Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Talata 11/11/2025

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Talata 11/11/2025

Rahoto kai-tsaye

Isiyaku Muhammed da Annur Muhammad

  1. Shugaban Syria jajirtacce ne da zai iya ciyar da ƙasar gaba - Trump

    Amurka

    Asalin hoton, Getty Images

    Amurka ta ce Syria za ta shiga cikin kawancen da take jagoranta na yaki da mayakan IS, kuma za ta dawo da huldar diflomasiya da Washington.

    Wakilin BBC ya ce bayan ganawar, Donald Trump ya bayyana shugaban na Syria a matsayin jajirtaccen mutum.

    Shugaba Trump ya ce ya so Syria ta kasance wani babban bangare na shirinsa na samar da zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya Kasa da shekara guda ne.

    Ahmed Al Sharaa ya jagoranci mayaka suka kwace mulki a Damascus inda suka hambarar da gwamnatin Assad.

    A wata hira da kafar Fox, Mr Sharaa ya ce tsohon mukaminsa na kwamandan al-Qaeda wani lamari ne da ya wuce.

  2. Farawa

    Jama'a barkanmu da safiyar ranar Talata daga nan sashen Hausa na BBC, inda za mu kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya.

    Da fata za ku kasance tare da mu.