Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Gasar kofin duniya 2026: An raba maki tsakanin Brazil da Moroko
Takaitaccen Bayanin Wasa
Key Events
Brazil
- Vinícius Júnior Goal 32 minutes
Moroko
- I. Saibari Goal 21 minutes
Taƙaitattu
- Brazil za ta fafata da Morocco a rukuni na uku a gasar cin kofin duniya
- Wannan shi ne karo na 23 da Brazil ke zuwa kofin duniya mai biyar jimilla
- Morocco za ta buga gasar kofin duniya na bakwai, ta kai daf da karshe a 2022
- Abin da ya kamata ku sani kan Gasar Kofin Duniya ta 2026
- Za a buga wasan ne a filin MetLife da ke New Jersey a birnin New York
- Za ku iya tafka muhara a shafnmu na sada zumunta a BBC Hausa Facebook
- Scotland da Haiti suma suna cikin rukunin na uku a gasar kofin duniya 2026
- Kasa 10 ce daga Afirka da za su buga gasar kofin duniya a bana
- Ku shiga zaurenmu na BBC Hausa WhatsApp
Rahoto kai-tsaye
Mai gabatarwa Mohammed Abdu da taimakon AI
Fili ya cika da ƴan kallo, domin wannan shi ne ɗaya daga wasan da ake sa ran za a murza leda.
Yan wasa na cikin fili ana daf da kara karawar.
Yanzu kuma an shiga taken Moroko, wadda ake fatan ko za ta kai zagayen karshe a bana, bayan da ta kai matakin daf da karshe a Qatar a 2022.
Yanzu haka ita take rike da kofin nahiyar Afirka, gasar da ta gudanar a 2025, wadda ta ci karo da takaddama.
Senegal ce ta lashe kofin daga baya aka bai wa Moroko, sakamakon karar da ta shiga ga hukumar ƙwallon kafa ta Afirka.
Yanzu haka ana taken kasar Brazil, wadda ake sa ran za ta taka rawar gani mai fitatcen koci, Carlo Ancelotti, wanda ya yi bajinta a ƙungiyoyi da dama a Turai
Karon farko da zai ja ragamar kasa a gasar cin kofin duniya a tarihi.
Morocco ta taka mataki mafi girma a gasar kofin duniya, Brazil da Morocco
Morocco a halin yanzu tana matsayi na bakwai a jerin jadawalin FIFA a taka leda a duniya, kuma ta kai wasan daf da karshe a gasar cin kofin duniya ta 2022 a Qatar, inda ta sha kashi a hannun Faransa.
Wa zai yi nasara a wasan nan? Za ku iya kada zabe
Wasan farko daga rukuni na uku a gasar kofin duniya 2026, Brazil da Morocco
Wannan shi ne wasa ɗaya daga matakin rukuni da kasashen biyu ke cikin ƴan 10 farko a jadawalin tawagogin da suke kan gaba a iya taka leda a duniya wato FIFA World Rankings yayin da Brazil ke matsayi na shida, ita kuwa Morocco tana mataki na bakwai.
Wannan ya sa karawar za ta yi zafi, watakila karfi ya zo ɗaya.
Sauran kasashe biyu a rukunin na uku, Haiti da Scotland, za su buga wasansu ranar Lahadi.
Jerin ƴan 10 farko a jadawalin FIFA...
- Ajentina
- Sifaniya
- Faransa
- Ingila
- Focugal
- Birazil
- Maroko
- Nezalan
- Baljiyom
- Jamus
Lokaci ya yi da katafaren filin wasa da ke New Jersy ya haska, Brazil v Morocco
Neil Johnston, BBC Sport a filin wasa na New Jersey New York
Lokaci ya yi da filin wasa na New Jersey zai haskaka a gasar cin kofin duniya.
A wannan filin za a buga wasan karshe ranar 19 ga watan Yulin 2026.
Gasar kofin duniya 2026: Abin da kuke son sani kan wasan Brazil da Morocco
Brazil, wadda ta lashe kofin duniya sau biyar, za ta kara da mai rike da kofin nahiyar Afirka, Morocco a ɗaya daga cikin wasannin da zai ja hankali a matakin rukuni a gasar cin Kofin Duniya ta 2026.
Kuma BBC Hausa za ta kawo muku wasan kai-tsaye a shafinmu na bbchausa.com
Wannan shi ne wasan farko da za a kara ranar Asabar a rukuni na uku da ya haɗa har da Haiti da kuma Scotland, waɗanda sai a ranar Lahadi za su buga nasu wasan.
Brazil, wadda yanzu ke karkashin jagorancin shahararren koci, Carlo Ancelotti na fatan taka rawar gani a wannan gasa da ake yi a Amurka da Kanada da kuma Mexico.
Brazil ɗin za ta fuskanci kalubale a wajen Morocco, wadda ta kafa tarihin zama ta farko daga Afirka da ta kai matakin daf da karshe a gasar duniya da aka yi a Qatar a 2022.
Bayani kan ƴan wasan da za a fara wasan farko a rukuni na uku, Brazil da Morocco
Kocin Brazil, Carlo Ancelotti ya bai wa dan wasan Brentford, Igor Thiago damar fara buga gasar cin kofin duniya da za a yi a daren nan.
Mai shekara 24 zai fara wasan tare da Raphinha da Vinicius Jr, yayin da tsohon dan wasan, Neymar yana jinya da ƙyar ne idan zai buga karawar cikin rukuni.
Ƴan wasan Brazil 11:
Alisson, Ibanez, Marquinhos, Gabriel, Santos; Casemiro, Paqueta, Guimaraes; Raphina, Vinicius Jr, Thiago.
Ƴan benchi: Weverton, Ederson, Alex Sandro, Danilo, Bremer, Pereira, Silva, Fabinho, Santos, Cunha, Endrick, Henrqiue, Martinelli, Rayan.
A ɗaya bangaren kuwa ɗan wasan Real Madrid, Brahim Diaz da mai tsaron baya na Paris St-Germain Achraf Hakimi, suna daga cikin ƴan wasa 11 da kociya Mohamed Ouahbi ya sanar da za su fuskanci Brazil.
Ƴan wasan Moroko: Bounou, Hakimi, Riad, Diop, Mazraoui; Bouaddi, El Aynaou; Diaz, El Khannouss; Saibari.
Ƴan benci: El Kajoui, Tagnaouti, Saadane, El Ouahdi, Belammari, Halhal, Salah Eddine, Amrabat, Talbi, El Mourabet, Yassine, Rahimi, Sbai, El Kaabi, Amaimouni.
Ko Brazil za ta iya sake ɗaukar kofin duniya a Amurka?, Gasar cin kofin duniya
Koda yaushe masu bibiyar tamaula na son kallon wasannin tawagar Brazil, musamman a gasar cin kofin duniya
Tana da shi biyar jimilla, kuma ita ce ta ɗauki wanda Amurka ta gudanar a 1994.
Barkanmu da shiga fagen labarin wasanni
Jama'a barkanmu da kasancewa a wannan lokacin da za mu kawo muku kai tsaye a wasan gasar kofin duniya tsakanin Brazil da Moroko a wasan farko a rukuni na uku..
Sunana Mohammed Abdu zan gabatar muku da shirin tare da taimakon AI, za ku iya tafka muhawara a BBC Hausa Facebook ko kuma ku bibiyi labaran da muke wallafawa a BBC Hausa WhatsApp.

