Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 25/02/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Laraba 25 ga watan Fabrairun 2026.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Daga Aisha Babangida da Isiyaku Muhammad

  1. Wane ne zai gaji jagoran addinin Iran Ayatollah Khamenei?

    ....

    Asalin hoton, AP

    Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito cewa Iran na shirin sanar da "sabbin matakai" game da shirinta na nukiliya domin samun damar cimma yarjejeniya da Amurka.

    Matakin zai bayar da damar ɗage wa ƙasar takunkumai da kuma amincewa da shirinta na sarrafa makamashin nukiliya ƙarƙashin shirinta na zaman lafiya.

    Reuters ya ambato wani babban jami'in gwamnatin Iran na cewa ɓangarorin biyu sun sha bamban a wasu fannoni, ciki har da batun sassauta tsauraran takunkuman Amurka da ke kan ta.

    Wannan na zuwa ne yayin da Oman, ƙasar da ke shiga tsakanin ɓangarorin biyu, ta tabbatar cewa za a shiga zagaye na gaba na tattaunawar a birnin Geneva, ranar Alhamis.

  2. Ba zan bari Iran ta mallaki makamin nukiliya ba - Trump

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Amurka, Donald Trump ya bayyana cewa duk da hare-haren da Amurka ta kai kan cibiyoyin nukiliyar Iran a bara, har yanzu ƙasar na ci gaba da shirye-shiryenta na nukiliya.

    Trump ya ce gwamnatinsa ba ta samu wani tabbaci daga hukumomin Tehran da ke nuna cewa ba za su mallaki irin wannan makami ba.

    Ya ƙara da cewa burinsa shi ne a warware rikicin ta hanyar diflomasiyya, amma ya jaddada cewa ba zai taɓa bari abin da ya kira ƙasar da ta ke ta farko wajen daukar nauyin ta'addanci ta mallaki nukiliya ba.

    Haka kuma ya zargi mahukuntan Iran da kashe aƙalla mutum dubu 32 yayin zanga-zangar adawa da manufofin gwamnati.

  3. Da gaske ne gwamnatin Najeriya ta biya Boko Haram kuɗi don sakin ɗaliban Neja?

    ....

    Asalin hoton, Boko Haram

    Gwamnatin Najeriya ta yi martani kan zargin da wata kafar yaɗa labarai ta ƙasar waje ta yi cewa ƙasar ta biya Boko Haram ''maƙudan kuɗi'' a matsayin fansa tare da sakin wasu kwadamandojin ƙungiyar da ake tsare da su kafin sakin ɗaliban da ƙungiyar ta sace a jihar Neja.

    Rahoton kamfanin dillancin labarai na AFP, wanda BBC ba ta tabbatar da gaskiyarsa ba ya nuna cewa gwamnatin Najeriya ta biya kuɗaɗe masu yawa ga Boko Haram kafin ƙungiyar ta saki ɗaliban makarantar St Mary's Catholic Church da ke ƙauyen Papiri fiye da 260 da ke jihar Neja.

    Sai dai cikin wata sanarwa da ministan yaɗa labaran ƙasar ya fitar a ranar talata ya ce zargin ba shi da tushe balle makama.

    ''Gwamnati na jaddada cewa waɗannan zarge-zarge tsantar ƙarairayi ne marasa tushe, kuma an ƙirƙire su ne domin karya gwiwar ƙwarewar dakarunmu da ƙoƙari da sadaukarwar da suke yi ba dare ba rana'', a cewar sanarwar.

    Kamfanin dillancin labaran na AFP ya kafa hujja da wasu majiyoyi, waɗanda ya ce suna da masaniya kan batun biyan kuɗin.

  4. Assalamu alaikum

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da safiyar wannan rana ta Laraba.

    Kamar kullum, yau ma za mu kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Aisha Babangida ke fatan sake kasancewa da ku a daidai wannan lokaci.

    Za ku iya leƙawa shafukan sada zumuntanmu na intanet, da facebook da X da kuma whatsapp domin karanta sauran labarai da kallon bidiyo da tafka muhawara.