Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 21/11/2024

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 21/11/2024

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Haruna Kakangi, Abdullahi Bello da Isiyaku Muhammed

  1. ACF ta dakatar da shugabanta kan zaɓen ɗan takara a 2027

    Ƙungiyar tuntuɓa ta dattawan arewa wato Arewa Consultative Forum ta ce ta dakatar da shugaban majalisar ƙolinta, Mamman Mike Osuman dangane da wasu kalamai da aka alaƙanta da shugaban a wani taronta da ta yi ranar Laraba a Kaduna.

    A wata sanarwa mai sa hannun Alhaji Bashir Muhammad da Alhaji Murtala Aliyu, ƙungiyar tuntuɓa ta musanta wasu bayanai da ke yawo cewa sun bayyana goyon bayan fito da ɗantakarar shugaban ƙasar Najeriya daga yankin arewa a 2027.

    Ƙungiyar ta kuma ce yankin na arewa na fama da ƙangin talauci da matsalar tsaro da jahilci, inda ta bayyana cewa gundarin matsalar yankin na hannun ‘yan arewa.

    Ƙungiyar ta bayyana cewa an jirkita bayanan ta wata fuskar da ba ita ce alƙiblar da ta ɗauka ba, haka ma ta nuna damuwa game da yadda yankin na arewa ya samu kansa a komabaya, a fannonin da suka shafi ilmi da tattalin arzki da kuma talauci, sai kuma uwa-uba matsalar tsaro.

    Wannan na kumshe ne a cikin wata takardar bayan taro da kakakinta Farfesa Tukur Baba ya sakawa hannu a ranar Laraba, da kuma aka raba wa manema labarai.

    Wadannan kalaman na zuwa ne bayan da aka samu wasu bayanai da wasu jaridun Najeriya suka wallafa da ke cin karo da juna da aka danganta da shugaban kungiyar tuntuba ta dattawan arewacin Najeriyar, Mamman Mike Osuman, da aka ce ya fadi cewa lokaci ya yi da yankin ya dace ya fito da shugaban da zai jagoranci Najeriya a shekarar 2027, da kuma ya san zafin al'ummarsa.

  2. Gwamnatin Kano ta miƙa ƴan zanga-zanga ga iyalansu

    Gwamnatin jihar Kano ta miƙa mutanen nan guda 76 ciki har da ƙananan yara fiye da 20 da shugaba Tinubu ya yi wa afuwa bayan kotu ta same su da laifin yi wa ƙasa cin amana bisa ɗaga tutar Rasha da suka yi a lokacin zanga-zangar matsin rayuwa ta watan Agustan 2024.

    Gwamnatin ta Kano dai ta hannanta mutanen ga iyalansu bayan karɓar su daga hannu mataimakain shugaban ƙasar Najeriya, Kashim Shettima ranar 5 ga watan Nuwamba.

    Gwamnatin jihar Kanon dai ta yi alkawarin ɗaukar nauyin karatun mutanen 76 tare da ba su jari, domin samar musu da madogara.

  3. Ƴanbindiga sun sace mutum 30 a Katsina

    A jihar Katsinar Najeriya, wasu ƴanbindiga sun sace akalla mutum 30 da suka hada da maza da mata tare da dabbobi masu yawa.

    Wannan lamari ya faru ne a garin Unguwar Daudu da ke cikin karamar hukumar Funtuwa da tsakar daren ranar Alhamis.

    Mutane a yankin na cikin zulumi ganin cewa ba su iya zuwa gonaki ɗauko abubuwan da suka noma sanadiyar hare-hare da yin gurkuwa da jama’a da ‘yan bindigar ke yi domin neman kuɗin fansa.

    Bayan abun da ya faru a garin na Unguwar Daudu, a garin Mai ruwa da ke maƙwabtaka da ƙauyen ƴan bindigar sun yi awon gaba da wasu mutane da su ka je daukar albarkatun gona a daji.

  4. Na yi farin cikin kama Simon Ekpa - CG Musa

    Babban hafsan hafsoshin Najeriya, Janar Christopher Gwabin Musa ya ce ya yi fari ciki da kamen da hukumomin Finland suka yi wa shugaban haramtacciyar ƙungiyar ƴan aware ta IPOB ta Najeriya, Simon Ekpa.

