mutum huɗu sun bar gidajensu da safe domin neman abinci amma an harbe su. Hatta mace mai ciki ta shiga cikin waɗanda aka kashe. Mutanen Anambra yanzu suna rayuwa cikin tsoro saboda gwamnati ta bai wa ’yandaba bindiga da rigunan hukuma," in ji Huriwa.

    Ƙungiyar ta kuma buƙaci a gurfanar da jami’an da ake zargi da yin harbe-harben a gaban kotu.

  12. Jamus ta ce jiragen Rasha da suka shiga Poland tsokana ce 'da gangan'

    Wakilin ƙasar Jamus Jens Plötner ya ce abi da Rasha ta aikata "tsokana ce da gangan" kan Poland da kuma ƙawancen Nato "gaba ɗaya".

    Ya ce hakan ya jawo rukunin ƙasashe biyar na E5 "sun ɗauki mataki cikin hanzari".

    Bayan ganawar da suka yi a yau Laraba, Plötner ya ce ƙasashen na aikata saƙon da ke nuna haɗin kansu wajen goyon bayan Ukraine.

    Ya ƙara da cewa ganawar "ta nemo sababbin hanyoyi ce da kuma sauyi".

  13. Babban layin wutar lantarkin Najeriya ya sake lalacewa

    Yawan wutar lantarkin da Najeriya ke samarwa ya faɗo daga megawatts 2,917.83 zuwa megawats 1.5 a tsakanin ƙarfe 11 da 12 na safiyar ranar Larabar nan.

    Jim kaɗan bayan lalacewar, shafin na babban layin wutar Najeriya na X ya bayar da muhimman bayanai dangane da al'amarin inda ya ce aikin ƙoƙarin shawo kan matsalar na ci gaba.

    Bayanai sun nuna cewa kusan dukkannin tashoshin samar da wutar lantarki idan ban da na Ibadan sun zama ba tare da wutar ba.

    Da yake tabbatar da al'amarin, kamfanin samar da wutar lantarki na babban birnin tarayya wato Abuja Disco ya tabbatar wa da abokan hulɗarsa cewa yana ƙoƙarin ganin ya sha kan matsalar.

    “Ya ku abokan hulɗarmu, muna son sanar da ku cewa rashin wutar da ake fuskanta na faruwa sakamakon rashinta daga babban layin wutar na ƙasa tun daga ƙarfe 11:23 na safiyar yau ɗin nan."

  14. Kotu ta ƙi bayar da belin waɗanda ake zargi da hannu a harin cocin Owo

    Babbar kotun Tarayya da ke Abuja ta ƙi bayar da belin mutum biyar da ake tuhuma da shirya harin da aka kai a cocin Katolika ta Owo dake jihar Ondo, kamar yadda gidan talabijin na Channels ya ruwaito.

    Hukumar tsaro ta farin kaya DSS ta gabatar da mutum biyar ɗin ne a gaban alƙalin Kotun, Emeka Nwite, a ranar 11 ga Agusta, 2025, kan zargin hannunsu a harin da aka kai cocin a ranar 5 ga Yuni, 2022.

    Mutanen da ake tuhuma za su fuskanci shari’a kan harin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutum sama da 40 tare da jikkata fiye da 100.

    A lokacin sauraron ƙarar, Alƙalin Kotun, ya ƙi amincewa da belin, inda ya bayyana cewa laifin da ake tuhumarsu da shi yana da nauyi sosai.

    Alkalin ya kuma jaddada yiwuwar cewa waɗanda ake tuhuma za su iya tsoratar da shaidu su rinjayi shari’a, ko su tsere idan aka sake su.

    Alƙalin ya kuma amince da hujjojin DSS, wadda ta ce akwai hujjoji masu ƙarfi a kan waɗanda ake tuhuma.

  15. Mutum 12 sun mutu a hatsarin tankar gas a Imo

    Wata tankar gas ta ci karo da mota a kan Owerri/Onitsha Expressway a Jihar Imo, inda mutum 12 suka mutu ciki har da yara 4 da manya 8., kamar yadda gidan talabijin Channels ya ruwaito.

    Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar Imo, Henry Okoye, ya ce wasu mutum 8 kuma sun jikkata, kuma suna samun kulawa a Asibiti.

    ‘Yan sanda sun fara bincike kan hadarin, yayin da aka ci gaba da bin titin bayan share tarkace daga hatsarin da ya faru.

    Kwamishinan ƴan Sanda, Aboki Danjuma, ya tura gaisuwar ta’aziyya ga iyalan mamatan, tare da gargadin direbobi da kada su yi tuƙi a kan hanyar da ba ta dace ba.

  16. Dabaru takwas na samun tsawon rai

    Najeriya na daga cikin ƙasashen da mutanenta suka fi ƙarancin tsawon rai, kamar yadda rahoto ya bayyana.

    Baya ga Najeriya, ƙasashe da dama na Afirka, kudu da hamadar Sahara na cikin wannan jeri: kamar Chadi, Sudan ta Kudu, Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, Mali, Guinea, Burkina Faso da kuma Somalia.

    A irin waɗannan ƙasashe adadin shekarun rayuwar a'ummarsu kan kama ne daga 61.3 zuwa 54.6 ya zuwa shekara ta 2025.

  17. 'Jiragen yaƙi marasa matuƙa 19 na Rahsa sun ƙetare sararin samaniyar Poland'

  18. Adadin yaran da ke fama da matsananciyar ƙiba ya zarce na marasa nauyi a duniya

  19. Wasu masu neman dama ne suka ƙwace zanga-zangarmu - Matasan Nepal