Sama da mutum 14 sun mutu a ramin haƙar zinare a Mali
Rahoto kai-tsaye
Muhammad Annur Muhammad da Abdullahi Bello Diginza
Rufewa
Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye nan muka kawo ƙarshen labarai da rahotonnin abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.
Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu, za mu sake dawowa domin ci gaba da kawo muku sabbin labarai.
Amma kafin goben, a nan muke cewa mu kwana lafiya.
Tarayyar Turai ta soki Trump kan tamakansa kan haraji
Asalin hoton, Getty Images
Ƙungiyar Tarayyar Turai ta soki matakin shugaban Amurka Donald Trump ya ɗauka na sanya wa manyan abokan hulɗar kasuwancin Amurka ƙarin haraji
Haka kuma EU ta yi gargaɗin cewa ita ma za ta mayar da martani idan shugaban ya aiwatar da barazanar da ya yi na ƙaƙaba wa ƙasashen Turai irin wannan harajin.
Shugaban gwamnatin Jamus, Olaf Scholz ya ce kowa ya na cin gajiyar yadda hada-hadar kasuwanci ke gudana a duniya a halin yanzu.
Sai dai Firaministan Birtaniya, Sir Keir Starmer ya ɗan yi taka tsan-tsan da kalamansa inda ya ce ƙasarsa za ta sa ido ta gani domin yanzu ne mulkin Trump ya fara kuma yana son ƙulla hulɗar kasuwanci mai ƙarfi da Amurka.
Shugaban riƙo na Syria ya ce Saudiyya na da muradin tallafa wa ƙasarsa
Shugaban riƙo na ƙasar Syria, Ahmed Al-Shaara, ya ce Saudiyya ta bayyana ra'ayin taimaka wa sake gina ƙasarsa.
Al-Shaara ya bayyana hakan ne bayan ganawarsa da yarima mai jiran gado Mohammed bin Salman a birnin Riyadh,
Sabon shugaban na Syria ya ce dangantakar da ke tsakanin ƙasshen biyu ta haifar da abubuwa masu matuƙar alfanu da kowa ke iya gani, kuma suna son mu ci gaba da inganta ta.
Masu sharhi sun yi bayanin cewa zaɓen Saudiyya da Al-Shaara ya yi a matsayin ziyararsa ta farko zuwa ƙasashen ƙetare na nuni da irin sauyin da ake samu a yankin
'Sojojin Najeriya sun lalata wurare 12 da ake tace man fetur ba bisa ƙa'ida ba'
Asalin hoton, Defence HQ/X
Bayanan hoto, Hafsan hafsoshin Najeriya, Janar CG Musa
Rundunar sojin Najeriya ta ce ta lallata wurare 12 da ake tace man fetur ba bisa ƙa'ida a yankin Naija Delta da ke kudancin ƙasar.
Cikin wata sanarwar da muƙaddashin daraktan yaɗa labaran runduna ta 6 ta sojin Najeriya da ke birnin Fatakwal, Laftanar Kanal Jonah Danjuma ya fitar ranar Lahadi, ya ce dakarun sun kuma ƙwato lita 70,000 na man fetur, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
Sojojin sun ce a wani farmakin mako guda da suka ƙaddamar tare da haɗin gwiwar sauran jami'ar tsaro sun samu nasarar lalata ƙananan jiragen ruwa shida da ƙwato bututun mai tara da aka sace, tare da kama mutum 16 da suke zargi da hannu a jihohin yankin huɗu.
Sanarwar sojojin ta kara da cewa dakarun sun ƙaddamar da farmakin ne tun daga ranar 27 ga watan Janairu zuwa 2 ga watan Fabarirun 2025.
Yankin Naija Delta ya yi ƙaurin suna da ayyukan ɓata-gari, waɗanda ke fasa bututun man fetur tare da sace man, wani abu da masana ke bayyanawa da yi wa tattalin arziin ƙasa zagon ƙasa.
Man fetur shi ne kan gaba a hanyoyin da Najeriya ke samun kuɗaɗen da gwamnati ke samu.
Duk da karin harajin da muƙa kaƙaba wa ƙasashe uku za su taimaka mana - Trump
Asalin hoton, Getty Images
Shugaban Amurka, Donald Tump ya ce duk da cewa harajin da ya ƙaƙaba wa Canada da Mexico da China na iya haifar da raɗaɗi ga Amurka, amma ya ce daga baya kwalliya za ta biya kuɗin sabulu.
Ya yi alƙawarin cewa manufofinsa za su haifar da sakamako mai ban sha'awa, amma bai ambaci harajin ramuwar gayya da Kanada da Mexico suka ce za su sanya kayayyakin Amurka ba.