    Cikin wani saƙo da kakakin ma'aikata tsaron ƙasar, Manjo Janar Tukur Gusau ya aike wa BBC ya ce babban hafsan tsaron ƙasar ya ce yana fatan kamen ya zama wani mataki na tisa ƙeyar Mista ekpa zuwa Najeriya don ya fuskanci shari'a.

    A ranar Alhamsi ne hukumomin Finland suka kama Simon Ekpa tare da aika shi gidan yarin ƙasar, byan gurfanar da shi a kotu, kan zargin tunzura mutane su aikata ayyukan ta'addanci.

    Kotun ta ce ta samu Simon Ekpa ne da laifin yaɗa aƙidu na ƴan aware a kafar sada zumunta, a ranar 23 ga watan Agustan 2021 a birnin Lahti na ƙasar ta Finland.

  5. Majalisar wakilan Najeriya ta yi fatali da ƙudirin wa'adi mulki ɗaya na shekara shida ga shugaban ƙasa da gwamnoni

    Ƙudurin ɓukatar yi wa kundin tsarin mulkin Najeriya kwaskwarima don mayar da wa'adin mulkin ƙasar zuwa wa'adi ɗaya na shekara shida ga shugaban ƙasa da gwamnoni ya gamu da cikas a majalisar wakilan ƙasar.

    Ƙudirin wanda Ikenga Ugochinyere ya gabatar ya buƙaci a zagaya da matsayin shugabancin ƙasar zuwa yankuna ƙasar shida.

    Haka kuma ƙudurin ya buƙaci a riƙa gudanar da duka zaɓukan ƙasar a rana guda.

    A lokacin da aka gabatar da kuɗirin domin karatu na biyu a zauren majalisar, sai mafi yawan 'yan majalaisar suka yi fatali da shi.

    A shekarar 2019, wani ɗan majalisar daga jihar Benue ya gabatar da makamancin wannan ƙuduri, wanda shi ma ya gamu da cikas a majalisar.

  6. 'Mutum 26 sun jikkata a harin da Rasha ta kai mahaifar Zelensky'

    Hukumomi a Ukraine sun ce wani hari da Rasha ta kai birnin Kryvyi Rih na ƙasar ya raunata mutane da dama.

    Gwamnan yankin Dnipropetrovsk, Serhy Lysak, ya ce mutum 26 ne suka jikkata a harin da aka kai da safiyar yau Alhamis.

    Ya ƙara da cewa daga ciki wasu mata biyu sun samu munanan raunuka.

    Birnin Kryvyi Rih - da ke tsakiyar Ukraine - shi ne mahaifar shugaban ƙasar, Volodymyr Zelensky.

  7. An harbe mutum 38 a Pakistan - 'Yansanda

    'Yansanda a yankin arewa maso yammacin Pakistan sun ce aƙalla mutum 38 aka harbe a wani hari da aka kai wa motocin fasinja a lardin Kai-ba- Pak- tun-kwa.

    Mazauna yankin sun shaida wa BBC mutanen na tafiya ne cikin ayarin motoci biyu daga Peshawar zuwa Para-chinar tare da rakiyar 'yansanda a lokacin da aka kai musu hari a garin Kurram.

    Sakataren gwamnatin yankin ya faɗa wa kamfanin dilancin labarai na Reuters cewa wata mata da wani yaro na cikin waɗanda aka kashe.

    Harbe-harben su ne tashin hankalin na baya-bayan nan da aka samu a rikicin da ake yi tsakanin yan Shi'a da yan Sunni da ya yi sanadin mutuwar mutane da dama a yankin.

  8. Majalisar dattawa ta amince Tinubu ya ciyo bashin naira triliyan 1.77

    Majalisar dattawa ta Najeriya ta amince da buƙatar shugaban ƙasa Bola Tinubu na ciyo bashin $2.2, wanda ya kai kimanin naira triliyan 1.77.

    Majalisar ta amince da buƙatar ne bayan kwamitin ciyo bashi daga ciki da wajen ƙasar, ƙarƙashin jagorancin Sanata Aliyu Wamakko wai wakiltar Sokoto ta arewa ya gabatar da rahotonsa.

    Daily Trust ta ruwaito cewa idan aka karɓo wannan sabon bashin, bashin ake bin Najeriya zai kama naira triliyan 136 ke nan.

    Tinubu ya aika wa majalisar buƙatar ciyo bashin ne, wanda ya ce zai yi amfani da shi domin cike giɓin kasafin kuɗin bana na.

