Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar 27/06/2024.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Daga Nabeela Mukhtar Uba, Umaymah Sani Abdulmumin & Abdullahi Bello Diginza

  1. 'Fiye da rabin al'ummar da suka daidaita a Sudan za su fuskanci karancin abinci'

    Hukumar kula da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce fiye da rabin al’ummar da ke yankunan da yaki ya daidaita a Sudan za su fuskanci gagarumar matsalar karancin abinci a watanni masu zuwa.

    A rahotonta na baya-bayan nan, hukumar ta ce Sudan na fuskantar tabarbarewar matsalar abinci.

    Fiye da mutum miliyan 25 ne ke fama da karancin abinci a Sudan yayin da yanayin da ake ciki a kasar ke kara dagulewa.

    Hukumar ta FAO a rahoton, ta nuna cewa wannan ce matsalar karancin abinci mafi muni da Sudan ta taba fuskanta a tarihi.

    Akwai kuma hadarin yankuna da dama a kasar za su fuskanci la’akari da karancin ruwan sama tsakanin watan Yuni da Satumba, kamar yadda hukumar ta bayyana.

    Ana dai yi ta gargadin yiwuwar durkushewar kasar idan har aka ci gaba da yaki a Sudan.

    A watan Aprilun bara ne fada ya barke tsakanin sojojin kasar da dakarun RSF.

  2. 'Mutanen da suka mutu a harin masallacin Kano ya karu zuwa 23'

    A dadin mutanen da suka mutu a gobarar masallaci da matashi Shafi'u Abubakar ya haddasa a garin Larabar Abasawa da ke ƙaramar hukumar Gezawa a jihar Kano ya karu zuwa 23 inda a yanzu mutum biyu suka rage masu rai cikin waɗanda gobarar ta yi wa illa a watan Mayun 2024.

    Wakilin jaridar Daily Trust ne ya samo bayanan a ranar Laraba bayan ziyartar asibitin Ƙwararru na Murtala Muhammad da ke jihar ta Kano inda mutanen da abin ya shafa ke samun kulawar likitoci inda ya gano cewa mutum 22 cikin 24 da aka kwantar a asibitin sun rasu.

    Mutum ɗayan da a ka kai asibitin koyarwa na Aminu Kano wanda shi ma ya samu raunuka sakamakon gobarar ya rasu wanda ya ƙara adadin mutuwar zuwa 23.

    Wakilin jaridar ya samo cewa ɗaya cikin biyun da suka rayu na ci gaba da zama a asibiti da ƙarbar kulawa yayin da aka sallami ɗayan ya koma gida.

    Rahotanni sun bayyana cewa Abubakar ya watsa fetur tare da kulle kofar wajen ibadar sannan ya cinna wa masallacin wuta yayin da mutane sama da 30 ke gabatar da sallar Asuba.

    An gurfanar da wanda ake zargi gaban babbar kotun Shari'a wadda Halhalatu Zakariya ke wa alƙalanci kuma an tsare matashin a kurkukun kotun.

  3. El Rufai ya yi riga mallam masallaci zuwa kotu – Majalisa

    ..

    Asalin hoton, El Rufai/Facebook

    Majalisar dokokin jihar Kaduna ta yi watsi da karar da tsohon gwamnan jihar Malam Nasir El-Rufai ya shigar gaban wata kotun tarayya inda yake kalubalantar rahoton Majalisar da ya zarge shi da almundahana da kuɗin gwamnati a lokacin mulkinsa.

    Shi dai tsohon gwamnan na zargin Majalisar ne da take masa hakki kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya tanadar.

    Majalisar ta musanta cewa an take masa hakki a bincikenta.

    Ita dai Majalisar dokokin jihar Kaduna a martanin da ta mayar, ta ce ta yi matukar mamaki ne yadda tsohon gwamnan ya ruga zuwa kotu, yana kalubalantar sakamakon binciken da kwamitinta ya gudanar, tana mai cewa yin hakan tamkar riga Malam Masallaci ne.

    Mai magana da yawun Majalisar dokokin jihar Kaduna, Hon Henry Maraa, ya ce an mika rahoton ne domin a ci gaba da bincike kuma "za a kira shi".

    Game da zargin El Rufai na rashin ba shi dama domin kare kansa kuwa, Hon Maraa ya kara da cewa "za a bashi dama, za a kira shi, abin da muka lura da shi shi ne wadanda suka sa hannu da wadanda suka karbi kudi, da wadanda suka ba da kudi, idan an je gaba, idan an yi bincike idan an je kan shi, za a kira shi."

    Sai dai ya ce akwai abin mamaki a ce a yanzu tsohon gwamnan yana zuwa kotu "El Rufai da bai martaba kotu ba a wayi gari shi yake zuwa kotu."

    Ya dage cewa babu kuskure a binciken da suka yi sannan za su zauna da lauyoyinsu sannan kuma su mayar masa da martani.

    A nasa bangaren, Mohammad Lawal, kakakin gwamna Uba Sani na jihar Kaduna, ya ce takaddamar da ake ciki tsakanin El Rufai da sauran jami'an gwamnatinsa da kuma majalisar dokokin jihar Kaduna ta kunshi abubuwa da yawa - zargi da badakala.

