Usman Minjibir, Isiyaku Muhammed da Aisha Aliyu Jaafar
Amurka ta sanya wa shugaban gwamnatin sojin Sudan takunkumi
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Shugaban mulkin soji na Sudan, Abdel Fattah al-Burhan
Amurka ta sanya wa shugaban sojin Sudan, Adel Fattah al Burhan takukumi saboda rawar da yake takawa a kazamin yakin basasar kasar.
Ko a makon da ya gabata, gwamnatin Amurka ta sanya irin wannan takunkumi kan kwamandan dakarun RSF, Mohamed Hamdan Dagalo.
Amurka ta zargi sojoji da cigaba da amfani da makamai masu guba a yakin da suke yi.
Tun a shekarar 2023 bangarorin biyu ke yaki, yanayin da ya jefa kusan rabin al'ummar Sudan cikin yunwa.
Manufofin gwamnatin Najeriya sun tsunduma al'umma cikin talauci a 2024 - HRW
Asalin hoton, State House, Nigeria
Bayanan hoto, Shugaban Najeriya, Bola Tinubu
Kungiyar kare hakkin bil'adama ta Human Rights Watch ta yi zargin
cewa kungiyoyi ‘yan bindiga da kuma dakarun gwamnatoci a yammacin Afrika sun
tafka ta’asa ba tare da daukar wani mataki ba a shekara ta 2024.
A rahoton da ta fitar na sabuwar shekara, kungiyar ta Human Rights
Watch ta ce dubban mutane sun rasu wadansu kuma an jima musu raunuka amma kuma
ba a dauki hukunci ba.
Kungiyar Human Rights Watch ta ce a shekarar ta da wuce ta yi
Nazari kan cin zarafin bil adama a kasashe fiye da 100 a duniya, abin da ya
ba ta damar fitar da wannan rahoto na ta ke nan.
Rahoton, mai shafi 546 ya nuna cewa a kasashe da dama
gwamnatoci sun murkushe masu zana-zanga da karfi, an kama mutane ba tare da sun
aika ta laifi ba sannan kuma an garkame abokan hamayya na siyasa a kurkuku. Tare
da cin zarfin ‘yan jarida da kuma masu rajin kare hakkin bil'adama.
Kungiyar ta ce ƴan bindiga da sojojin gwamnati sun kashe fararen
hula babu gaira babu dalili, waɗansu mutanen an raba su da muhallansu.
A cewarta, a kasashe fiye da 70 a bara da aka gudanar da zabe,
shugabanni masu kama karya sun kara karfi tare da kafa dokoki na zalunci.
Shugaban Human Rights Watch a Afrika, Mausi
Samuel ya ce akwai bukatar kungiyar tarrayar Afrika AU ta gudanar da bincike
kan irin munanan cin zarafin bil adama da ake yi a nahiyar.
A kan Najeriya kuwa rahoton ya ce akwai rauni game da irin matakan da gwamnati
ke dauka wajen hukunci ‘yan bindiga saboda yadda suka raba miliyoyin mutane da
muhallansu tare da kashe daruruwan mutane.
Kungiyar ta human rights watch ta ce sauye-sauyen tattalin arziki
a Najeriya sun jawo mummunan talaucin da ba a taba gani ba a cikin shekaru 30
kuma babu wani tsari na hakika da gwamnati ta dauka domin magance matsalar, sai
ma ta yi amfani da karfin da ya wuce kima wajen hana zanga-zangar tsadar
rayuwa.
Rahoton kungiyar kuma ya taɓo irin ta’asar da aka tafka na cin
zarafin bil'adama a kasashen Guinea, da Mali da Nijar da kuma Burkina Faso
wadanda sun kara nuna irin gwamnatocin da ke shugabanci a yankunan.
Isra'ila ta 'kashe mutum 73' a Gaza bayan amincewa da tsagaita wuta
Asalin hoton, AFP
Isra'ila ta ci gaba da kai hare-hare ta sama a Gaza gabanin fara aikin yarjejeniyar tsagaita wuta da sakin waɗanda Hamas ke garkuwa da su, da aka amince da ita a jiya Laraba.
Ana sa ran yarjejeniyar za ta fara aiki ne a ranar Lahadi, idan majalisar gudanarwar Isra'ila ta amince da ita.
