Mu kwana lafiya
Ƙarshen rahotonni kenan a wannan shafi.
Za ku iya karanta labaran da muka kawo muku a yau idan kuka yi ƙasa.
Umar Mikail ke muku fatan alheri.
Wannan shafi ne da ke muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, 02/08/2025
Isiyaku Muhammed da Umar Mikail
Ƙarshen rahotonni kenan a wannan shafi.
Za ku iya karanta labaran da muka kawo muku a yau idan kuka yi ƙasa.
Umar Mikail ke muku fatan alheri.

Asalin hoton, EPA
Wata kotu a kudancin Indiya ta yanke wa wani fitaccen ɗansiyasa a jihar Karnataka hukuncin ɗaurin rai da rai saboda yi wa ɗaya daga cikin masu yi masa aiki a gida fyaɗe.
An yanke wa Prajwal Revanna hukuncin, wanda ya fito daga sanannen gida a jihar, kwana guda bayan da aka same shi da laifin cin zarafin wata tsohuwar mai aikinsa mai shekara 48.
A cewar wakilin BBC, Revanna ya fashe da kuka inda ya roƙi kotu ta yi masa sassauci bayan an same shi da laifin a jiya Juma'a.
Kotun ta umarce shi ya biya fiye da dala 9,000 a matsayin diyya ga matar.
Ƴansiyasa a Rasha sun yi watsi da sanarwar da Shugaba Donald Trump ya yi cewa zai girke jiragen ruwa na nukiliya kusa da Rasha.
Ɗaya daga cikin ƴanmajalisar Rasha ya ce jiragen ruwan biyu na Amurka da ake magana a kai, tuni Rashar take sanya masu ido sannan kuma babu buƙatar mayar da martani.
A jiya Juma'a ne Trump ya ce sake tura jiragen ya faru ne sakamakon kalaman da tsohon Shugaban Rasha Dmitry Medvedev ya yi a shafukan sada zumunta.
Mista Medvedev ya bayyana barazanar Amurka ta ƙara ƙaƙaba wa Rasha takunkumi a matsayin mataki na shiga yaƙi.

Asalin hoton, EPA
Hamas ta sake jaddada cewa ba za ta ajiye makamanta ba har sai an samar da ƙasar Falasɗinawa mai ƴancin kanta.
Cikin wata sanarwa, ƙungiyar ta ce za ta ajiye makamanta ne kawai idan aka tabbatar wa Falasɗinawa cikakken ƴancinsu.
A ƴan kwanakin da suka gabata, ƙasashen Larabawa sun buƙaci Hamas ta ajiye makamanta tare da miƙa ikon Gaza bayan da ƙasashen Yamma da dama sun yi alƙawarin amincewa da ƙasar Falasɗinawa.
Cikin ƙasashen da suka bayyana shirin amincewa da ƙasar Falasɗinu har da Faransa da Birtaniya da Canada.

Asalin hoton, Getty Images
Babbar ƙungiyar ma'aikatan jinya da ungozoma a Najeriya ta sanar da janye yajin aiki na kwana bakwai da ta fara yi bayan cimma matsaya da gwamnatin tarayya.
Sun fara yajin ne a ranar Laraba bayan sun zargi gwamnatin ƙasar da kasa cika alƙawarin ƙara musu albashi da alawus-alawus, da ƙara yawan ma'aikata, da inganta wuraren aiki.
Shugaban ƙungiyar ta National Association of Nigeria Nurses and Midwives (NANNM), Haruna Mamman, ya shaida wa BBC cewa gwamnati ta bayar da umarnin cika akasarin buƙatun nasu.
"Saboda yarjejeniyar da muka cimma da kuma nuna jajircewarmu, mun jingine yajin aikin da muke yi na ƙasa baki ɗaya nan take," in ji shi cikin wata sanarwa daban a yau Asabar.
A jiya Juma'a Ministan Lafiya na Najeriya Muhammed Ali Pate ya ce ƙungiyar ta amince da janye yajin aikin bayan yarjejeniyar da suka ƙulla.
Sanarwar ta nemi 'ya'yan ƙungiyar su koma bakin aikinsu nan take.

Asalin hoton, Reuters
Jam'iyyar Democrat a Amurka da masana tattalin arziki sun yi Allah wadai da matakin Shugaba Donald Trump na korar shugabar hukumar ƙididdigar alƙaluman bunƙasar ayyuka ta ƙasar.
Trump ya kori Erika McEntarfer sa'o'i bayan fitar da rahotan fuskantar koma-baya a samar da ayyukan yi a ƙasar, inda ya zarge ta da jirkita alƙaluman "domin ɓata masa suna".
A wata sanarwar da tsofaffin shugabannin hukumar biyu suka fitar, sun ce babu hujjar wannnan kora kuma hakan barazana ce ga yardar da ake da ita kan alƙaluman gwamnati.
Jigo a jam'iyyar Democrats a majalisar dattijai, Chuck Schumer, ya ce shugaban ba ya son gaskiya.
Ya ce "a wasu lokutan Donald Trump na ƙaunar masu mulkin kama-karya, kuma a wasu lokutan ma halayensu yake nunawa".

