Faɗa ya sake ɓarkewa tsakanin sojojin Sudan da RSF a kudancin tsakiyar ƙasar

Asalin hoton, Getty Images
Rahotanni na cewa ana ƙazamin fada a yankin kudancin tsakiyar Sudan tsakanin rundunar sojin kasar da kuma kungiyar RSF.
Sojojin sun ce sun ƙwace garin Mabsouta da ke kudancin Kordofan, amma kuma dakarun rundunar da ke Arewacin Kordofan din na fama da harin jiragen sama marassa matuka.
Mazauna babban birnin - El-Obeid, sun ce sun ga hayaki na tashi daga wani sansanin soji da ke birnin.
Duk wani yunƙuri na dakatar da bude wuta ya ce tura inda bangarorin biyu ke kafewa kan wasu sharudda da ba za su yiwu ba.
Jihohin Kordofan din uku sun kasance fagen-daga a yakin basasar Sudan din na wata talatin , ind a yanzu kungiyar ta RSF ta kame Darfur. do a headline for this