Wasu hare-hare da Isra'ila ta kai a Gaza, jim kaɗan bayan amincewa da yarjejeniyar a daren Alhamis sun kashe aƙalla mutum 73, kamar yadda hukumomi a yankin suka ruwaito.
Ma'aikatar lafiya a Gaza ta ce cikin mutanen da abin ya rutsa da su akwai mutum 12 wadanda ke zama a wani gida da ke unguwar Sheikh Radwan, a birnin Gaza.
Tun farko, ma'aikatar tsaro ta Isra'ila ta bayar da rahoton faɗawar wani makami da aka gani a kudancin ƙasar ta Isra'ila a yau Alhamis, sai dai daga baya ta ce kuskure ne.
Wani likita a asibitin Baptist da ke birnin Gaza ya ce ma'aikata "ba su samu hutun koda minti ɗaya ba" a cikin daren.
"An ci gaba da kawo waɗanda aka raunata," in ji Dakta Amjad Eliwah, kamar yadda ya shaida wa BBC.
Ya ce "an tura gawarwaki kai-tsaye zuwa mutuware".
"Da farko kowa na ta farin ciki" saboda labarin tsagaita wuta.
"To amma yanzu mutanen da ke murna sun zama gawa."
Sai Hamas ta amince da yarjejeniya kafin majalisarmu ta zauna - Isra'ila
Mai magana da yawun gwamnatin Isra'ila, David Mencer wanda yake bayar da bayani dangane da yarjejeniyar tsagaita wutar, ya nanata aniyar Isra'ila cewa Hamas na ƙoƙarin karya alƙawari wanda ya ce ya janyo "tsaiko a ƙoƙarin da ake yi na cimma al'amarin a ɗan ƙaramin lokaci na ƙarshe."
Ya kuma ce ba zai yiwu ba majalsiar tsaron Isra'ila ta zauna ba tare da masu shiga tsakani sun sanar da gwamnatin Isra'ila cewa Hamas ta amince da yarjejeniyar da tun a baya aka amince da ita.
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin motoci ɗauke da kayan jinƙai suka yi cirko-cirko a hanyar shiga Gaza inda suke jiran su ji an amince da yarjejeniyar sannan kuma a ba su damar shiga yankin.
Kaso 90 na al'ummar Gaza dai na fama da ƙarancin kayan agaji.
Ƙungiyar Tarayyar Turai ta sanar da bayar da kayan jinƙan na miiyoyin kuɗi.
Shugaban Koriya ta Kudu da aka kama ya ƙi amsa tambayoyi
Asalin hoton, Getty Images
Shugaban Koriya Ta Kudu da aka dakatar, Yoon Suk Yeol, yaƙi yarda ya amsa tambayoyin da ake masa a rana ta biyu da kama shi.
Ana dai tuhumar sa ne da sanya dokar soji da ba ta samu karɓuwa ba a ƙasar.
A jiya Laraba ne da safe wasu jami'ai masu bincike kimanin 1000 tare da ƴansanda suka kama shi, inda yake fuskantar tuhuma kan karya dokokin mulki.
Akwai kotun da kuma ke sauraron ƙarar da lauyoyinsa suka shigar na ƙalubalantar sammancin kama shi da suka an saɓa ka'ida.
Kotun mulkin ƙasa na ci gaba da zaman yanke hukunci kan tabbatar da soke shi daga mulki ko kuma akasin hakan.
Bisa tsarin sammaci, masu binciken ka iya riƙe mista Yoon har tsawon awanni 48, kuma daga nan ne suke buƙatar samun sabon sammaci na ci gaba da tsare shi domin ci gaba da bincike.
Idan aka samu wannan sammaci, to za su iya ci gaba da tsare shi har tsawon ƙarin kwana 20 kafin a gurfanar da shi a gaban kuliya.
Idan kuma ba a samu sabon sammacin ba to dole ne a sake shi bayan ƙarewar awanni 48 ɗin.
Magoya bayan mista Yoon dai na ci gaba da gudanar da zanga-zanga domin nuna ƙin amincewarsu da kamun nasa.