Asalin hoton, Muhammad Idris Malagi
Ministan yaɗa labarai da wayar da kan al'umma na Najeriya, Muhammad Idris Malagi ya buƙaci kowane ɓangare ya mayar da kubensa kan batun rufe gidan rediyon Badegi FM da ke birnin Minna a jihar Neja.
Ministan ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Rabiu Ibrahim ya fitar, inda a ciki ya ce hukumar kafafen watsa labarai ta Najeriya wato NBC na da hanyoyin shiga tsakani idan aka samu irin wannan matsalar.
Rahotanni sun nuna cewa Gwamnan jihar Neja, Umaru Bago ya bayar da umarnin rufe gidan rediyon ne a lokacin taron masu ruwa da tsaki na jam'iyyar APC na jihar a ranar 1 ga watan Agusta.
Gwamnan ya zargi gidan rediyon ya karya dokokin watsa labarai, da kuma tunzura mutane a kan gwamnatin jihar.
"Duk da cewa mun fahimci abin da gwamnatin ke zargi, ma'aikatar watsa labarai na so a fahimci cewa Hukumar NBC ce ke da hurumin dakatar da lasisin gidan rediyo Gwamnatin Neja ba, kamar doka ta tanada.
"Don haka ne ma'aikatar ke kira ga gwamnatin jihar Neja da ta kai ƙorafinta ga NBC kan gidan rediyon NBC bisa zargin "karya doka" da take yi wa gidan rediyon."
A ƙarshe ministan ya yi kira da a bi lamarin a hankali, inda ya tabbatar da cewa NBC za ta yi aikin da ya dace domin tabbatar da sasanci kan lamarin.

Asalin hoton, Amnesty International
Ƙungiyar Amnesty International ta yi Allah-wadai da sakacin da ta ce gwamnatin Najeriya na yi kan ɓacewar matashin ɗan gwagwarmaya, Abubakar Idris Dadiyata.
Amnesty International ta bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da ta raba wa manema labarai, inda ta ce tana mamakin yadda aka yi shekara shida ba tare da sanin halin da yake ciki ba.
Dadiyata ya ɓace ne a ranar 2 ga watan Agustan shekarar 2019, bayan wasu mutane ɗauke da makamai sun kutsa gidansa da ke unguwar Barnawa a Kaduna jim kaɗan bayan ya koma, suka suka tafi da shi.
"Tun lokacin ne iyalansa suke ta da jiran komawarsa, amma har yanzu da ya cika shekara shida babu bayani."
Shugaban ƙungiyar a Najeriya, Isa Sanusi ya ce shi kansa ya san Dadiyata a matsayin jajirtacce mai girmama na gaba.
"Mutane da dama, ciki har da Amnesty International na tunanin cewa ɓacewar Dadiyata na da alaƙa da sukar gwamnati da wasu ƴansiyasa a kafofin sadarwa da yake yi ba."
Amnesty ta ce duk da gwamnati ta ce ba ta da hannu a ɓacewarsa, "duk da haka dole a zargi gwamnati. Kuma bayan haka, haƙƙin gwamnati ne ta rufe duk wasu ƙoƙofin zargi game da ɓacewar matashin ta hanyar ganowa da bayyana asalin abin da ya faru da Dadiyata domin sauƙaƙa ƙuncin da iyalansa da ƴanuwansa da abokan arziki suke ciki.
Amnesty ta ce akwai buƙatar jami'an tsaron Najeriya su ƙara ƙaimi wajen bincike domin gano asalin abin da ya faru, tare da bayyana abin da suka gano, "abin mamaki ne a ce shekara shida an kasa samu tabbataccen bayani. Tilas shugaban Najeriya Bola Tinubu ya sa baki a kan batun ɓacewar Dadiyata."
"Don haka muna Allah-wadai da rashin kula da gwamnatin Najeriya take ba batun ɓacewar Dadiyata, kuma lokaci na ƙara ƙurewa. Ƴan'uwa da iyalan Dadiyata na neman amsar tambayar: ina Dadiyata yake?"
Daga cikin waɗanda suka halarci taron akwai matarsa, Khadija Lame da ƙaninsar Usman Idris.

Asalin hoton, TWITTER/ DADIYATA

Asalin hoton, Reuters
Wasu muhimman tsare-tsare na dokokin Tarayyar Turai kan amfani da fasahar ƙirƙirariyar basira ta AI sun soma aiki daga yau, kuma hakan zai shafi yadda ake amfani da manhajoji AI, irinsu ChatGPT.
Waɗannan tsare-tsare wanda kusan su ne dokokin farko kan amfani da AI an samar da su ne domin shawo kan barazana ko matsalolin haƙƙin mallaka.
Kamfanonin da suka amince su riƙa amfani da manhajoji AI a yanzu dole su riƙ bibbiyar yadda manhajoji ke aiki, da kuma sanar da mutane.
Wakilin BBC ya ce, Kamfanin Meta, mallakin Facebook da Instagram da WhatsApp zuwa yanzu dai bai amince da sabbin dokokin Tarayyar Turan ba.

