Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Najeriya ta amince da jagorancin jam'iyyar ƴan haɗaka ta ADC, ƙarƙashin shugabancin tsohon shugaban Majalisar Dattijan Najeriya, David Mark
Hakan na zuwa ne bayan fafutikar da haɗakar ƴan'adawa na ƙasar ke yi wajen ganin sun yi abin da suka kira "inganta jam'iyyar" domin tunkarar babban zaɓen ƙasar na shekara ta 2027.
A ranar 2 ga watan Yulin wannan shekara ne haɗakar ƴan hamayyar siyasa na Najeriya suka ayyana ADC a matsayin jam'iyyar da za su yi amfani da ita, tare da bayyana Sanata David Mark da Rauf Aregbesola a matsayin shugaba da kuma sakataren jam'iyyar na ƙasa.
Sai dai duk da haka an shafe tsawon lokaci babu sunan sabbin shugabannin da aka ayyana a shafin na hukumar Inec.
Sauran waɗanda sunayensu suka bayyana a shafin intanet ɗin na Inec a matsayin shugabannin ADC su ne:
Ibrahim Ahmad Mani a matsayin ma'aji, Akibu Dalhatu a matsayin sakataren kuɗi da kuma Oserheimen Aigberaodion Osunbor a matsayin mai bayar da shawara kan harkokin shari'a.
Gamayyar ƴan adawar ta Najeriya sun haɗe a jam'iyyar ne domin ƙalubalantar shugaban ƙasar mai ci Bola Tinubu wanda ya hau mulki a shekarar 2023 bayan lashe babban zaɓen ƙasar.
Bayan hawa kan mulki, Tinubu ya ɗauki manyan matakai da dama wadanda suka sauya rayuwar al'ummar ƙasar, kamar cire tallafin man fetur da kuma sauye-sauye a fannin kuɗi.
Kusan a yanzu ɗaukacin manyan jam'iyyun siyasa na ƙasar na fama da rikici na cikin gida, inda suke zargin jam'iyyar APC mai mulkin ƙasar da yi musu zagon ƙasa.