Jakadiyar Canada a Washington, Kirsten Hillman, ta ce tana fatan harajin ba zai ta fara aiki a ranar Talata kamar yadda aka tsara ba, yayin da ake ci gaba da tattaunawa.
Ta ce ba mu da sha'awar ta'azzara lamarin amma ina ganin za a buƙaci gwamnatinmu ta tabbatar da cewa mun tsaya tsayin daka kan yarjejeniyar kasuwancin da muka riga muka ƙulla da Amurka
An kashe sojojin Tanzaniya biyu da raunata huɗu a JD Kongo
An kashe sojojin Tanzaniya biyu da raunata huɗu a lokacin da suke taimaka wa dakarun Jamhuriyar Dimokraɗiyyar Kongo yaƙar 'yantawayen M23.
Kakakin rundunar sojin ƙasar, Kanal Gaudentius Ilonda ya ce sojojin waɗanda ke cikin sojojin SAMIDRC da ke aikin wanzar da zaman lafiya a gabashin DR Kongo sun mutu ne sakamakon harin 'yantawayen M23 a gabashin Kongo.
Cikin wata sanarwa da rundunar sojin Tanzaniya ta fitar, ta ce an kai harin ne a garin Sake da ke Goma tsakanin 24 zuwa 28 ga watan Janairu.
Hukumomin Tanzaniya sun ce suna shirye-shiryen mayar da gawarwakin zuwa ƙasar, yayin da waɗanda suka jikkata ke karɓar magani yanzu haka a asibitin Goma.
'Yansanda na binciken matar Firaministan Isra'ila kan babban laifi
Asalin hoton, Reuters
Ofishin babban lauyan gwamnatin Isra'ila ya ce 'yansanda sun fara gudanar da binciken aikata babban laifi a kan matar Firaministan ƙasar Benjamin Netanyahu, a kan zargin neman ɓatar da shedar shari'a.
Bayanin ya ƙara da cewa binciken farko da aka ƙaddamar a watan Disamba bayan wani fim da ke zargin, Sara Netanyahu ta bayar da umarnin muzanta wani babban sheda a shari'ar da ake yi wa mijinta kan rashawa.
Kotu ta samu Sarah Ntanyahu da laifin ɓarnata kuɗin gwamnati a 2019.
Isra'ila ta tsananta hare-hare a Gaɓar Yamma
Sojojin Isra'ila sun ce sun kashe tarin 'yanbindigar Falasɗinawa a hare-hare ta sama a yankin Gabar Yamma da ta mamaye, a jiya Asabar, yayin da take ta faɗaɗa hare-haren da take kaiwa a arewacin yankin.
Rundunar ta ce dakarunta sun shiga garin Tamun da daddare, kuma sun ce sun kama makamai da dama.
Sai dai ma'aikatar lafiya ta Falasɗinu ta ce hare-haren na Isra'ila a yankin Jenin sun kashe mutum biyar, ciki har da wani yaro mai shekara 16.
Wasu rahotanni na cewa sojin na Isra'ila sun kai hare-haren bam a sansanin 'yangudun hijira na Jenin.
Farmakin na Isra'ila na yanzu wanda ya shiga kwana na 12, ana ganin ya lalata aƙalla gida 20, inda take jefa bama-bamai.
Yayin da ake hakan Firaministan Isra'ilan Benjamin Netanyahu zai tafi Amurka inda zai gana da Shugaba Trump.
Dangote ya rage farashin man fetur a Najeriya
Asalin hoton, Getty Images
Matatar man Dangote ta rage farashin man fetur daga naira 950 zuwa 890, inda ragin ya fara aiki tun daga jiya Asabar 1 ga watan Fabarairun 2025.
A bayanin da matatar ta fitar ta nuna cewa ta yi ragin ne saboda raguwar farashin ɗanyen mai a kasuwar duniya.
Matatar ta ce hakan na daga ƙudurinta na tabbatar da gaskiya da adalci a harkar, a duk lokacin da aka samu rangwame a kasuwar duniya ita ma ta yi hakan ta yadda al'umma za su amfana.
Ta kara da cewa ta yi amanna ragin zai sa a samu saukin farashin a faɗin Najeriya, wanda hakan ta ce zai sa a samu saukin farashin kaya da ayyuka da saukin rayuwa gaba ɗaya.
Matatar ta kuma yi kira ga 'yankasuwa masu sayar da man da su bayar da hadin kai ta wannan fanni domin ganin al'ummar Najeriya sun amfana da sauƙin.
Kyrgyzstan ta haramta wa mata sanya niƙabi
Asalin hoton, AFP
Kyrgyzstan ta zama ƙasar da Musulmi suka fi rinjaye ta baya-bayan nan a yankin tsakiyar Asiya da ta haramta amfani da lilliɓin da mata ke rufe jikinsu gaba-daya - niƙabi.