  9. Biden ya ba Ukraine tallafin soji na dala miliyan 300

    Gwamnatin Joe Biden ta sanar da tallafin dala miliyan 300 na tallafin soji ga Ukraine a ƙoƙarin agaza mata a ƴan makonnin da ya rage mata a gwamnati.

    Wakilin BBC ya ce ƙunshin tallafin ya haɗa da harsasai, makamai masu linzami, da jirage marasa matuƙa da na'urorin kakkaɓo makamai da kuma nakiyoyi.

    Wannan mataki dai ya janyo zazzafar suka daga masu rajin kare haƙƙin ɗan'adam kan haɗarin da hakan zai jefa fararen hula.

    A ɓangare guda kuma, shugaba Zelensky ya yi maraba da matakin tare da cewa hakan zai taimakawa sojojin ƙasar da ke yaƙi da mamayar Rasha.

  10. Ba mu ce ba za mu goyi bayan Tinubu ba - ACF

    Ƙungiyar tuntuɓa ta Arewa, ACF, ta ce rahotannin da ake yaɗawa cewa ta yanke shawarar wanda za ta goya wa baya a zaɓen 2027 ba haka ba ne.

    Wasu kafofin watsa labarai a Najeriya ne suka ruwaito cewa ƙungiyar bayan taronta, ta ce ba za ta mara wa shugaban ƙasa Bola Tinubu baya ba.

    BBC ta tuntubi Farfesa Tukur Baba, wanda mai magana da yawun ƙungiyar ne, wanda ya ce, "Gaskiya ƙungiyar tuntuba ba ta ce haka ba. Mun fitar da bayani da muka karanta a gaban ƴan jarida na bayan taro, inda muka ce ƙungiyar ta gamsu ta fito fili ta bayar da shawarwari da kuma yin bayani kan inda arewa ta nufa. Sai muka ce akwai abubuwa da ya kamata mu yi a game da halin da ƙasar take ciki, sai muka ga abin da ya shafi arewa shi ne rashin tsaro da taɓarɓarewar tattalin arziki wanda muka ga ya fi shafar ƴan arewa."

    Farfesa Baba ya ƙara da cewa, "Mun ga wasu matakai da wannan gwamnati ta ɗauka suna ƙara kawo koma-baya ga zamantakewa musamman ma na tattalin arzikin arewa."

    "Sannan mun buƙaci gwamnati ta gyara inda ta nufa a wajen gyara tattalin arziki. Mun ce ba shakka tattalin arziki na son gyara, amma a yi gyaran ta yadda mutane ba za su tagayyara ba domin kada magani ya zo ya fi ciwo zafi. Don haka muka kira gwamnatin tarayya ta sake duba abin da take yi, ta tabbatar da cewa mutane ba su tagayyara ba."

    Farfesa Baba ya ƙara da cewa an samu ci gaba a ɓangaren ilimi a yankin arewa, amma ana buƙatar ƙari.

    "Idan ka koma shekarar 2950, a arewa masu digiri ba su wuce biyu ba, haka aka zo lokacin da aka samu ƴanci, nan ma ba su wuce su 10 ba. Amma yau babu wata ƙaramar hukuma da ba za ka samu yaro da ya je jami’a ba."

    Sai dai ya ce akwai buƙatar gwamnati da dukkan masu ruwa da tsaki a yankin arewa su bayar da gudunmuwa domin ƙara inganta harkokin ilimin yankin.

    "Muna kira ga gwamntoci da duk wani ɗan arewa a duk inda yake ya taimaka wajen inganta ilimi. Ba gwamnati ba ce kaɗai za ta yi aikin. Kowa zai iya taka rawarsa, ko dai mutum ya ɗaukar nauyin karatun wani ko ka gyara makaranta ko faɗakar da iyaye a kan muhimmancin ilimi," in ji farfesa Tukur Baba.

  11. An kashe mutum ɗaya da jikkata wasu a rikici tsakanin sojoji da ƴansanda a Ebonyi

    Ƴansanda da sojoji sun yi rikici a jihar Ebonyi, wanda ya yi sanadiyar mutum ɗaya wanda ya zo wucewa.

    Rikicin wanda aka yi a ranar Laraba, ya faru ne a yankin Ugwuachara bayan an samu saɓani tsakanin ƴansanda da suke duba motoci a hanya da wani soja da yake kan babur, kamar yadda tashar Channels ta ruwaito.

