Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 20/08/2024

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 20/08/2024

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Aisha Babangida, Haruna Kakangi, Isiyaku Muhammed, Umar Mikail da Ahmad Bawage

  1. Asuba ta gari

    Mun zo karshen rahotanni a wannan shafi na labarai kai-tsaye.

    Sai kuma gobe da safe idan Allah ya kai mu.

    Ahmad Bawage ke cewa mu kwana lafiya.

  2. An kama jami’ai takwas da hannu a taimaka wa mai laifi tserewa daga gidan yari a Kenya

    Shugaban rundunar ƴan sandan Kenya ya ce an kama jami’ai takwas da suka taimaka wa wani mutum da ake zargi da kisan mutane da dama ya tsere daga daga gidan yari.

    An ce Collins Jumaisi Khalusha da wasu ƴan Eritrea 12 da ake zargin sun shigo Kenya ba bisa ka'ida ba, sun tsere daga inda ake tsare da su a birnin Nairobi.

    An kama Mista Khalusha ne a watan da ya gabata bayan da aka tsinci gawawwaki a wani rumbun shara.

    Ƴansanda sun ce ya amsa laifin kashe mata 42 ciki har da matarsa.

    Sai dai daga baya lauyan Mista Khalusha ya ce an tilasta masa ne ya amsa waɗannan laifukan.

    Ƙungiyoyin kare hakkin dan'adam na son a gudanar da bincike mai zaman kansa domin tabbatar da cewa babu hannun ƴan sanda a kashe-kashen.

  3. 'Muna shirin samar da riga-kafin kyandar biri miliyan goma a Afrika'

    Babbar hukumar kula da lafiyar jama'a ta Afirka ta ce tana shirin samar da allurar riga-kafin cutar kyandar biri miliyan goma don amfani da su a ƙasashe da ke nahiyar.

    Shugaban cibiyar yaƙi da yaɗuwar cututtuka ta Afrika, Dr Jean Kaseya ya ce an kulla yarjejeniya da wani kamfanin ƙasar Denmark, Bavarian Nordic, don amfani da fasaharsa wurin sarrafa alluran a cikin gida.

    Ya ce wannan tsarin zai taimaka wurin sauko da farashin allurar da kuma tabbatar da ingancinta, kuma zai taimaka wurin guje wa matsalolin da nahiyar ta fuskanta lokacin ɓarkewar cutar Korona inda ta dogara kan abin da take samu daga ƙasashe masu arziki.

  4. Kebbi ta bai wa ma’aikatan lafiya na wucin gadi takardun kama aiki bayan shirin BBC, Daga Zubairu Ahmad

    Gwamntin jihar Kebbi ta bai wa ma’aikatan kiwon lafiya na wucin gadi su fiye da 200 takardun kama aiki na dindindin bayan wani korafi da suka yi a lokacin gabatar da shirin BBC Hausa da haɗin gwiwar Gidauniyar MacArthur na ‘A Faɗa A Cika’ wanda aka gudanar a Kebbi ranar 1 ga watan Janairun 2024.

    Wasu daga cikin ma’aikatan da suka yi korafin sun gode wa BBC kan wannan taimako.

    Haka ma gwamnatin ta bayyana cewa ta cika alkawarin sama wa manoman shinkafa da suka yi korafi fanfunan ban ruwa har kimanin 6,000.

    Gwamnan jihar Dakta Nasir Kauran Gwandu da ya ke amsa tambaya a lokacin shirin a Fada a Cikan da ya gudana a jihar Kebbi ranar 1 ga watan Janairun wannan shekara ta 2024, ya ce tattaunawar da aka yi ta haifar da alfanu.

    Malam Yahaya Muhammed da kuma Hauwa'u Umar na daga cikin ma'aikatan wucin gadin da suka yi korafin a lokacin gudanar da shirin na A Fada A Cika, kuma sun shaida wa BBC iri farin ciki da suka ji bayan tabbatar da su a matsayin cikakkun Ma'aikata.

    Kwamishinan yaɗa labaran jihar ta Kebbi, Alhaji Ahmad Yakubu, ya shaida wa BBC cewa gwamnatin ta cika galibin alkawuran da ta dauka a lokacin shirin.

    Shirin A Fada a Cika na BBC Hausa da hadin gwiwar gidauniyar MacArthur dai na mayar da hankali ne game da alkawuran da shugabanni suka daukarwa al'umma musamman a lokacin zabe da kuma yadda ake tafiyar da muhimman ayyukan raya karkara da sauran su.

    Ko a watanni baya ma gwamnatin jihar Jigawa ta samar da ruwan sha ga al'ummar kauyen Gwari bayan wani korafi da suka yi cewa suna shan wahala wajen daukan ruwa daga wuri mai nisa a lokacin shirin da BBC ta yi da gwamnan jihar Malam Umar Namadi.

  5. Chelsea ba ta sa Sterling cikin masu buga Conference League ba

    Chelsea ba ta sa sunan Raheem Sterling ba, cikin waɗanda za su buga mata karawar cike gurbin shiga Europa Conference League da za ta kara da Servette.

    Wasa na biyu kenan da aka ajiye mai shekara 29, bayan da bai buga wa Chelsea karawar da Manchester City ta yi nasara 2-0 a Premier League ranar Lahadi.

    Haka kuma Chelsea ba ta sa sunan Ben Chilwell da Wesley Fofana da kuma Tosin Adarabioyo ba, cikin waɗanda ta aike wa da hukumar ƙwallon kafa ta Turai, Uefa.

    Ranar Alhamis, Chelsea za ta buga wasan a Stamford Bridge, wadda take fatan samun gurbin shiga Europa Conference League ta bana.

    Ranar Lahadi wakilan Sterling suka fitar da sanarwar neman makomar ɗan wasan, bayan da ba a saka sunansa cikin waɗanda za su fuskanci City ba a Premier.

    Chelsea ta kashe £185m wajen sayen ƴan wasa 11 tun kan fara kakar bana, kenan koci, Enzo Maresca yana da manyan ƴan ƙwallo sama da 40 a kasa.

  6. 'Ba mu ga ragin da gwamnatin Jigawa ta yi kan kayan Kantin Sauki ba', Daga Zahraddeen Lawan

    Ma'aikata a Jigawa na ƙorafin cewa ba su ga ragin kashi 10 na kayan Kantin Sauƙi da gwamnatin jihar ta buɗe a baya-bayan nan ba.

    Gwamnatin Jigawa ta buɗe kantunan ne da nufin samar da kayan masarufi a farashi mai rangwame domin sauƙaƙa wa al'ummar jihar tsadar rayuwa da matsanancin hauhawar farashin da ake fama da su a Najeriya.

    Gwamnatin ta yi gargaɗin cewa duk wanda aka samu da sauya farashin kaya a "Kantin Sauƙi", zai fuskanci tsattsauran hukunci.

    A ƴan kwanakin nan ne dai aka buɗe kantin a Dutse, babban birnin jihar bayan da mataimakin shugaban Najeriya ya kaddamar da shi a watan jiya.

    Sai dai tuni wasu ma’aikata suka fara korafin cewa babu ragin da gwamna Malam Umar Namadi yayi alkawari.

    Tun da farko an tsara fara sayarwa da ma’aikata kayan masarufi kafin daga bisani a shiga sayarwa sauran al’umma, sai dai wannan ma’aikacin da ya je sayen shinkafa ya ce ya kamata gwamna ya shiga lamarin.

    "Lokacin da aka bude kantin dukkanmu muna murna saboda abin alkhairi ne gwamna ya kawo. Bai kamata a ce an samu canjin farashi daga buɗe kantin ba, abin da ya ba mu mamaki shi ne a baya buhun shinkafa mai nauyin kilogram 25 ana sayar da shi kan 27,000 sai ga shi yau mun ga ana bai wa ma’aikaci kan 35,000, sun kuma ce sau ɗaya za a yanke wa mutum albashi," in ji ma’aikacin.

    Ya ce tilas ya fasa sayan shinkafa da taliya da ya yi niyya saboda ta yi tsada.

