Rundunar IRGC ta bayyana Donald Trump a matsayin "maƙaryaci kuma mayaudari"

Asalin hoton, Getty Images
Kamfanin dillancin labarai na Fars da ke da alaƙa da dakarun juyin-juya hali na Iran ya wallafa maganar wani babban sojan ƙasar a shafinsa na Telegram.
Manjo Janar Abdullahi wanda ya rubuta saƙon da Farsi ya ce rundunar IRGC ta wahalar da Amurka da Isra'ila inda ta tilasta musu neman tsagaita wuta ido biyu.
Ya ƙara da cewa rundunar ba za ta bar "maƙaryaci kuma mayaudarin shugaban Amurka ya rinƙa ƙirƙirar labaran ƙarya dangane da haƙiƙanin abin da ke faruwa ba," musamman a kan batun mashigar Hormuz.