    Wani ganau ya ce sojan ne ya ƙi amince a duba babur ɗinsa, shi kuma ɗansandan ya yi yunƙurin kama babur ɗin.

    A lokacin da rikicin ne aka harbi wani mutum daban ya rasu, sannan wasu mutum uku suka jikkata.

    Kwamishinar ƴansandan jihar Ebonyi, Anthonia Uche-Anya ta tabbatar da aukuwar lamarin a tattaunawarsa da tashar Channles ta wayar tarho.

    Ta ce da sojan da ɗansandan duk suna hannu, kuma ana cigaba da bincike.

  12. Ƙasashe masu tasowa sun buƙaci manyan ƙasashe su ɗauki nauyin yaƙi da sauyin yanayi

    Yayin da ake gab da cimma wa'adin tattaunawa a taron sauyin yanayi na COP29, mai masaukin baƙi Azerbaijan ta yi kira ga ƙasashen Burtaniya da Brazil su taimaka a samu matsaya mai inganci da ƙasashe za su amince da ita.

    Ƙasashe masu tasowa dai sun kafe cewa ƙasasahe masu ƙarfin arziki ne ya kamata su biya biliyoyin daloli a kowacce shekara domin taimaka musu wajen magance matsalolin sauyin yanayi.

    Sai dai wakilai da ke taron sun ƙi amincewa da hakan.

    An kuma tafka mahawa kan ko sun sanya dogon buri kan rage hayaƙi da ke ƙara ta'azzara ɗumamar ya nayi a duniya.

  13. An naɗa Janar Abdoulaye Maiga a matsayin sabon firaiministan Mali

    Shugaban mulkin soji na ƙasar Mali ya sanar da naɗa na hannun damar shi, Janar Abdoulaye Maiga a matsayin sabon firaiministan ƙasar, kwana ɗaya bayan ya cire Choguel Kokalla Maiga daga muƙamin.

    An cire tsohon firaimistan ne daga muƙamin bayan ya bayyana rashin jin daɗinsa kan yadda mulkin soji a ƙasar ya ɗauki dogon lokaci ba tare da an koma mulkin farar hula ba, da rashin bayyana yadda ake tafiyar da gwamnati da ware shi a harkokin gudanar da gwamnatin.

    An sanar da naɗa Janar Abdoulaye Maiga ne a wata sanarwar da sakatare janar na gwamnatin ƙasar ya bayyana a tashar talabijin ƙasar.

    Maiga, wanda bai daɗe da samun muƙamin janar ba, ya kasance kakakin gwamnatin, kuma ya taɓa riƙe muƙamin na wucin gadi a shekarar 2022, lokacin wanda aka cire yake rashin lafiya.

    Janar Maiga ba ya cikin sojojin da suka yi juyin mulki a shekarar 2020, amma daga bisani ya shiga cikinsu.

  14. Kotun hukunta manyan laifuka ta bayar da sammacin kama Netanyahu

    Alƙalan kotun hukunta manyan laifuka wato ICC sun bayar da sammacin kama firaministan Isra'ila da tsohon ministan tsaron ƙasar da wasu kwamandojin Hamas.

    Kotun ta yi watsi da yunƙurin Isra'ila na ƙalubalantar huruminta, inda bayan sauraron ƙara, ta bayar da sammacin kama Netanyahun da Yoav Gallant.

    Haka kuma an bayar da sammacin kama Mohammed Deif, duk da cewa sojojin Isra'ila sun ce sun kashe shi a wani hari a Gaza a watan Yuli.

    Alƙalan sun ce sun gamsu da hujjojin cewa mutanen uku sun "aikata laifukan yaƙi" da wasu laifukan cin zarafin mutane a yaƙin Isra'ila da Hamas. Sai dai Isra'ila da Hamas ɗin duk su musanta aikata laifukan yaƙi.

    Yanzu hankali ya koma kan ƙasashe mambobin kotun duniyar guda 124 domin yanke shawarar tabbatar da umarnin kotun ko su yi watsi da shi.

    A watan Mayu ne mai gabatar da ƙara na kotun hukunta manyan laifuka, Karim Khan ya buƙaci kotun ta bayar da sammacin kama Netanyahu da Gallant da Deif da wasu kwamandojin Hamas biyu, waɗanda an riga an kashe su wato Ismail Haniyeh da Yahya Sinwar. Duk da cewa Isra'ila ta ce ta kashe Deif, kotun ta ce ba ta tabbatar da hakan ba.

    Mai gabatar da ƙarar ya shigar da ƙarar ce saboda abin da ya biyo bayan harin Hamas na 7 ga Oktoban 2023, wanda ya yi sanadiyar kashe kusan mutum 1,200 a arewacin Gaza, sannan suka yi garkuwa da mutum 251.

    Isra'ila ta ƙaddamar da mayar da martani, inda ta kashe aƙalla mutum 44,000 a Gaza, kamar yadda ma'aikatar lafiya ta yankin wanda ke ƙarƙashin Hamas ta bayyana.

    An zargi jagororin Hamas da kisa da garkuwa da mutane da fyaɗe da azabtarwa.

    A gefe guda kuma an zargi Isra'ila da kai hare-hare kan fararen hula da gangan da amfani yunwa a matsayin makamin yaƙi da kashe-kashe

  15. Shugaban mulkin soji na Mali ya kori firaiministan ƙasar saboda ya 'soke shi'

    Shugaban mulkin sojin Mali, ya kori firaiministan ƙasar Choguel Kokalla Maiga, da ɗaukacin gwamnatinsa.

    Matakin na zuwa ne bayan sukar da Mr Maiga ya yi wa sojojin da suka yi juyin mulki kan gaza cika alƙawarin da suka ɗauka na maida mulki hannun farar hula.

    Wakilin BBC ya ce a ƙarshen mako ne Maiga ya yi ƙorafin gwamnatin soji ta maida shi saniyar ware ba a shaida masa komai kan lokacin da za a gudanar da zaɓe ba, fiye da wanda aka aminta da shi na shekara mai zuwa.

    Mali dai ta jima ta na fama da tada kayar bayan mayaka masu ikirarin jihadi, da tashin hankalin da ya biyo bayan jyin mulkin da sojoji suka yi a shekarar 2020 da 2021.

  16. Faransa ta wanke tsohon ɗantawayen Chadi daga zargin aikata laifukan yaƙi

    Kotu a ƙasar Faransa ta wanke tsohon ɗantawayen Chadi, wanda ƙasar ta Chadi ta tuhuma da aikata laifukan yaƙi ciki har da yin amfani da ƙananan yara a yaƙin, kamar yadda kafar labarai ta Tchadinfos mai zaman kanta ta ruwaito.

    An zargi janar Mahamar Nouri, wanda shi ne jagoran dakarun UFDD, da amfani da ƙananan yara a yaƙi da kuma aikata wasu laifukan a yaƙin da aka yi tsakanin Chadi da Sudan a shekarar 2005 da 2010.

    Kamar yadda rahotonni suka nuna, binciken wanda aka fara a shekarar 2017 wanda ofishin yaƙi da laifukan cin zarafi na France's Central Office for the Fight against Crimes against Humanity, Genocide and War Crimes (OCLCH), bai samu isasshen hujja domin tabbatar da zargin da aka yi wa tsohon ministan tsaron na Chadi ba.

    "Ina farin cikin jin wannan labarin, duk da cewa tun farko na san hakan hukuncin zai kasance. Ina godiya ga Allah bisa wannan nasarar da ƙwarin gwiwar da ya ba ni tare da iyalina na fuskantar wannan matsala," in ji Nouri.

    An kama Nouri ne a shekarar 2019, sannan aka sake shi a Maris na 2020.

  17. An kama jagoran IPOB da wasu mutum huɗu a Finland bisa zargin laifukan ta'addanci

    Jagoran haramtacciyar ƙungiyar IPOB ta kudu maso kudancin Najeriya, Simon Ekpa ya shiga hannu a ƙasar Finland bisa zarginsa da aikata laifukan ta'addanci.

    Kafofin watsa labarai na ƙasar Finladn sun ruwaito cewa wata kotu a yankin Päijät-Häme ta tura Ekpa gidan yari bisa zarginsa da ingiza mutane su aikata laifuka.

    Kotun ta ce Simon Ekpa tana yaɗa farfagandar a ware a kafofin sadarwa.

    Bayan Ekpa kuma, kotun ta ce a kamo mata wasu mutum hudu bisa zarginsu da laifukan ta'addancin.

