Ƙungiyar ƙwadago na tattaunawa kan gayyatar da ƴansanda suka yi wa shugabanta
Manyan jagororin ƙungiyar ƙwadago ta Najeriya NLC da suka hada da shugabanta, Joe Ajaero, sun hallara a hedikwatar ƙungiyar ta NLC domin gudanar da wani taron gaggawa na shugabannin ƙungiyar.
Taron ya biyo bayan sammacin da rundunar ‘yan sandan Najeriya ta yi wa Ajaero na ya gurfana a gabanta domin amsa tambayoyi kan zarge-zargen da suka shafi samar da kuɗaɗe ga ayyukan ta’addanci, da cin amanar kasa, da kuma aikata laifuka ta shafukan intanet.
Umarnin ‘yan sanda dai ya buƙaci Ajaero ya gabatar da kansa da misalin karfe 10:00 na safiyar yau Talata domin amsa tambayoyi.
A jiya Litinin ne aka gayyaci Ajaero ta hanyar wata wasiƙa mai dauke da sa hannun ACP Adamu Muazu a madadin mataimakin kwamishinan ƴansanda mai kula da ɓangaren tattara bayanan sirri.