Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 13/12/2024

Wannan shafi ne da ke kawo labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 13/12/2024

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Haruna Ibrahim Kakangi, Abdullahi Bello Diginza da Badamasi Abdulkadir Muktar

  1. 'Jihohin Najeriya sun nuna goyon bayan kafa 'yansadan jihohi'

    'Yansanda

    Asalin hoton, Getty Images

    Majalisar tattalin arzikin Najeriya (NEC) ta karɓi rahotonnin matsayar gwamnonin jihohin ƙasar 36 kan kafa rundunonin 'yansandan jihohi.

    Majalisar tattalin arzikin ƙarƙashin jagorancin mataimakin shugaban ƙasa, ta yi zamanta a jiya Alhamis a fadar gwamnatin ƙasar da ke Abuja, inda gwamnoni da mataimakan wasu gwamnonin suka halarta tare da wasu masu bai wa shugaban ƙasa shawara.

    Yayin da yake jawabi ga manema labarai a fadar gwamnatin jim kaɗan bayan kammala ganawar, gwamnan jihar Kaduna Uba Sani ya ce gwamnonin jihohin sun nuna cikakken goyon bayansu kan ƙirƙirar 'yansandan jihohi saboda matsalolin tsaro da jihohin ke fama da su.

    “Tabbas kowace jiha na da irin nata matsalolin da suka shafi tsaro, kuma da dama sun amince da kafa rundunonin 'yansandan jihohi a matsayin mafita kan matsalolin,'' in ji gwamnan na Kaduna.

    To sai da majalisar ta dakatar da tattaunawa game da batun har sai a zamanta na gaba da za a yi cikin watan Janairun sabuwar shekara mai kamawa.

  2. Ya kamata tunanin Nato ya koma na yaƙi - Shugaban ƙungiyar

    Hoton shugaban Nato

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Shugaban ƙungiyar tsaro ta Nato, Mark Rutte

    Shugaban ƙungiyar tsaro ta NATO, Mark Rutte ya ce lokaci ya yi da ya kamata tunanin ƙungiyar ya koma na yaƙi.

    Mista Rutte ya kuma yi gargaɗin cewa mambobin ƙawancen tsaron ba sa kashe kuɗaɗen da suka kamata don shiryawa barazanar rikici da Rasha.

    A cikin wani muhimmin jawabinsa na farko tun bayan zama Sakatare Janar na ƙungiyar a watan Oktoba, Mista Rutte ya ce Moscow na shiryawa domin yaƙi da Ukraine da kuma NATO.

    Ya ce ''idan kuna tunanin ya kamata a kiyaye tsarin rayuwarmu da dimokuradiyya da ɗabi'unmu, to dole ne mu ba da fifiko kan tsaro. Kuma idan ba mu yi haka ba nan da shekaru huɗu ko biyar za mu fuskanci manyan matsaloli''.

  3. Macron zai naɗa sabon firaministan Faransa

    Macron

    Asalin hoton, EPA

    Ofishin shugaban ƙasa a Faransa ya ce Emmanuel Macron zai naɗa sabon firaminista nan da sa'o'i masu zuwa, bayan rugujewar gwamnatinsa a makon jiya.

    Da farko Mista Macron ya ce zai bayyana sabon Firaministan ne a jiya Alhamis.

    Yana fuskantar matsin lamba wajen zaɓar sabon firaministan wanda zai yi ƙoƙarin haɗa kan gamayyar kawancen jam'iyyu tare da zartar da kasafin kuɗin shekara mai zuwa.

    Rahotanni sun ce abokin tarayyar Mista Macron, Francois Bayrou, da kuma tsohon ministan harkokin wajen Jean-Yves Le Drian na daga cikin waɗanda za su iya maye gurbin Michel Barnier a matsayin Firaminista.

  4. Assalamu alaikum

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da safiyar wannan ranar ta Juma'a, Haji babbar rana kamar yadda Hausawa ke yi mata kirari.

    Muna fatan sake kasancewa da ku a daidai wannan lokaci domin kawo muku irin wainar da ake toyawa a faɗin duniya.

    Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa.