Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 20/08/2024

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 20/08/2024

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Aisha Babangida, Haruna Kakangi, Isiyaku Muhammed, Umar Mikail da Ahmad Bawage

  1. Ƙungiyar ƙwadago na tattaunawa kan gayyatar da ƴansanda suka yi wa shugabanta

    ...

    Asalin hoton, NLC

    Manyan jagororin ƙungiyar ƙwadago ta Najeriya NLC da suka hada da shugabanta, Joe Ajaero, sun hallara a hedikwatar ƙungiyar ta NLC domin gudanar da wani taron gaggawa na shugabannin ƙungiyar.

    Taron ya biyo bayan sammacin da rundunar ‘yan sandan Najeriya ta yi wa Ajaero na ya gurfana a gabanta domin amsa tambayoyi kan zarge-zargen da suka shafi samar da kuɗaɗe ga ayyukan ta’addanci, da cin amanar kasa, da kuma aikata laifuka ta shafukan intanet.

    Umarnin ‘yan sanda dai ya buƙaci Ajaero ya gabatar da kansa da misalin karfe 10:00 na safiyar yau Talata domin amsa tambayoyi.

    A jiya Litinin ne aka gayyaci Ajaero ta hanyar wata wasiƙa mai dauke da sa hannun ACP Adamu Muazu a madadin mataimakin kwamishinan ƴansanda mai kula da ɓangaren tattara bayanan sirri.

  2. MDD ta ce ambaliyar ruwa ta hana kai kayan agaji zuwa Sudan

    ...

    Asalin hoton, EPA

    Shirin Samar da Abinci na Duniya (WFP) ya ce sama da tireloli 50 ɗauke da tan 4,800 na kayan agajin da ya aika zuwa Sudan sun maƙale saboda ambaliyar ruwa a ƙasar.

    "Damina na ƙara ta'azzara matsalar da Sudan ke ciki domin ambaliyar ruwa ta raba mutane da dama da muhallansu, wanda hakan ya ƙara buƙatar ayyukan jinƙai.

    "Yanzu haka ana fama da wahala saboda ambaliya ta hana a kai wa mutanen ɗauki.

    Ruwan sama mai ƙarfi ya yanke gadoji, wanda hakan ya sa motocin kai agajin tsayawa domin ba za su iya wucewa ba saboda ambaliya da taɓo a hanyoyin," kamar yadda wata kafar yaɗa labaru a Sudan ta ruwaito.

    Sama da mutum 60 suka mutu, sannan dubban gidaje sun lalace a sanadiyar ambaliyar, wadda ta shafi jihohi 12 cikin 18 na ƙasar Sudan. Haka nan ambaliyar ta yi sanadiyyar jawo ɓarkewar annoba kamar kwalara da zazzaɓin typhoid da sauransu.

    Ambaliyar ta sa ana shan wahala wajen zuwa wuraren da yaƙin ya fi ta'azzara kamar Babban Birnin Ƙasar, Khartoum da Jihar Gezira, da kuma yankunan Kordofan da Dafur.

    Sama da mutum miliyan 25 - rabin mutanen ƙasar - na fuskantar matsananciyar yunwa saboda Yaƙin Basasar da ta dabaibaye mafi yawa na yankunan ƙasar.

  3. Za a shafe kwana uku ana ruwa marka-marka a wasu jihohin Najeriya

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumar kula da yanayi ta Najeriya NiMet, ta yi gargaɗin samun ambaliya a wasu jihohin ƙasar sakamakon mamakon ruwan sama da za a samu kwanan nan.

    Hukumar ta ce jihohin da suka haɗa da Kano, da Katsina, da Zamfara, da Jigawa da Kebbi da Kaduna, da kuma jihar Adamawa na cikin barazanar fuskantar ambaliyar ruwa, don haka ne ta yi kira ga mahukuntar jihahin su ɗauki matakan kare al'ummominsu.

    Tuni dai dama ambaliyar ta fara ɓarna a wasu jihohin Najeriya inda aka samu asarar rayuka da ta dukiyoyi.

    Alhaji Bashir Idris Garga, darakta a hukumar bada agajin gaggawa ta Najeriyar NEMA ya ce wannan ruwan saman da za ayi na kwana uku ba ƙaƙautawa zai sanya magudanar ruwa da dama ba a cika damuwa da yashe su ba su cike wanda daga bisani ruwan zai malala har ya je yayi ɓarna.

    "Saboda haka ya kamata a ɗauki mataki ƙwarai da gaske ya zama cewa ambaliyar bai yi ɓarna fiye da yadda ake zato ba." daraktan ya ƙra da cewa.

    Daraktan ya ce akwai irin wasu matakai da ake ɗauka na gaggawa irin su samun buhani a cika da yashi sai ayi tandagarƙi a canzawa ruwan akala yadda ba zai shiga yayi ɓarna ba.

    Darakatan ya ƙara da cewa bayan haka, ya kamata a yashe magudanar ruwa sannan kuma a dage a sanar da ƴan uwa da abokan arziƙi cewa ga sanarwar da aka bayar kuma ya kamata a ɗau matakai.

  4. Barka da Hantsi!

    Muna yi maku barka da wannan lokaci.

    Da fatan za ku bibiye mu domin sanin halin da duniya ke ciki, musamman abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Jamhuriyar Nijar da Kamaru da ma wasu sassan duniya.

    Kuna kuma iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta domin karanta ƙarin labarai da kallon bidiyo.