Ya za a kwatanta ƙarfin sojin Najeriya da na ƙasashen Afirka ta yamma?

Asalin hoton, Getty Images
Tun bayan ɗauki da sojojin saman Najeriya suka kai ƙasar Benin inda suka taimaka wajen daƙile yunƙurin juyin mulki da sojoji suka so yi, da kuma amincewar da majalisar dokoki ta yi na buƙatar Bola Tinubu na aikewa da rundunar soji zuwa Benin ɗin domin wanzar da zaman lafiya, ƴan Najeriya da ma Afirka sanin irin karfin da Najeriya ke da shi idan aka kwatantan da sauran ƙasashen Sahel.
Alƙaluman World Factbook sun nuna cewa dakarun Najeriyar 180 na Sudan da Sudan ta Kudu, inda ta aike da dakaru 200 zuwa Gambia a ƙarƙashin ƙungiyar Ecowas sai kuma 150 da ke Guinea-Bissau nan ma a ƙarƙashin ƙungiyar Ecowas.
Wannan ne ya sa ƴan Najeriya da ma Afirka ke tambayar shin Najeriyar ce ta fi kowace ƙasa ƙarfin soji? Yaya za a kwatanta ƙarfin sojin na Najeriya da sauran ƙasashen Afirka ta yamma?
