Abu 5 da suka fito game da Buhari watanni biyar bayan rasuwarsa

Asalin hoton, Getty Images
Littafin da Dakta Charles Omole ya rubuta dangane da marigayi shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari ya ftio da wasu abubuwa muhimmai da ba a san su dangane da tsohon shugaban.
Littafin mai taken "Daga Soja zuwa Dattijo, Abubuwan da Muhammadu Buhari ya bari", ko kuma "From Soldier to Statesman, The Legacy of Muhammadu Buhari," ya yi waiwaye kan rayuwar Buhari daga ƙuriciya zuwa rasuwarsa.
An dai ƙaddamar da littafin ne a makon da ya gabata kuma batutuwan da ke ƙunshe a littafin sun tayar da ƙura saboda yadda littafin ya tuntuɓi makusantan Buhari walau iyali ko kuma na aiki.
BBC ta yi nutso cikin wannan littafi inda ta zaƙulo wasu abubuwan da ƴan Najeriya da dama ba su sani ba dangane da tsohon shugaban ƙasar nasu.