    Kwamishinan ma’aikatar ayyuka na musamman da ke lura da shirin, Alhaji Auwalu Danladi Sankara ya ce gwamnan jihar ya samu irin waɗannan korafe-korafe kuma an tattauna maganar a taron majalisar zartawa na jihar inda ya nuna ɓacin ransa tare da gargaɗin cewa kada wanda ya sauya farashin da aka amince da shi.

    Bayanai na cewa gwamnati ta fara sayar da kayan masarufin a Kantin Sauki na birnin Dutse da nufin cewa idan aka tabbatar babu wata matsala sai a buɗe na sauran ƙananan hukumomi, in kuma aka samu matsala sai a gyara sannan a ci gaba.

  7. Ghana na shirin gina babbar matatar mai a ƙasar

    Shugaba Nana Akuffo Addo na Ghana ya kaddamar da shirnin gina babbar matatar mai a ƙasar.

    Gwamnatin Ghana na fatan matatar za ta mayar da ƙasar babbar cibiyar samar da man fetur a yammacin Afirka.

    Matatar man za ta rika samar da ganga dubu 300,000 na mai a kowace rana, sannan ta samar da albarkatun mai.

    Aikin dai zai lakume dala biliyan 12 kuma ana sa ran kammala shi nan da shekara ta 2036.

    Sai dai masu suka sun bayyana shakku kan ingancin aikin, sun kuma nuna damuwa game da kiyaye lafiyar al’umma da muhalli.

  8. Najeriya za ta karɓi rigakafin kyandar biri a mako mai zuwa

    Ma'aikatar lafiya a Najeriya ta tabbatar da cewa tana shirin karɓar kashin farko na riga-kafin cutar kyandar biri ranar 27 ga watan Agustan 2024.

    Darektan kula da cutuka masu yaɗuwa da kuma allurar riga-kafi a ma'aikatar, Dakta Garba Ahmed Rufia, ya ce allurar riga-kafin guda 10,000 wanda gwamnatin Amurka ta bayar ta hannun hukumarta ta raya ƙasashe wato USAID, za a yi amfani da su wajen yin riga-kafi a jihohi.

    Ya ƙara da cewa Najeriya na aiki domin samun ƙarin allurai da za a rarraba.

    "Wannan ba shi ne riga-kafi na karshe da zai zo Najeriya ba. Muna tsare-tsare wajen tabbatar da cewa ƙarin allurai sun zo, ganin cewa akwai masu buƙata da yawa," in ji Dakta Rufia.

    Yandu dai ana horar da jami'an lafiya domin gane alamomin cutar kyandar biri da kuma ganin an yi riga-kafi a kan lokaci.

    Dakta Rufia ya ce kare jami'an lafiya da kuma al'umma ya zama wajibi, musamman ta hanyar ci gaba da faɗakar da mutane a faɗin ƙasar na yadda za su kare kansu da kuma ɗaukar matakan kariya domin rage yaɗuwar cutar.

    Najeriya dai ta ƙara kaimi wajen sa ido a tashoshin jiragen ruwa da kuma kan iyakoki domin gano sabbin masu ɗauke da cutar da kuma ɗaukar mataki.

  9. Barca ta saka ƴan wasa uku masu shekara 17 a tare a La Liga

    Barcelona ta fara kakar 2023/24 da kafar dama, bayan da ta je ta doke Valencia 2-1 ranar Asabar a wasan makon farko a La Liga.

    To sai dai ƙungiyar ta yi amfani da matasa uku masu shekara 17 a karawar da ta je ta ci Valencia.

    Cikinsu sun haɗa da Lamine Yamal da Cubarsí da kuma Marc Bernal, waɗanda aka fara fafatawar da su.

    Karo na biyu da Barcelona ta yi amfani da ƴan ƙwallo uku a lokaci ɗaya masu kasa da shekara 18.

    Haka kuma Barcelona ce keda wannan tarihin a karni na 21 ta kuma kara maimaita hakan a bana.

    Ta fara yin hakan a Mayun 2024 lokacin da Xavi ke koci, wanda ya fara da Lamine Yamal da Cubarsí da kuma Hector Fort a karawa da Almeria.

