Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
'Shekara 30 ina kwana a ƙarƙashin gada a Legas'
- Marubuci, Mansur Abubakar
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Lagos
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 6
Bayan da ya shafe kusan rabin yawan shekarunsa na haihuwa yana rayuwa a karkashin gada a birnin Lagos, Liya'u Sa'adu na daukar kansa a matsayin tamkar wani uba ga mutane da dama marassa muhalli da ke rayuwa irin tasa ta daukar karkashin gada a matsayin muhallinsu.
Akwai mutum sama da 60 da a yanzu suke irin wannan rayuwa da suka mayar da karkashin gada a unguwar Obalende, gidansu, duk da irin hayaniya da kara ta hada-hadar jama'a da ababen hawa da ake fama da su a wajen - kasancewar haya ta yi tsada sosai a wajensu.
Mallam Liya’u yana shawartar sababbin zuwa birnin na Ikko, wadanda galibi matasa ne 'yan ci-rani daga garuruwa da birane na sassan kasar daban-daban har ma da wajen kasar a kan yadda za a su iya rayuwa a birnin - domin birni ne da mutum zai iya fadawa hannun abokai bata-gari da za su iya shigar da shi rayuwa da aikata miyagun laifuka da shan miyagun kwayoyi.
A hirarsa da BBC ya bayyana cewa, “Shekarata 60, akwai matasa da suka zo nan 'yan watannin baya ko shekarun baya. Ina ganin wani nauyi ne da ya rataya a wuyana na ba su shawara.”
Bahaushe ne kamar yawancin 'yan'uwansa da ke rayuwa a karkashin gadar, wadanda ko da dai ba Hausawa ba ne asalinsu, da suna magana da Hausa.
“Abu ne mai saukin gaske mutum ya kauce hanya a nan musamman ma matasa, kasancewar ba sa tare da iyaye ko wani babba da zai kwabe su,” in ji shi.
Liya’u, ya shaida wa BBC cewa ya je Lagos ne a shekarar 1994, daga garinsu da ke, yankin karamar hukumar Zurmi a jihar Zamfarar, Najeriya.
A tsawon wadannan shekaru ya ce yawancin abokanansa na da ko dai sun rasu ko kuma sun koma garuruwa ko kauyukansu daga jihar ta Lagos.
Tukur Garba, wani wanda shekararsa biyar ke nan yanzu da ya fara wannan rayuwa a karkashin gada ya ce shawarar Liya'u na da amfani sosai - kuma duk wani da ya zo wajen yana girmama shi.
Shi kuwa Tukur, mai shekara 31 ya je birnin na Lagos ne daga jihar Katsina, da ke arewacin kasar.
Ya gaya wa BBC cewa, Liya'u tamkar yaya ne a wajensu saboda ya dade a wajen.
''Muna bukatar shawararsa saboda Lagos shu'umin waje ne wanda idan ba ka yi a sannu ba nan da nan za ka fada cikin wahala,'' in ji shi.
Sa'adu ya sheda wa BBC cewa, shi dai wannan wuri sunansa a yanzu, "Karkashin Gada" kawai, kuma lokacin da ya zo wurin mutanen da ke zaune ba su kai ma 10 ba.
Kuma ya ce mutanen da ke zuwa wurin ko dai daman sun san wani da ke zaune a wurin ko kuma wani ya ba su labari.
Wani mutum da ke zaune a wani gida a kusa da Karkashin Gada, tsawon sama da shekara 30, Adamu Sahara, ya ce masu kwana a titi a Lagos a kullum karuwa suke yi.
Ya ce matsalar tsaro da ta hada da rikicin 'yan Boko Haram da fatara da talauci na daga cikin abubuwan da ke sa mutane da yawa na barin arewacin kasar.
“Ya kamata shugabannin Najeriya su san abin da yake faruwa don su shawo kan matsalar bai kamata a ce wani dan'Adam na kwana a karkashin gada ba,” in ji shi.
To a yanzu dai mutumin da za a iya cewa ya zma kamar mai'unguwar Karkashin Gada, wato Liya'u ya ce ba shi da wani shiri ko lokaci n akowa jiharsa, Zamfara, saboda babu wasu harkoki na kasuwanci da zai yi.
Bugu da kari ga kuma uwa uba matsalar satar mutane da 'yan fashin daji ke yi kullum.
