Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 21/02/2025

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 21/02/2025

Rahoto kai-tsaye

Usman Minjibir, Annur Mohammad, Isiyaku Muhammed, Haruna Kakangi, da Umar Mikail

  1. Isra'ila ta ce motocin da suka fashe a Tel Aviv harin ta'addanci ne

    Isra'ila

    Asalin hoton, Reuters

    Ministan tsaron Isra'ila, Isreal Katz ya ce ya umarci dakarunsu da su ƙaddamar da hare-hare a yankin gaɓar yamma da kogin Jordan da aka mamaye, bayan fashewar wasu motocin bas uku da babu kowa a cikinsu a kusa da Tel Aviv.

    Babu rahoton jikkata daga fashewar motocin, an kuma samu nasarar lallata ƙarin wasu bama-bamai a cikin wasu motocin daban.

    Wakiliyar BBC ta ce kafofin watsa labaran yankin sun ruwaito cewa a cikin bama-baman da ƴansanda suka yi nasarar kwancewa, guda daga ciki an rubuta saƙon ɗaukar fansa kan samamen da sojojin Isra'ila suka kai a sansanin ƴangudun hijira na Tulkarem.

    Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu ya amince da aikin soji a yankin na gaɓar yamma da tekun Jordan, sannan ya umarci jami'an tsaron ƙasar su ƙara sa ido domin daƙile wasu hare-hare a yankin.

  2. Isra'ila ta ce gawarwakin da Hamas ta mayar kisan gilla aka musu

    Isra'ila

    Asalin hoton, Reuters

    Rundunar sojin Isra'ila ta ce cikin gawar da Hamas ta ba su jiya a Gaza a matsayin na Shiri Bibas, ba ita ba ce.

    Haka kuma sun ce ƙananan yaranta biyu da aka dawo da gawarwakinsu, kisan gilla aka yi musu.

    Sojojin Isra'ila ta zargi Hamas da karya yarjejeniyar tsagaita wuta da buƙatar ta dawo musu da gawar Shiri Bibas.

    A jiya Alhamis ne Hamas ta miƙa gawarwakin mutum huɗu, inda ta ce daga ciki akwai gawar Shiri da ƴaƴanta biyu, inda Isra'ila ta fara binciken ƙwaƙwaf domin tantance gawarwakin.

  3. Majalisa ta buƙaci a kafa sansanin soji a yankin Bukuyum na Zamfara

    Soji

    Asalin hoton, Other

    Majalisar wakilan Najeriya ta yi kira da a kafa sansanin soji a yankin Bukuyum sakamakon ƙamarin matsalar tsaro a yankin.

    Ɗanmajalisar da ke wakiltar yankin, Sulaiman Abubakar Gumi ne ya gabatar da ƙudirin buƙatar hakan, inda ya ce ƴanbindiga sun mayar da yankinsa matsayin mafaka.

    Ya ce suna tserewa yankin ne sakamakon yaƙarsu da ake yi a yankin Shinkafi da kuma sulhun da gwamnatin Kaduna ta yi da su.

    Sojojin ƙasar dai sun ce suna ci gaba da luguden wuta kan ƴanbindiga, kuma sun ce suna samu nasara.

  4. Assalamu alaikum

    Jama'a barkanmu da wannan safiya ta Juma'a daga nan sashen Hausa na BBC, inda za mu kawo muku labaran kai-tsaye na abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya.

    Za ku iya leƙawa shafukanmu na sadarwa irin su Facebook da X da Instagram domin karanta wasu labaran da kallon hotuna da bidiyo.

    Ku kasance tare da mu.