Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Litinin 01/12/2025

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Litinin 01/12/2025

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Isiyaku Muhammed da Aisha Babangida

  1. Ana zargin tsoffin shugabannin sojin Birtaniya da ɓoye shaidar aikata laifukan yaƙin a Afghanistan

    ...

    Ana zargin tsoffin shugabannin rundunar sojin Birtaniya ta musamman biyu da ɓoye shaidar aikata laifukan yaƙi.

    An gabatar da zargin ne a gaban wata kotun sauraron ƙararraki da suka shafi zarge-zargen haramtaccen kisan da rundunar ta musamman ta yi a Afghanistan.

    Wani rahoto da shirin BBC na Panorama ya yi akan zargin aikata laifukan yaƙi a Afghanistan ya janyo wannan tuhuma.

    Wani babban jami'i wanda ba a bayyana sunansa ba na ɗaya daga cikin manyan jami'an rundunar kuma ya shaida wa kotun cewa ya yi matukar shiga damuwa akan abin da ya ce zargin kisan babu gaira babu dalili da aka yi wa mutanen da basu ji basu gani ba ciki har da yara.

    Ya ce tsoffin shugabannin rundunar sun san da zarge zargen amma basu yi komai akai ba.

  2. Amurka na ƙokarin kawo ƙarshen yaƙin Rasha da Ukraine

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Babban jami'in Amurka da kuma wakilan Ukraine na tattaunawa a Florida, a yayin da gwamnatin Trump ke kokari wajen ganin an kawo karshen yakin da Rasha ke yi da Ukraine.

    Sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio, ya bayyana cewa Amurka na son cimma yarjejeniyar zaman lafiyar da zata tabbatar da cikakken 'yancin Ukraine.

    Shugaban ya ce yana son a dakatar da kisan da ake yi wa mutane kuma ya yi imani cewa Rasha ma na son ganin ta kawo ƙarshen hakan.

    Kazalika shugaba Trump ya tabbatar da cewa wakilinsa na musamman Steve Witkoff zai je Moscow a cikin makonnan don ci gaba da tattaunawar.

    Sabon jagoran tawagar Ukraine da suka je tattaunawar, Rustem Umerov, ya ce tattaunawar na da tsauri to amma kuma akwai ci gaba sosai, inda ya kara da cewa kasarsa na son a samu zaman lafiya mai dorewa.

  3. Buɗewa

    Jama'a barkanmu da wannan safiya ta Litinin daga sashen Hausa na BBC, inda za mu ɗaura daga inda muka tsaya a jiya Lahadi wajen kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Ku kasance tare da mu.