    "Ba za a yi saurin yanke hukunci ba, sai an zauna an bincika abin, sannan a gwamnatance ba wannan aikin kawai muka sa a gaba ba, ana samun wadanda suke cewa a bincika, ana samun wadanda suke cewa ba su yadda ba." in ji shi.

    Ya kara da cewa "ba za a hada baki da mu a cuci talakan jihar Kaduna ba." kamar yadda kakakin ya bayyana.

    Tun da farko dai daya daga cikin mukarraban tsohon gwamnan, ya ce bisa la’akari da suka yi cewa, Majalisar dokoki wuri ne da za a martaba doka, amma, a fahimtar su, sai ga mai dokar barci ya bige da gyangyadi, kamar yadda Malam Ja’afaru Sani tsohon kwamishina a gwamnatin El- Rufai ya shaida wa BBC.

    A cewarsa, an kafa kwamitin bisa tsarin doka don haka ya ce bai kamata ace masu doka a gwamnatin dimokradiyya na take dokokin da suka ba da yancin fadin albarkacin baki ba.

    "Abin da muke nema shi ne kotu ta yi watsi da wannan rahoto saboda ya take masa hakki." in ji Malam Jafaru Sani.

    Wannan al’amari na binciken tsohon gwamnan jihar Kadunan dai shi ne gaba-gaba cikin batutuwan da jama’a da dama a jihar ke tafka muhawara a kai, wani abu da wasu masana ke cewa manuniyace na irin wainar da za a toya a fagen siyasar jihar a zaben 2027.

  4. Sarkin musulmi na fuskantar barazanar sauke shi - Muric

    Kungiyar Musulmi ta Muric ta nuna matukar damuwa tare da gargadin cewa kujerar sarkin Sokoto na cikin barazana duk da cewa gwamnati ta musanta cewa akwai yiwuwar ta cire sarkin.

    Wannan na zuwa ne yayinda ake ta dambarwa kan kudirin neman ayi kwaskwarima kan sarautar Sokoto, wanda galibi mutane ke ganin kamar yunkuri ne na ragewa sarkin karfi ko kuma soke shi.

    Farfesa Ishaq Akintola na Muric, a wata sanarwa da ya fitar ya ce muddin kudirin ya tsallake karatu na farko da na biyu, har aka kai ga ta zama doka, to za a ragewa sarkin karfi.

    Tun soma wannan batu ake ta samu al'umma musamman manya kasa ciki harda mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima da ke gargadin gwamnatin Sokoto tare da jadadda bukatar kare masarautar da al'adun kasar Hausa.

    Gwamnatin Sokoto dai ta musanta duk wani tunani da ake yi a kanta.

  5. ...Daga Bakin Mai Ita tare da Hafsat Tugge ta Amaryar Tiktok

    Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyo
  6. An kama tsohon kwamandan soji kan yunkurin kifar da gwamnatin Bolivia

    ..

    Asalin hoton, Reuters

    An kama tsohon kwamandan sojin Bolivia saboda abin da gwamnati ta bayyana a matsayin yunkurin kifar da gwamnati.

    An tsare Janar Juan Jose Zuniga bayan da ya girke daruruwan sojoji da motocin yaki a tsakiyar birnin La Paz.

    Ya bukaci a sauya gwamnati. Shugaba Luis Arce ya nada sabbin kwamandojin soji.

    Wani sanata daga bangaren hamayya, Andrea Barrientos ya zargi shugaban kasar da hannu a kitsa kifar da gwamnatinsa a kokarin da yake na samun goyon baya a gida da kuma sauran kasashen duniya.

    An kori Janar Zuniya a ranar Talata bayan ya fada wa wani gidan Talabijin cewa zai yi duk mai yiwuwa don dakile tsohon shugaban kasar Evo Morales daga komawa kan mulki.

  7. Zanga-zangar karin kuɗin haraji na sake karaɗe Kenya

    Masu zanga-zanga a Kenya sun lashi takobin komawa kan tituna a wani shiri na ci gaba da zangar nuna kin jinin karin haraji duk da cewa shugaba William Ruto ya janye shirin na sa.

    Mista Ruto ya janye matakin ne bayan da masu zanga-zangar suka kutsa kai cikin ginin majalisar dokokin kasar a ranar Talata, lamarin da ya rikiɗe zuwa tashin hankalin da ya haifar da mutuwar samar da mutane 20.

    Ya ce jama'ar Kenya, sun nuna karara cewa basu son wannan doka, don haka an yi watsi da ita.

    Amurka ta yi yi na'am da janyewar, sai dai masu zanga zangar sun ce ko a jikinsu, don haka babu gudu ba ja da baya.

  8. Assalamu Alaikum

    Barkan ku da shigowa shafinmu na kai tsaye a yau Alhamis.

    Kuna tare da Nabeela Mukhtar Uba da Umaymah Sani Abdulmumin. Da fatan za ku kasance tare damu domin samun ƙayatattun labarai daga Najeriya da maƙwabtanta da ma sauran sassan duniya.

    Kuna kuma iya bibiyar mu a shafukanmu na sada zumunta Fesbuk da X da Instagram domin samun ƙarin wasu labaran.