Asalin hoton, Getty Images
Koriya ta Arewa ta buɗe iyakarta ga masu yawon buɗe ido tun bayan korona
Asalin hoton, Getty Images
Koriya Ta Arewa ta sake buɗe daya daga cikin iyakokin biranenta ga baki 'yan yawon buɗe ido a karon farko cikin shekaru biyar.
Hukumomi sun tabbatar da cewa 'yan China da sauran baki daga sauran ƙasashe na da damar zuwa birnin Rason da ke arewacin ƙasar.
Koriya Ta Arewa ce kasa ta farko da ta soma rufe iyakarta lokacin ɓullar annobar korona.
Baki dubu biyar ne ke kai musu ziyara a duk shekara kafin rufe iyakar.
Bai kamata a bai wa tsirarrun attajirai dama a Amurka ba - Biden
Asalin hoton, Getty Images
Shugaba Biden ya yi amfani da jawabinsa na bankwana domin gargaɗin Amurkawa kan haɗarin da ke tattare da ba wasu tsirarun mutane attaijrai mahimmanci a mulki.
Mista Biden wanda zai sauka daga muƙami nan da kwana biyar, ya ce baiwa attajirai damar da ta wuce iyaka barazana ce ga Amurka.
Wakiliyar BBC ta ce Biden ya ce hakan yana da hatsari kai tsaye ga dimokradiyya da kuma haƙƙin Amurkawa.
Ya kuma yi kakkausan suka ga kamfanonin shafukan sada zumunta kan yin watsi da binciken gaskiya, inda ya ce sun bar Amurkawa cikin duhun kai ta hanyar yaɗa labaran da ba na gaskiya ba.
Mun samar wa gwamnatin tarayya naira tiriliyan 10 a 2024 - NNPCL
Asalin hoton, NNPC
Kamfanin man fetur na Najeriya NNPCL ya ce ya zuwa watan Satumban shekarar 2024, kuɗin da ya samar wa gwamnatin tarayya ya kai naira tiriliyan 100.
Shugaban kamfanin, Mele Kyari ne ya sanar da hakan a lokacin da ya bayyana a gaban kwamitin kuɗi na majalisar dattawa, inda yake kare kasafin kuɗin kamfanin na bana.
Ya ce NNPCL na fitar da bayanan asusunsa na shekara-shekara, "Hada-hadarmu a fili suke, kuma muna bayyana duk harkokin kuɗin da muka yi a fili ba tare da nuƙu-nuƙu ba," in ji shi kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Kyari ya ce kamfanin na NNPCL ne kamfanin da ya fi biyan haraji, kuma wanda ya fi samar da riba ga masu zuba jari.
Sai dai ya ce sai sun zauna tare da daraktocin kamfanin ne za su iya fitar da hasashen kuɗin da za su samar a bana.
Duk ɗanwasan da ya je Real Madrid zai lashe kofuna - Khedira
Asalin hoton, Getty Images
Tsohon ɗanwasan Real Madrid da Jamus, Sami Khedira ya ce da zarar ɗanwasa ya je ƙungiyar Real Madrid, to lallai zai fara lashe kofuna saboda ƙoƙarin samun nasara wabiji ne a kan kowane ɗanwasa.
Tun a kakar 1955-56, da aka fara fafata gasar cin kofin zakarun turai, wanda tsohon shugaban ƙungiyar, Santiago Bernabeu ya taimaka wajen assasawa, ƙungiyar ta Spain ta lashe gasar sau 15, na ƙarshen ne suka lashe a kakar 2023-24.
Ƙungiyar AC Milan ta Italiya ce ke biye mata, inda ta lashe kofuna bakwai, wanda hakan ya nuna yadda Real ɗin ta yi fintikau.
A game da hakan ne, tsohon ɗanwasan tsakiya na ƙungiyar, wanda yake cikin ƴanwasan da suka lashe gasar karo na 10 wato La Decima a kakar 2013-2014, ya ce ai da Real Madrid da kofuna, ɗanjuma ne da ɗanjummai.
"Da zarar ka je ƙungiyar, dole ne ka yi iya yinka domn ƙungiyar samun nasara idan ka je. Neman sakamako mai kyau da lashe kofuna wajibi ne," in ji shi a wani shiri na musamman da BBC ta yi kan yadda Real Madrid ta yi kaka-gida gasar.
