Kungiyar kare hakkin bil'adama ta Human Rights Watch ta yi zargin
cewa kungiyoyi ‘yan bindiga da kuma dakarun gwamnatoci a yammacin Afrika sun
tafka ta’asa ba tare da daukar wani mataki ba a shekara ta 2024.
A rahoton da ta fitar na sabuwar shekara, kungiyar ta Human Rights
Watch ta ce dubban mutane sun rasu wadansu kuma an jima musu raunuka amma kuma
ba a dauki hukunci ba.
Kungiyar Human Rights Watch ta ce a shekarar ta da wuce ta yi
Nazari kan cin zarafin bil adama a kasashe fiye da 100 a duniya, abin da ya
ba ta damar fitar da wannan rahoto na ta ke nan.
Rahoton, mai shafi 546 ya nuna cewa a kasashe da dama
gwamnatoci sun murkushe masu zana-zanga da karfi, an kama mutane ba tare da sun
aika ta laifi ba sannan kuma an garkame abokan hamayya na siyasa a kurkuku. Tare
da cin zarfin ‘yan jarida da kuma masu rajin kare hakkin bil'adama.
Kungiyar ta ce ƴan bindiga da sojojin gwamnati sun kashe fararen
hula babu gaira babu dalili, waɗansu mutanen an raba su da muhallansu.
A cewarta, a kasashe fiye da 70 a bara da aka gudanar da zabe,
shugabanni masu kama karya sun kara karfi tare da kafa dokoki na zalunci.
Shugaban Human Rights Watch a Afrika, Mausi
Samuel ya ce akwai bukatar kungiyar tarrayar Afrika AU ta gudanar da bincike
kan irin munanan cin zarafin bil adama da ake yi a nahiyar.
A kan Najeriya kuwa rahoton ya ce akwai rauni game da irin matakan da gwamnati
ke dauka wajen hukunci ‘yan bindiga saboda yadda suka raba miliyoyin mutane da
muhallansu tare da kashe daruruwan mutane.
Kungiyar ta human rights watch ta ce sauye-sauyen tattalin arziki
a Najeriya sun jawo mummunan talaucin da ba a taba gani ba a cikin shekaru 30
kuma babu wani tsari na hakika da gwamnati ta dauka domin magance matsalar, sai
ma ta yi amfani da karfin da ya wuce kima wajen hana zanga-zangar tsadar
rayuwa.
Rahoton kungiyar kuma ya taɓo irin ta’asar da aka tafka na cin
zarafin bil'adama a kasashen Guinea, da Mali da Nijar da kuma Burkina Faso
wadanda sun kara nuna irin gwamnatocin da ke shugabanci a yankunan.