    Hansi Flick shi ne ke horar da Barcelona, bayan da ƙungiyar ta raba gari da Xavi a bara.

    Barcelona na fama da matsin tattalin arzikin da take tsuke bakin aljihu, sannan tana kokarin bin dokar La Liga ta kashe kuɗi daidai samu.

    A kakar da ta wuce Barcelona ta kare a mataki na biyu a teburin La Liga, inda Real Madrid ta lashe kofin tare da na Champions League.

    Ranar Asabar Barcelona za ta karɓi bakuncin Athletic Bilbao a wasan mako na biyu a La Liga.

  10. Isra'ila ta kashe mutum 12 a hari da ta kai wata makaranta a Gaza

    Hukumomin tsaro da ke ƙarƙashin ikon Hamas a Gaza sun ce an kashe Falasɗinawa aƙall 12 sakamakon wani hari da Isra'ila ta kai ta sama a wata makaranta.

    An ce harin ya shafi hawa na biyu ne a wani gini da ke birnin Gaza, wanda ke ɗauke da mutane da dama da suka rasa matsugunansu.

    Rundunar sojin Isra'ila ta ce an kai harin ne kan wata cibiyar bayar da umarni na Hamas da ke cikin makarantar.

    Rundunar ta bayyana hakan a matsayin hujja kan ikirarin da ta ke yi na cewa Hamas na amfani da fararen hula a matsayin garkuwa wajen kai hare-hare kan sojojin Isra'ila - zargin da kungiyar ta Hamas ta dade ta na musantawa.

  11. An hana jami'an gwamnatin Gabon tafiya hutu ƙasashen waje

    Shugaban Riƙon Ƙwarya na Gabon, Brice Oligui Nguema ya dakatar da jami'an gwamnatinsa na riqon ƙwarya tafiya hutu a ƙasashen waje, a wani yunƙuri da ya dace da tsarin shugabacinsa.

    An bayar da sanarwar ce a wata wasiƙa da aka karanta a talabijin ɗin ƙasar, inda jagororin juyin mulkin suka sanar da cewa hutun mako ɗaya ne kawai jami'in gwamnati yake da shi a shekara.

    "Dole a cikin kasar nan kowa zai yi hutunsa, sannan duk wanda zai yi hutu, asalin garinsa zai koma domin su riƙa shiga cikin harkokin mutanensu na yau da kullum," kamar yadda sanarwar ta nuna.

    Wannan na zuwa ne bayan Janar Nguema ya zagaya cikin ƙasar, inda ya tattauna da mutanen ƙasar, sannan ya saurari matsalolinsu.

    "Wannan matakin zai taimaka wajen ƙarfafa gwiwar komawa gida, sannan zai ƙara kawo kusanci da mutane," inji kakakin gwamnatin sojin, sannan ya ƙara da cewa za a iya samun akasin hakan ne kawai domin rashin lafiya ko kuma wani lamarin da zai iya zuwa ba zato ba tsammani.

    Tun bayan da Janar Oligui ya yi juyin mulki daga tsohon Shugaban Ƙasar Ali Bongo a bara, ya dage wajen nuna wa mutanen ƙasar cewa gwamnatinsa ta mutane ce. Wannan matakin ne hana jami'an gwamnati tafiya hutu a ƙasashen waje na zuwa makonni ƙaɗan bayan shekara ɗaya da juyin mulkin da aka hamɓarar da Ali Bongo.

    Haka kuma wadannan matakan suna zuwa ne a daidai lokacin da ake raɗe-raɗin cewa Janar Nguema yana kamun ƙafa ne domin tsayawa takarar Shugaban Ƙasa, wanda ake sa ran za a yi a Agustan baɗi.

    Sai dai har yanzu bai fito fili ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar ba.

  12. Shugaban ƙwadago bai amsa gayyatar ƴansanda ba a ranar Talata

    Shugaban kungiyar kwadago ta Najeriya NLC, Joe Ajaero, ya bayyana cewa zai mutunta gayyatar da rundunar ‘yan sandan Najeriya ta yi masa a ranar Laraba 29 ga watan Agustan 2024, maimakon yau Talata 20 ga watan Agustan 2024 kamar yadda aka buƙata tun farko.