Dokar da ta fara aiki tun daga jiya Asabar, ta tanadi hukuncin tarar dala 230 (kuɗin ƙasar som 20,000) a kan duk matar da ta sanya niqabin a wurin jama'a ko waje na gwamnati.
Gwamnatoci a ƙasashen tsakiyar Asia sun daɗe suna magana ko muhawara kan tufafin mata na Musulunci misali niqabi da kuma gemu ga maza, inda gwamnatocin da ke da tsananin aƙidar raba addini da harkar mulki suke tsoron tasirin Musulunci a ƙasashen.
'Yanmajalisar dokokin ƙasar ta Kyrgyzstan sun ce ana buƙatar dokar saboda dalilai na tsaro - ta yadda za a iya ganin fuskar mutum a kuma gane ko wace ce.
To amma kuma masu suka sun ce dokar ta tauye wa mata 'yancinsu na zaɓar tufafin da suke son sanyawa.
Dokar wadda Shugaba Sadyr Japarov ya sanya wa hannu ranar 21 ga watan Janairu da ya wuce, ba ta ambaci niqab ƙarara ba, amma ta ce duk tufar da za ta sa a kasa gane mutum (saboda ya rufe fuska) a wuraren gwamnati da taruwar jama'a.
Sai dai dokar ba ta shafi rufe fuska da ake bukata saboda yanayin aiki ko dalilai na lafiya ba.
'Yanmajalisar dokoki da kuma shugabannin addini da ke da alaƙa da gwamnati sun ce haramcin bai shafi hijabi ba - wanda ke rufe kai da wuya amma ana ganin fuska.
Kyrgyzstan ita ce kasa ɗaya kawai a yankin Asiya ta Tsakiya da ba ta harmta amfani da hijabi a makarantu da ofisoshi ba.
Amurka ta ƙaddamar da hare-hare kan ISIS a Somalia
Asalin hoton, US Africa Command
Shugaban Amurka Donald Trump ya bayar da umarnin ƙaddamar da hare-hare ta sama kan ƙungiyar ISIS a Somalia.
Mista Trump ya ce an kashe da dama daga mayaƙan ƙungiyar a harin, wanda ya kuma lalata wuraren da mayaƙan ke ɓuya.
Shugaban ya ƙara da cewa hare-haren sun nuna aniyar Amurka ta gano tare da kashe duk wanda ke yi wa Amurkawa barazana.
Ƙungiyar ISIS na ɗaya daga cikin manyan ƙungiyoyi masu iƙirarin jihadi da suka ɓulla a 2010, amma a yanzu ƙungiyar ta taƙaita ayyukanta ne a wasu yankunan Afirka.
Amurka ta sha ƙaddamar da hare-hare a Somaliaa, musamman a shekarar da ta gabata da nufin kakkaɓe masu iƙirarin jihadi.
Kanada ta ce za ta mayar wa Amurka martanin ƙarin haraji
Asalin hoton, Reuters
Firaministan Kanada Justin Trudeau ya ce ƙasarsa za ta ɗauki irin matakin da Amurka ta ɗauka na ƙaƙaba harajin kashi 25 cikin ɗari kan kayan Amurka.
Mista Trudeau ya ce abin da zai fi zamar wa Amurka alheri shi ne ta haɗa ƙarfi da Kanada ba wai ta wofintar da ita ba.
Ya ce a yau ina sanar da ku cewa Kanada ta dauki matakin mayar da martani na kashi ashirin cikin dari na kayan biliyoyin daloli da ake shigowa da su daga Amurka.
Ita ma Mexico ta bayyana cewa za ta ɗauki mataki, yayin da ita kuwa China ta yi barazanar ɗaukar matakin shari'a kan Amurkar.
Wannan ya biyo bayan ƙarin kashi 25 cikin ɗari da Shugaban Amurka Donald Trump ya yi ne a kan kayan da ƙasashen uku ke shigarwa Amurka, inda China har ma da ƙarin kashi 10 cikin ɗari ya ƙara lafta mata.
Sama da mutum 14 sun mutu a ramin haƙar zinare a Mali
Asalin hoton, AP
Aƙalla mutum goma sha uku ne yawancinsu mata da ƙananan yara suka rasu a gabas maso yammacin Mali sakamakon ruwa da ya mamaye ramin da suke haƙar zinari a cikinsa.
Masu haƙar zinarin na kalen ragowar zinarin da ya rage a kusa da ƙauyen Danga inda wata cibiyar ruwa ta bude tare da cika ramin da ruwa da laka.
Mali na ɗaya daga cikin ƙasashen Afirka da ke samar da zinari, inda kuma ake yawan samun haɗari a wuraren da ake haƙar zinarin ba bisa ƙa'ida ba.
