Real Madrid ta kara yin canji, Real Madrid 2-1 Barcelona
Rodrygo da Dani Carvajal sun maye gurbin Vinicius Jr da kuma Federico Valverde.
To sai dai Vinicius bai ji daɗi ba da aka cire shi daga fafatawar.
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wannan shafi ne da ke kawo muku muhimman abubuwan da ke faruwa a duniyar wasanni daga Asabar 25 zuwa 31 ga watan Oktoban 2025
Mohammed Abdu
Rodrygo da Dani Carvajal sun maye gurbin Vinicius Jr da kuma Federico Valverde.
To sai dai Vinicius bai ji daɗi ba da aka cire shi daga fafatawar.
Tun farko Barcelona ta sa ran yin kan-kan-kan a yawan samun nasara a El Clasico
Kafin nan karawar Real Madrid ta yi nasara 105 a fafarawar El Clasico, ita kuwa Barcelona tana da 104.
Newcastle da Brighton da Fulham da Brentford duk suna zawarcin ɗan wasan Middlesbrough da Ingila Hayden Hackney mai shekara 23. (TBR Football)
Roma na son sake tattaunawa kan yarjejeniyar aro na ɗan wasan gaban Brighton da Jamhuriyar Ireland Evan Ferguson, inda ake ganin yiwuwar ɗan wasan mai shekara 21 zai koma ƙungiyar ta Premier a watan Janairu. (Gazzetta dello Sport)
Newcastle da Tottenham na zawarcin ɗan wasan bayan Juventus da Faransa Pierre Kalulu, mai shekara 25. (TuttoJuve)
Barcelona na sanya ido kan ɗan wasan Marseille ɗan ƙasar Ingila Mason Greenwood mai shekara 24. (Sun)
Inter Milan na iya amincewa da tayin da Leeds ke yi wa Piotr Zielinski, inda ake ganin yiwuwar tafiyar ɗan wasan tsakiyar Poland mai shekara 31 a watan Janairu. (Football Insider)
Jami'ai daga Arsenal da Chelsea da Manchester City na sanya ido kan ɗan wasan gaban Bayern Munich da Jamus Lenart Karl mai shekara 17. (Caught Offside)
Real Madrid ta ci ƙwallo ta hannun Jude Bellingham, amma an soke da cewar an yi satar gida.
Mai masaukin baƙi ta yi canji, inda Brahim Diaz ya maye gurbin Arda Guler.
Filin wasa na Santiago Bernabeu sai shewa ake daga magoya bayan Real Madrid, saboda maki ukun da suke fatan samu a karawar ta hamayya.
Barcelona tana ta kai kora domin ta farke ƙwallon da aka zura mata, har ma an yi kokarin bai wa Mbappe ƙwallo yana cikin gudu ta bugi dunduniyarsa, Barcelona ta sake karɓa ta kai kora.
Eder Militao ya jawo ƙwallo daga gefen hagu har cikin da'irar Barcelona, amma sai ya kama dibi-dibi kan wanda zai bai wa daga baya ya yi kokarin turawa Vinicius Junior, amma Barcelona ta ɓata ƙwallon.
An sa ƙwallo mai ƙyau daga Barcelona.
Marcus Rashford ya jawo ƙwallo cikin da'irar Real Madrid da ta kai ta je wajen Ferran Torres, amma bai samu damar farkewa ba.
Fermin Lopez ya ɗauka ya ci Real Madrid ƙwallon da zai farke wa Barcelona.
A gefen damansa ga Marcus Rashford sai kuma Ferran Torres daga hagunsa, amma sai ya zaɓi ya buga ƙwallon amma bai ci ba.
Thibaut Courtois ne ya tare ƙwallon.
To sai dai Kylian Mbappe ya buga, amma mai tsaron ragar Barcelona, Wojciech Szczesny ya hana ƙwallon ya shiga ragar ta tafi kwana.
Real Madrid ta yi korafin fenariti da cewar Eric Garcia ya taba ƙwallo da hannu.
An kara soke ƙwallon da Real Madrid ta ci.
Kylian Mbappe ne ya taɓa ta kuma hakika akwai satar gida.
Jude Bellingham ma ya taɓa ƙwallon a cikin rububi.
Real Madrid ta kara shiga gaban Barcelona
Real ce ta kai kora cikin gidan Barcelona kuma Jude Bellingham ne ya ci ƙwallon bayan da aka ci kasuwar sama sai kawai ƙwallon ya je kafar ɗan wasan tawagar Ingila, shi kuma bai jira ba ya sa kafa ya ci.
Arda Guler ya yi sakacin da Pedri ya karɓi ƙwallo ya kuma kai mugun hari.
Marcus Rashford ya karba ya bai wa Fermin Lopez wanda ya buga ƙwallon ta wuce Thibaut Courtois.
Kylian Mbappe ne ya ja ƙwallo da gudu cikin gidan Barcelona daga nan ya bai wa Vinicius, shi kuma sai da ya tsaya ya duba, koda yake ya ɗaga ƙwallon amma ba ta wuce Wojciech Szczesny ba, wanda ya sa hannu.
Dama mai kyau da Barcelona ta samu na farke ƙwallon
Ferran Torres ne ya jawo ƙwallon daga kusurwa koda yake Thibaut Courtois bai yi wahalar kama ƙwallon ba.
Real Madrid ta samu dama mai kyau, amma cikin ruwan sanyi Wojciech Szczesny ya taɓa ta je kwana.
Kylian Mbappe ne ya ja ƙwallon domin ya kara na biyu.