Asalin hoton, Getty Images
Jami'ai a Malawi sun ce ƙasar ta yi nasarar cimma muradan Majalisar Ɗinkin Duniya wajen yaƙi da cutar HIV/AIDS.
Ƙasar dai ta kasance ɗaya daga cikin waɗanda suka fi yawan masu cutar, inda mutum ɗaya daga cikin ko wane mutane bakwai ke ɗauke da ƙwayar cutar HIV a shekarun 1990.
Amma yanzu jami'an sun ce wannan adadin ya ragu zuwa rabi.

Asalin hoton, INEC Nigeria
Hukumar zaɓe mai zaman kanta, INEC ta sanar da shirinta na fara rajistar masu zaɓe a Najeriya, wadda hukumar ta ce za a fara daga ranar 18 ga watan Agustan wannan shekara ta 2025.
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da hukumar ta wallafa a shafinta na X a jiya Juma'a.
Ta ce za a buɗe rajistar ne a shafin hukumar a ranar 18, sannan mutane za su fara zuwa cibiyoyin rajistar da hukumar ta tanada daga ranar 25 ga watan na Agusta.
Ta ƙara da cewa za a riƙa zuwa rajistar ne a ofisoshin ƙnananan hukumomin da sauran cibiyoyin hukumar ke faɗin ƙasar.

Asalin hoton, EPA/KCNA
Wani ɗan Koriya ta Arewa da ya yanke alaƙa da ƙasar, ya shaida wa BBC yadda ya kasance cikin wata ƙungiya da ke ayyuka a asirce wajen samar da kuɗaɗe ta haramtacciyar hanya ƙarƙashin mulkin kama-karya na Shugaba Kim Jong-Un.
A wata tattaunawa da ba kasafai aka saba ji ba, Jin-Su wanda ba sunansa na asali ba ne ke nan - ya ce yana amfani da takardun bogi wajen neman aiki a manyan kamfanonin fasaha a Amurka da Turai.
Ya ce a kowanne wata yana samun dala dubu biyar, amma kaso mai yawa na kuɗin Koriya ta Arewa ya ke aikawa.
Jin-Su ya bayyana yada ya ke aiki cikin yanayi na wahala da sa ido daga tawaga ta musamman.
Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce irin waɗannan ayyuka na samar wa ƙasar dala miliyan 600 a kowacce shekara

Asalin hoton, Getty Images
An yanke wa tsohon shugaban Colombia, Alvaro Uribe, hukuncin ɗaurin talala na shekara 12 bayan samunsa da laifin lalata shaidu.
Mista Uribe wanda ya mulki ƙasar tsawon shekara 8 har zuwa 2010, ya ce zai ɗaukaka kara.
A shari'ar da aka shafe tsawon lokaci ana yi, an same shi da laifin haɗa kai da jami'ai masu tsatsauran ra'ayi a lokacin mulkinsa wajen cusgunawa mutane.
Ya yi fice wajen murƙushe 'yan tawayen FARC kuma yana da ƙarfin faɗa a ji a Colombia.

Asalin hoton, Reuters
Shugaba Trump ya ce, ya umarci a matsar da wasu jiragen ƙarƙashin teku masu ɗauke da makaman nukilliya guda biyu kusa da Rasha, a matsayin martani ga abin da ya kira "wauta da tsokana" kan kalaman da tsohon shugaban Rasha, Dmitry Medvedev ya yi.
Mutanen biyu sun jima suna sukar juna kai-tsaye a shafukan sada zumunta.
A saƙon da ya wallafa na baya-bayanan, Mista Medvedev ya ce barazanar da Amurka ke musu na tsaurara takunkumai saboda yaƙin Rasha da Ukraine takalar gagarumin yaƙi take yi.
Sai dai wakilin BBC ya ce, shugaba Trump na kaffa-kaffa wajen bayyana ko hakan na nufin zai yi amfani da makaman nukilliya.
A ranar Juma'a shugaba Putin ya nuna cewa babu wani abu da ya sauya kan sharuɗan na zaman lafiya da Ukraine.
Jama'a barkanmu da wanan safiya ta Asabar daga nan sashen Hausa na BBC, inda za mu kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya.
Ku garzaya shafukanmu n sadarwa irin su Facebok da X da Instagram da ma zaurenmu na Whatsap domin karanta wasu labara da ma tafka muhawara.
Ku kasance tare da ni, Isiyaku Muhammed, zuwa wani lokaci.