Turkiya za ta ladabtar da raflin da suke yin caca a fannin taka leda
Hukumar ƙwallon kafar Turkiya, TFF za ta ɗauki matakin ladabtarwa ga duk raflin da aka same shi ya yi caca a wasan tamaula, bayan da aka gano cewar da damansu suna da asusun yin caca.
Cikin rahoton da aka bankaɗo alkalan wasan kasar 371 daga 571 da suke kwararrun a Turkiya suna da asusun yin caca, kuma 152 suna yin cacar gadan-gadan.
Kuma daga cikinsu har da manyan rafli bakwai da mataimaka 15, kuma wasu daga ciki sun yi caca sau 18,227 da kuma guda 42 da suka yi sama da 1,000 da wasu sau ɗaya tal suka yi.
Idan aka tabbatar da laifin, za a iya dakatar da alkalin tamaula daga busa wasa daga wata uku zuwa shekara ɗaya.