    A cikin wata wasiƙa da shugaban ƙwadagon ya aika wa ƴansanda ta hannun lauyoyinsa, Ajaero ya bayyana cewa, wasikar gayyatar ta same shi ne a jiya Litinin, kuma shugaban yana da wasu ayyukan da ya tsara gudanarwa a yau Talata.

    Sai dai sanarwar ta ce Ajaero a shirye yake ya amsa gayyatar Laraba mai zuwa, ranar 28 ga watan Agusta.

    Bugu da kari, Ajaero ya buƙaci ƴansanda da su bayar da cikakkun bayanai game da zargin da ake yi masa, waɗanda suka haɗa da samar da kuɗaɗen tallafa wa ayyukan ta'addanci da haɗa baki wajen aikata laifuffuka da cin amanar ƙasa, da kuma aikata laifuka ta shafukan intanet.

    Wasiƙar ta ambato sashe na 36 na kundin tsarin mulkin Najeriya, wanda ya bai wa wanda ake tuhuma ƴancin samun cikakken bayani game da yanayi da takamaiman zarge-zargen da ake yi masa.

  13. Amurka za ta bai wa Najeriya tallafin jin-ƙai dala Miliyan 27

    Ofishin Jakadancin Amurka a Najeriya ya sanar da cewa Najeriya za ta samu dala miliyan 27 a wani ɓangare na tallafin dalar Amurka miliyan 536 da gwamnatin Amurka za ta bai wa ƙasashen Afirka a kudu da hamadar Sahara.

    "Wannan tallafin wani ɓangare ne na ƙudurin Amurka na isar da muhimmin taimakon tallafa wa rayuwar al'umma masu rauni a faɗin nahiyar Afirka," a cewar sanarwar.

    Jakadan Amurka a Najeriya, Richard Mills, ya bayyana muhimmancin sabon tallafin inda ya ce “Wannan taimakon zai kawo sauyi sosai a rayuwar waɗanda suka fi buƙata a Najeriya da ma nahiyar Afirka baki daya.”

    Mataimakin sakataren harkokin wajen Amurka kan tsaron fararen hula da Dimokuradiyya da kare haƙƙokin ɗan'adam, Uzra Zeya ne ya ƙaddamar da shirin tallafin a hukumance inda hakan ya kawo jimillar taimakon jin-kai da Amurka ke bayarwa ga yankin kudu da hamadar Sahara a shekarar kasafin kudi ta 2024 zuwa kusan dala biliyan 3.7.

    An yi shirin bayar da tallafin ne don magance buƙatu na gaggawa tsakanin mutane masu rauni a fadin yankin, da suka hada da ƴan gudun hijirar da suka tsere daga yaki da ta’addanci da masu neman mafaka, da ƴan gudun hijira a cikin gida da marasa galihu, da sauran wadanda rikici ya shafa.

  14. Za mu tsayar da Najeriya cak idan aka kama shugabanmu - NLC

    Ƙungiyar Ƙwadago ta Najeriya NLC, ta yi gargaɗi tare da yin barazanar fara yajin aikin sai baba-ta-gani, idan har aka kama shugabanta, Joe Ajaero.

    Ƙungiyar ta yanke wannan shawarar ne a wani taron gaggawa da jagororinta suka gudanar a yau, Talata.

    Taron ya gudana ne bayan gayyatar da rundunar ƴansandan Najeriya ta yi wa shugaban ƙungiyar, Joe Ajaero, wanda ta ce hakan na da alaƙa ne da bincikensa da ake yi kan zargin samar da kuɗade domin tallafa wa ayyukan ta'addanci, da aikata laifuffuka ta shafukan intanet, da zamba, da haɗa baki wajen aikata laifuka da kuma cin amanar ƙasa.

    Sai dai a nata ɓangaren, NLC ta bayyana zarge-zargen a matsayin marasa tushe kuma ta yi zargin cewa lamarin na da alaƙa da siyasa.

