Ya za ta kaya tsakanin Arsenal da Man City a Premier League?

Asalin hoton, Getty Images
Arsenal za ta karɓi bakuncin Manchester City a wasan mako na 24 a Premier League da za su kara ranar Lahadi a Emirates.
Gunners tana mataki na biyu a teburi da maki 47 da tazarar maki shida tsakani da City ta huɗun teburin Premier League a kakar nan.
Ƙungiyoyin biyu sun tashi 2-2 a wasan farko a kakar nan ranar 22 ga watan Satumba a Etihad.
Erling Haaland ne ya fara ci wa City ƙwallo a minti na tara da take leda, daga baya Gunners ta farke ta hannun Riccardo Calafiori, sannan Gabriel Magalhaes ya ci na biyu.
Daf da za a tashi a wasan na hamayya ne City ta farke ta hannun John Stones, hakan ya sa suka raba maki a tsakaninsu.
A karawar ce Rodri ya ji raunin da yake jinya har ƙarshe kakar nan, wanda ake ganin jinyar tasa ce ta janyo wa City koma-baya a wasannin da take yi a kakar nan.
Karin bayani kan lafiyar ƴan wasa

Asalin hoton, Getty Images
Arsenal tana auna ƙoshin lafiyar mai tsaron raga, David Raya, wanda bai yi karawar Champions League ba a wasa da Girona ranar Laraba.
Myles Lewis-Skelly zai buga wasan, bayan soke jan katin da aka yi masa a wasan Wolverhampton, sai dai Ben White da Takehiro Tomiyasu da Bukayo Saka da kuma Gabriel Jesus na ci gaba da jinya.
Kociyan Manchester City, Pep Guardiola ya ce baya da sabbin ƴan wasan da suka ji rauni a yanzu haka.
Ana sa ran waɗanda ya ɗauka a Janairu da ya haɗa da Omar Marmoush da Abdukodir Khusanov da Vitor Reis su buga wasan, bayan da ba sa cikin karawar da City ta doke Club Brugge a Champions League ranar Laraba - shi kuwa Oscar Bobb ya murmure.
Sai dai har yanzu Ruben Dias da Nathan Ake da Jeremy Doku da kuma Rodri na ci gaba da jinya.
Abinda ya kamata ku sani kan wasa tsakanin ƙungiyoyin biyu

Asalin hoton, Getty Images
Manchester City ta doke Arsenal wasa 12 a jere tsakanin 2017 zuwa 2023, sai dai ta kasa nasara a karawa uku bayan nan, ta yi canjaras biyu aka doke ta wasa ɗaya.
Arsenal na fatan doke City a gida karo biyu a jere a karon farko tun bayan nasara huɗu tsakanin Oktoban 2005 zuwa Afirilun 2009.
Arsenal

Asalin hoton, Getty Images
Wataƙila Arsenal ta tsawaita cin wasa na 14 a Premier League ba tare da rashin nasara ba ranar Lahadi, zai zama ƙwazo mafi kyau ƙarƙashin Mikel Arteta.
Gunners ta yi wasa 14 ba tare da rashin nasara ba a tarihi a Premier League tsakanin Agusta zuwa Disambar 2018 ƙarƙashin Unai Emery.
Arsenal ta ci ƙwallo 12 daga kwana da bugun tazara a bana, ta kuma ci ƙwallo biyar a hakan daga 10 da ta zura a ragar City.
An bai wa Gunners jan kati 19 tun bayan da Mikel Arteta ya karɓi aiki a cikin Disambar 2019.
Sun ci wasa 38 lokacin da aka kori ɗan wasan Gunners, an yi nasara 35 a kan Gunners a wasan da aka bai wa ɗan wasanta jan kati.
Manchester City

Asalin hoton, Getty Images
City na fatan cin wasa biyu a jere a karawar waje, rabon da ta yi hakan tun cikin watan Agustan 2024.
Mai riƙe da kofin Premier League ta ci ƙwallo 18 tun daga Disamba, ta yi wasa shida ba tare da rashin nasara ba da cin huɗu daga ciki.
Ta samu maki 17 daga wasan da ya kamata a doke ta a Premier League a kakar nan.
Wasa biyar daga 12 da ta yi nasara, ita ake fara cin ƙwallo daga baya ta farke.
Ƙwallo biyu ne ya shiga ragar City a ko dai bugun kwana ko tazara.