Ko a watan Janairu na bara wajen mutum 70 ne suka mutu lokacin da ramin da suke haƙar zinare ya rufa a yankin kudu maso yammacin ƙasar.
Majalisar Wakilai ta roƙi NLC ta fasa yajin aiki kan ƙarin kuɗin waya
Asalin hoton, NLC
Kwamitin majakisar wakilan Najeriya da
ke kula da harkokin sadarwa ya roki shugabannin kungiyar kwadago ta kasar ta
NLC, da su fasa shiga yajin aikin kasa baki daya da suka shirya yi daga ranar
Talata 4 ga watan nan nan Fabarairu 2025 saboda karin kashi 50 cikin dari na
kudin kiran waya da intanet.
A kwanan nan ne hukumar sadarwa ta kasar
ta amince da bukatar kamfanonin sadarwa ta kara kudin sadarwa da kashi 50 cikin
dari saboda dalilai na karuwar kudin gudanar da harkokin kamfanonin.
Dangane da karin ne kungiyar ta NLC ta
lashi takobin shiga yajin aikin kassa baki daya, tana mai kira ga gwamnatin
tarayya da majalisun dokoki na tarayya su koma ga tsohon farashin.
Kungiyar ta ce yajin aikin zai zama
gargadi ga gwamnati kan hadarin irin wannan karin a kan al'ummar da ke fama da
tsadar rayuwa - wadda mafi kankantar albashinta shi ne naira 70,000.
Baya ga karin kudin fetur da abinci da
wutar lantarki da kuma sauran wahalhalu da al'ummar ke fama da su, in ji
kungiyar kwadagon.
Ni ban iya munafurci ba - El-Rufai
Asalin hoton, OTHERS
Tsohon gwamnan jihar Kaduna Mallam Nasir El-Rufai, ya ce shi ba irin 'yansiyasar nan ba ne da ke munafurci da yaudara da karya ba, yana mai kwatanta 'yansiyasar da ke haka da 'yan fim din Najeriya.
El-Rufai ya bayyana hakan ne yayin da yake mayar da magana kan wani da ya yi rubutu a shafin X, Ira Habib inda ya koda shi bayan da ya ce ya karanta littafinsa ‘Accidental Public Servant,’
Habib ya rubuta cewa,''...lalle ba dansiyasar da zai so ya yi aiki da El-Rufai a majalisar ministocinsa sai dai in har da gaske yake yana son ya raya kasarsa nan. Bai iya munafurci ba.'' Kamar yadda mutumin ya rubuta a shafinsa na X.
A kan hakan ne El-Rufain ya jaddada maganar da Habib din ya rubuta cewa bai iya yaudara da karya ba - yana mai kwatanta 'yansiyasar da ke haka da 'yan fim din Najeriya na Nollywood.
Tsohon gwamnan na Kaduna ya bayyana hakan ne kuwa 'yan kwanaki bayan da aka ruwaito shi yana cewa idan da yana cikin gwamnatin Tinubu ba zai sauya matsayinsa ba a kan yadda yake faden gaskiya a kan gwamnatin ba.
Rasha ta kai harin bam a makaranta - Zelensky
Asalin hoton, Getty Images
Shugaba Volodymyr Zelensky na Ukraine ya ce Rasha ta kai harin bama-bamai a wata makarantar kwana da 'yan gudun hijira suka fake a yankin Rashar da Ukraine ta kama.
Ya ce ana shirin kwashe mutanen ne wadanda farar hula ne, kafin Rasha ta kai harin.
Sojojin Ukraine sun ce mutum hudu sun mutu kuma gommai yawanci tsofaffi sun ji raunia garin Sudzha da ke yankin Kurskwanda ke karkashin ikon Ukraine tsawon wata biyar.
Rahotanni sun ce an ceto mutum sama da tamanin daga ginin.
Sai dai BBC ba ta iya tabbatar da ikirarin Ukraine na cewa da gangan Rasha ta kai harin ba.
Rasha ta dora alhakin harin a kan Ukraine.
Buɗewa
Jama'a masu bibiyarmu a wannan shafin da ke
kawo muku labaran abubuwan da ke wakana a Najeriya da sauran sassan duniya kai
tsaye, muna muku maraba a wannan safiya ta Lahadi 02 ga watan Fabarairun 2025
Ni Muhammad Annur Muhammad da Abdullahi BelloDiginza za mu
kasance da ku daga yanzu zuwa wani lokaci a nan gaba.
Za kuma ku iya leƙawa
shafukanmu da sada zumunta domin karanta wasu labaran da kallon hotuna da
bidiyo.
Ku kasance tare da mu.
Mu fara
da wannan karin maganar da ke cewa - Sauro ba ya gasa da iska