    Ekpa, wanda ɗan Najeriya ne, wanda yake da izinin zama ɗan ƙasar Finland, an haife shi ne a shekarar 1985, kuma ya taɓa bayyana cewa yana jagorantar wata ƙungiya a Najeriya da take fafutikar kafa ƙasar Biyafara.

    Ƴansanda sun ce suna zargin Ekpa da yaɗa manufofinsa ne daga ƙasar ta Finland da zummar haifar da tarzoma, wadda ke cutar da fararen hula da sauran laifuka a yankin kudu maso kudancin Najeriya.

    A wani faifan bidiyo da ya a game da zaɓen 2023, ya ce ba za a yi zaɓe ba a yankin kudu maso kudu.

  18. Aƙalla kamfanoni 300 ne za su halarci baje-kolin kasuwar duniya ta Kano - KACCIMA

    Cibiyar bunƙasa ciniki da masana'antu da ma'adinai da ayyukan gona (KACCIMA) ta Jihar Kano ta ce aƙalla kamfanoni 300 daga cikin da wajen Najeriya za su halarci baje-kolin kasuwar duniya ta bana wanda shi ne karo na 45 a jihar Kano.

    Ana sa ran kasuwar za ta ci ne tsakanin 23 ga Nuwamba zuwa 7 ga Disamban 2024.

    Shugaban KACCIMA, Alhaji Garba Imam ya bayyana haka, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, inda ya ƙara da cewa ana sa ran kamfanoni daga ƙasashen India da Nijar da sauransu za su zo su baje-kolin kayayyakinsu.

    Imam ya ƙara da cewa cibiyar ta tanadi dukkan abubuwan da ake buƙata domin tabbatar da an ci kasuwar sumul, "sannan kuma mun mayar da shiga kasuwar kyauta domin ba mutane da dama damar zuwa."

    Shugaban na KACCIMA ya ce mataimakin shugaban ƙasa, Alhaji Kashim Shettima ne zai buɗe baje-kolin, sannan gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf zai zama babban mai masaukin baƙi, sannan ya ƙara da cewa akwai isasshen tsaro.

  19. Mutum 209 suka rasu, 99 suka jikkata a fashewar tankar man Jigawa — Kwamitin bincike

    Kwamitin binciken fashewar tankar mai na jihar Jigawa ya ce mutum 209 ne suka rasu, sannan mutum 99 suka jikkata, bayan kadarorin miliyoyin naira da aka rasa a ibtila'in wanda ya auku a ranar 14 ga Oktoba a garin Majiya da ke jihar ta Jigawa.

    Kwamitin, wanda Hafizu Inuwa ya jagoranta ne ya bayyana hakan a lokacin da yake miƙa rahoton bincikensa ga gwamna Umar Namadi a ranar Laraba kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

    Rahoton kwamitin ya kuma nuna cewa har yanzu akwai mutum 38 da suke jinya a asibiti a sanadiyar lamarin wanda ya shafi iyalai 167.

    Kwamitin ya kuma bayar da shawarar a riƙa kiyaye wajen sufurin man fetur, sannan ya buƙaci a samar da sashen kula da tashin hankali a asibitoci, sannan a kafa hukumar kula sufuri domin tabbatar da bin dokar tuƙi.

    A nasa ɓangaren, gwamnan jihar ya yaba wa mambobin kwamitin bisa aikin da suka yi, sannan ya ce a shirye suke su aiwatar da shawarwarin da kwamitin ya bayar.

  20. Ƙwace izinin zama ɗan ƙasa: Ƙungiyoyi a Nijar sun nuna damuwa kan matakin

    A Jamhuriyar Nijar, a karon farko tun bayan soke damar zama ɗan ƙasa ga wasu ƴan Nijar da hukumomin ƙasar suka yi, wasu ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan'adam na cikin gida sun fito fili sun nuna damuwa a kan matakin.

    Ƙawancen ƙungiyoyin MOJEDEC ya ce matakin zai sake raba kan al'ummar Nijar a daidai lokacin da aka fi buƙatar haɗin kan ƙasa.

    A tattaunawarsa da BBC, shugaban ƙawancen Abou Zaidi Sanusi Abdul Aziz ya nemi gwamnati ta janye wannan doka, da neman hanyoyin hukunta waɗanda aka zarga da aikata laifukan ta'addanci.