Liya'u dai yana nan yanzu da kayan kwanciyarsa - katifa da gidan sauro har da akwakwunsa na ajiyar kaya da dai sauran tarkace na dakin kwanba a wannan waje, Karkashin Gada, da ke unguwar Obalende a Lagos - mutu ka raba - takalmin kaza.
Shi dai Liya'u a iya cewa ta sa da kyau, domin wasu abokan zamansa a wannan waje, tabarma kawai garesu ita ma sai dare ya yi a baje ta su kwanta da abokansu a wannan waje, kafin safiya ta yi a shiga nema.
Ba a dai cika samun sace-sace sosai a wajen ba, saboda yawanci mutanen da ke rayuwa a wajen ko dai daman a nan suke sana'a ko kuma a nan suke hutawa.
Game da maganar bandaki kuwa a kusa da su akwai gidan wanka da bahaya wanda ake biyan naira 100.
Abinci kuwa daman ba matsala ba ne, domin mazauna wajen kasancewarsu yawanci 'yan arewacin Najeriya ne, ba sa rasa nau'ukan abincinsu na gargaji irin su tuwo da fura da nono.
Aisha Hadi, wata mai sayar da fura da nono a wurin ta yi wa BBC bayani, ''Nan daya ne daga cikin wuraren da a Lagos za ka ga 'yan arewa da yawa, saboda nake sayar da fura da nono a nan, kuma ina ciniki sosai.''
A tsawon shekaru talatin din da ya yi a Lagos, Liya'u, ya sauya sana'a daga mai gyara da wankin takalmi, inda a yanzu yake gwan-gwan na karafuna da yake sayarwa ana sake sarrafa su.
Ya ce a kullum yana samun akalla naira 5,000. To amma ba fa tana isarsa rayuwa ba ne a wannan lokaci.
''Kar ka manta fa a duk mako ina aika wa iyalina kudi a gida zihar Zamfara, ka ga gwagwarmaya ce ta kullum,'' in ji shi.
Ba a dai san hakikanin yawan mutnen da ke kwana a titunan Lagos ba, to amma wasu kungiyoyi wadanda ba na gwamnati ba sun ce, akwai kusan mutum rabin miliyan.
A 'yan watannin da suka gabata mutanen da ke zama a wannan wuri - Karkashin Gada sun gamu da matsin lamba da takurawa daga gwamnatin jihar Lagos.
Jami'an kan kai musu sumame a kai-a kai, da tsakar dare, bisa cewa zama a wajen ya saba wa doka, inda suke kama mutum.
Kuma duk wanda aka kama karshenta sai ya biya tarar naira 20,000, kusan abin da yawancin masu rayuwa a waje n ke samu a tsawon mako daya.
“Suna zuwa mana wajen karfe daya na dare ko biyu su kama mutane da ke bacci. Ina suke son mu je?” In ji Garba, wanda ya kara da cewa, ''zuwa safiya kowa ya dawo.''
Ya roki gwamnati da ta tausaya, ta duba yuwuwar samar wa da talakawa gidaje masu sauki da za su rayu.
To sai dai a najeriya gwamnati ba ta bayar da muhalli ga mutanen da ke kwana a titi. Kuma ma babu wani tsari na yin hakan sam-sam.
Sai dai abin da gwamnatin jihar Lagos ke son yi yanzu shi ne taimaka wa kananan ma'aikata su mallaki gidaje.
To amma ga talakawa irin su Liya'u, duk wani gida mai sauki da za a samar a Lagos ya fi karfinsu - domin haya a unguwannin da ke zama kamar na kama-wuri-zauna ma ta kai naira 100, 000 a shekara, yayin da ake biyar wajen naira 350,00 a shekara a unguwannin ma'aikata.
A irin wannan yanayi da haya ke tsada a birnin na Lagos da kuma yadda masu gida ke cin karensu babu babbaka, talakawa da sauran mutane irin su Liya'u ba su da mafita fa ce su ci gaba da zama da rayuwarsu a Karkashin Gada, a unguwar ta Obalende.
''A irin yanayin yadda rayuwa take da abin da nake yi abu ne mawuyaci na iya samun waje mai kyau da zan zauna,'' yana fadin haka y shimfide a katifarsa, kawai ya ja mayafinsa ya dukunkune, a Karkashin Gada, yayin da a samansa ba abin da kake ji sai karar motoci da sauran ababan hawa.
Ya leko ta mayafin ya ce, ''ai wannan karar motocin na saba da ita, ba ta hana ni bacci musamman ma idan an yi aiki an gaji.''