Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 05/12/2025.

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 05/12/2025.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Daga Aisha Babangida da Isiyaku Muhammad

  1. Modi da Putin sun tattauna kan yaƙin Ukraine da batun zaman lafiya

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Rasha Vladimir Putin na ci gaba da ziyararsa ta kwana biyu a India suka yi magana da manema labarai daga Hyderabad House a Delhi, wurin da ake gudanar da tattaunawarsu ta ƙula alaƙa da junansu.

    A jawabinsa na farko da aka watsa a talabijin, Putin ya ce Rasha na aiki kan “warware rikicin Ukraine ta hanyar zaman lafiya”, sannan ya gode wa India bisa ƙoƙarinta kan lamarin.

    Modi kuwa ya ce India ba ta tsaya a gefe ba game da yaƙin, inda ya jaddada cewa tana goyon bayan ɓangaren neman zaman lafiya.

    Ya ce dole ne a kawo ƙarshen yaƙin “ta hanyar tattaunawa da diflomasiyya”.

    “Muna goyon bayan warware rikicin cikin lumana,” in ji Firaministan.

  2. Ko za a iya dakatar da Shari'ar Musulunci a Arewacin Najeriya?

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Ƴan Najeriya musamman na arewacin ƙasar sun fusata dangane da bayanan da ke nuna yadda wani gungun ƴan Najeriya ya bayyana a gaban Majalisar Dokokin Amurka inda ya nuna wa majalisar cewa Shari'ar Musulunci da ake yi a arewacin Najeriya ce ke taimakawa wajen azabtar da Kiristoci a ƙasar.

    Tuni dai Majalisar Ƙoli ta addinin Musulunci da sauran ƙungiyoyin Musulmi na arewacin Najeriya suka yi kakkausan martani dangane da batun.

    Wannan ne ya sa BBC ta yi nazari kan Shari'ar ta Musulunci a tsarin kundin Mulkin Najeriya da kuma ko akwai yiwuwar cire ta daga kundin.

  3. Assalamu alaikum

    Jama'a barkanmu da wannan safiya ta Juma'a daga nan sashen Hausa na BBC, inda za mu ci gaba daga inda muka tsaya a jiya na labaran kai-tsaye na abubuwan da ke faruwa a cikin Najeriya da sauran sassan duniya.

    Za ku iya leƙawa shafukan sada zumuntanmu na intanet, da facebook da X da kuma whatsapp domin karanta sauran labarai da kallon bidiyo da tafka muhawara.