Gwamnatin Najeriya za ta yi wa fursunoni afuwa domin rage cunkuso
Asalin hoton, OTHER
Gwamnatin tarayyar Najeriya za ta yi wa wasu fursunoni afuwa domin ta rage cunkuson da ake fuskanta a gidajen gyara halin ƙasar.
Domin tabbatar da hakan ne, gwamnatin ta kafa wani kwamiti a ranar Laraba, ƙarƙashin ministan shari'a, Lateef Fagbemi kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Sakataren gwamnatin tarayya na Najeriya George Akume, wanda ya jagoranci kafa kwamitin, ya ce sashe na 175 na kundin tsarin mulkin ƙasar ya ba shugaban ƙasa damar yin afuwa ga fursunoni.
Ko a zamanin mulkin tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, an yi irin wannan afuwar, inda a watan Afrilun 2022 aka yi afuwa ga wasu fursunoni, ciki har da tsohon gwamnan Filato, Joshua Dariye da tsohon gwamnan Taraba, Jolly Nyame.
An yi kira ga gwamnonin arewa su bunƙasa ɓangaren kiwo
Asalin hoton, Getty Images
Ƙungiyar masu fatauci da kiwo da sarrafa naman shanu ta Nijeriya ta yi kira ga gwamnonin jihohin arewa su samar da tsarin da zai bunƙasa harkokin kiwon dabbobi don bunƙasa samar da nama da madara a ƙasar.
Ƙungiyar ta ce abin damuwa ne ganin yadda makiyaya suke fama saboda ƙarancin abincin da za su bai wa dabbobinsu da zarar damuna ta wuce.
Mallam Iliyasu Bulama, shi ne shugaban wannan ƙungiya, ya ce ƙungiyar na buƙatar gwamnonin su sa hannu domin sauƙaƙa hanyoyin inganta kiwo a yankin.
ICPC ta sake maka wani hadimin El-Rufai a kotu bisa zargin almundahana
Asalin hoton, GovKaduna
Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta Najeriya ICPC ta sake kai ƙarar wani hadimin tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, Jimi Lawal bisa zargin almundahana.
Takardar ƙarar mai lamba FCH/KD/16c/2025, ta nuna cewa ana tuhumarsa ne tare da wani mai suna Umar Waziri da Yusuf Inuwa da wani kamfani mai suna Solar Life Nigeria Limited bisa zargin karkatar da kuɗin gwamnati, kamar yadda tashar Channles ta ruwaito.
Mataimakin babban lauyan hukumar, Osuobeni Akponimisingha ne ya shigar da ƙarar a madadin hukumar kan tuhume-tuhume guda biyar a babbar kotun tarayya da ke Kaduna.
Wannan ƙarar na zuwa ne makonni bayan hukumar ta maka tsohon kwamishina kuma tsohon shugaban ma'aikatan gidan gwamnati a zamanin mulkin El-Rufai, Bashir Saidu.
ƙudurin harajin Najeriya zai yi wa jami'o'i illa - ASUU
Asalin hoton, Academic Staff Union of Universities - ASUU/Facebook
Ƙungiyar malaman jami’o’i ta Najeriya (ASUU) ta bayyana damuwa kan ƙudurin gyara dokokin harajin Najeriya na 2024, wanda ta ce "wata kutungwila ce".
Ƙungiyar ta ce ana so a yi amfani da ƙudurin ne domin a kashe asusun tallafawa manyan makarantu na TETFund.
ASUU ta ce yunƙurin idan ya tabbata - zai janyo gagarumin koma-baya ga ci gaban da aka samu a jami'o'i da manyan makarantun gwamnati a Najeriya.
Farfesa Abdulƙadir Muhammad shi ne shugaban ƙungiyar shiyyar Kano, ya shaida wa BBC bayan nazari da suka yi a kan ƙudurin gyara dokokin harajin sun gano akwai sashen da zai haifar da matsala ga ɓangaren ilmin ƙasar, musamman jami’o’i.
Gobarar Amurka: An fara samun sauƙin iska a kudancin California
Asalin hoton, Getty Images
An samu sauƙin iska a kudancin California, inda ya baiwa ma'aikatan kashe gobara damar samun hutu a lokacin da suke ci gaba da ƙoƙarin shawo kan mummunar gobara a Los Angeles.
