Harin bam a mota ya kashe wani janar ɗan Rasha

Asalin hoton, Russia's Investigative Committee
Jami'ai a Rasha sun ruwaito cewa wani janar ɗan Rasha ya mutu sakamakon fashewar bam da aka dasa a ƙarƙashin motarsa a birnin Moscow, a cewar jami’ai.
Kwamitin bincike na Rasha ya ce Laftanar Janar Fanil Sarvarov, mai shekaru 56, ya rasu da safiyar Litinin bayan da aka dasa masa bam ƙarƙashin motarsa.
Sarvarov shi ne shugaban sashen horas da aikin soja na rundunar sojin Rasha, in ji kwamitin.
Hukumomin sun ce ɗaya daga cikin ra’ayoyin da ake bincike a kai shi ne yiwuwar dasa bam ɗin da hannu ko taimakon jami’an leƙen asirin Ukraine.
Ukraine ba ta yi wata magana ba game da lamarin.