    Ƙungiyar ƙwadagon ta zargi mahukuntan Najeriya da yunƙurin tursasawa da kuma musguna wa shugabanninta.

    Ta kuma ce ana ƙoƙari ne wajen ganin an raunana ta bisa 'fafutikar da take ta kare manufofin dimokuradiyya da haƙƙokin ma’aikatan Najeriya'.

    Saboda haka ne jagororin ƙungiyar suka umarci dukkanin ɓangarorin ƙungiyar su fara haɗa kan mambobinsu a faɗin ƙasar da gargaɗin cewa ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen ɗaukar dukkan matakan da suka dace, waɗanda suka haɗa da zanga-zanga da kuma dakatar da komai a ƙasar don kare mutunci da ƴancin kai na ƙungiyar.

    "Idan har wani abu ya faru da shugabanmu, ko kuma aka kama shi, to za mu fara yajin aikin sai baba ta gani a faɗin ƙasar daga tsakar dare." in ji NLC.

    NLC na ɗaya daga cikin ƙungiyoyin ƙwadago mafiya ƙarfin faɗa a ji a Najeriya, wadda a lokuta da dama ta jagoranci ma'aikata domin nuna rashin amincewa da wasu manufofin gwamnati.

    Ko a wannan shekara ta 2024, ƙungiyar ta shiga yajin aiki tare da gudanar da zanga-zanga bayan zargin gwamnati da rashin mayar da hankali a batun ƙarin albashin ma'aikata.

    Hakan ya tursasa wa gwamnatin ƙasar sake kiran ƙungiyar zuwa teburin shawarwari, inda daga ƙarshe aka cimma matsayar nunka albashin ma'aikata daga naira 30,000 zuwa naira 70,000.

    Sai dai daga baya an ga alamu na rashin jituwa tsakanin ɓangarorin biyu bayan da ƙungiyar ta NLC ta ce ba za ta janye daga zanga-zangar matsin rayuwa da aka gudanar a ƙasar ba kasancewar ba ita ce ta shirya ta ba.

    Jim kaɗan bayan hakan ne wasu jami'an tsaro suka kai samame a babban ofishin ƙungiyar da ke Abuja, sai dai bayan koken da ƙungiyar ta yi, rundunar ƴansandan Najeriya ta ce ta kai samamen ne domin gano wasu muhimman takardu waɗanda za su zamo shaida a binciken da ake yi kan wani mutum, wanda 'ke da hatsari' ga ƙasar.

  15. Matakan da za ku ɗauka idan mutum ya ci abinci mai guba

    A baya-bayan nan labarin mace-macen mutane sanadiyyar cin abinci mai guba ya tayar da hankalin al'umma, musamman a jihohin arewacin Najeriya.

    Cikin wata ɗaya an samu rahoton mutuwar kimanin mutum 24 a jihohin Sokoto da Zamfara, inda lamarin ya shafi iyalai guda uku.

    Hakan na zuwa ne yayin da rahotanni ke cewa mutane na komawa cin ganyayayyaki da ba su saba amfani da su ba sanadiyyar matsin tattalin arziƙi.

    Mace-macen sun fara tayar da hankali ne bayan wasu iyalai su shida sun rasa rayukansu a jihar Sokoto bayan cin abinci da aka haɗa da rogo.

    Ci gaban labarin - https://bbc.com.im/hausa/articles/clywl5e0655o%3C/a%3E%3C/p%3E%3C/div%3E%3C/div%3E%3C/article%3E%3C/li%3E%3Cli class="css-xxlek1">

    Amnesty ta ja kunnen gwamnatin Najeriya kan 'tsangwamar' ƙungiyar ƙwadago

  16. Mutumin da ake zargi da kashe mata 42 ya tsere daga gidan yari a Kenya

  17. DR Congo ta sanar da karɓar rukunin rigakafin cutar Mpox na farko

  18. Biden ya yi jawabi mai sosa zuciya bayan miƙa takara ga Kamala Harris

  19. An gano gawar ƴan Isra'ila 6 da ake garkuwa da su a Gaza