Masu hasashe sun ce iskar teku kuma za ta kawo danshi a cikin kwanaki masu zuwa, da zai ƙara kawo sauƙin yanayin da ake ciki.
Ɗaya daga cikin masu hasashen James White ya ce, "mun gode Allah, yanayin da muka yi hasashe labari ne mai daɗi, saboda an wuce lokacin da ake fuskantar gagarumar barazana," in ji shi.
Gobarar wacce ta fara sama da mako guda ta kashe aƙalla mutum 24 tare da ɓarnata manyan yankunan birnin, inda har yanzu mummunar gobarar ke ci gaba da ci a wasu yankunan.
Shugaban Koriya ta Kudu da aka tsige ba zai halarci zaman bincike ba saboda rashin lafiya
Asalin hoton, Getty Images
Alamu na nuna cewa shugaban Koriya ta Kudu Yoon Suk Yeol wanda aka kama a ranar Laraba ba zai iya halartar yini na biyu na tambayoyin da ake masa kan cin hanci da rashawa ba.
An dai fara zama na farko ne ba tare da tsigaggen shugaban ƙasar ba, sannan ana tunanin ba zai samu halartar zama na biyu ba a yau.
Lauyan shugaban da aka tsige ya nuna cewa ba shi da lafiya ne shi ya sa ba zai samu halartar zaman ba.
Mista Yoon ya kwana a tsare bayan da ya ƙi amsa wasu tambayoyi bayan da aka kamashi a harabar fadar shugaban ƙasar, inda jami'an tsaro suka kutsa fadar suka kama shi.
An tsige shugaban ne bayan yunƙuri na yin amfani da dokar soji a watan da ya gabata.
Kuɗin da aka kasafta wa ɓangaren noma ya yi kaɗan - Majalisar Najeriya
Asalin hoton, Getty Images
Majalisar dattawan Najeriya ta ce akwai jan aiki a gaban gwamnati wajen kawar da yunwa a ƙasar bisa la'akari da kasafin kuɗin da aka ware wa harkokin noma a bana.
Kwamtitin majalisar mai kula da noma da raya karkara ne ya bayyana damuwa a kan rage kuɗin da za a kashe wa harkar noma a cikin kasafin 2025.
Gwamnati dai ta keɓe wa ɓangaren noma naira billiyan ɗari takwas da ashirin da shida wato kashi 1.7 na kasafin kuɗin na bana ne.
Sanata Salihu Mustapha shi ne shugaban kwamitin noma a majalisar, ya bayyana cewa wannan kasafin da aka ware ya yi kaɗan domin bunƙasa ɓangaren.
Majalisar Isra'ila za ta zauna domin amincewa da yarjejeniyar tsagaita wuta
Asalin hoton, Amir Cohen / Getty Images
A daidai lokacin da wasu ƴan Isra'ila suke farin cikin cimma yarjejeniyar tsagaita da aka daɗe ana hanƙoro a Gaza, wadda za ta sa a sako musu ƴanuwansu da ake garkuwa da su, a ɗaya ɓangaren kuma ana tsimayin matakin majaliar ƙasar.
Dole sai majalisar za ta zauna a safiyar yau ne domin amince da yarjejeniyar, kafin ta cika.
Sai dai akwai ministocin masu tsattsauran ra'ayi guda biyu da suka yi barazanar ajiye muƙaminsu da zarar aka amince da yarjejeniyar ta tsagaita wuta.
Ana tunanin a ranar Lahadi ne za a sako mutum uku daga cikin waɗanda aka yi garkuwa da su a Gaza su koma Isra'ila, duk da cewa wani babban jami'in Hamas ya shaida wa BBC cewa ana tattaunawa domin fara sakin waɗanda aka kama ɗin.
Assalamu alaikum
Jama'a masu bibiyarmu a wannan shafi na BBC Hausa, da ke kawo muku labaran abubuwan da ke wakana a Najeriya da sauran sassan duniya kai tsaye, barkanmu da safiyar ranar Alhamis.
Za ku iya leƙawa shafukanmu na sadarwa irin su Facebook da Instagram da X domin karanta wasu labaran da kallon hotuna da bidiyo da ma tafka muhawara.