Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 16/07/2027

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Haruna Kakangi da Ahmad Bawage da Umaymah Sani Abdulmumin

  1. Wane giɓi rasuwar Muhammadu Buhari za ta samar a siyasar Najeriya?

    Muhammadu Buhari

    Asalin hoton, Getty Images

    Rasuwar tsohon shugaban Najeriya, Muhamamdu Buhari babu shakka ta samar da giɓi a siyasar Najeriya musamman a arewacin ƙasar.

    Masu fashin baƙi na ganin rasuwar tsohon shugaban ƙasar ka iya haifar da wani ƙokari daga ƴan siyasar arewacin ƙasar na maye gurbinsa musamman a daidai lokacin da zaɓen shugaban ƙasa na 2027 ke ƙara ƙaratowa.

    A yankin arewacin ƙasar an ayi wa Muhammadu Buhari ba kawai a matsayin ɗan siyasa ba har ma da kasancewarsa mahaɗa tsakanin talakawa da masu faɗa a ji.

    Mutum ne da yake da mabiya na ga-ni-kashe ni a yankunan karkara da biranen yankin arewacin Najeriya.

  2. Gwamnatin Nijar ta yi wa dokar kasafin kuɗin 2025 kwaskwarima, Daga Tchima Illa Issoufou

    Tchiani

    Asalin hoton, ORTN

    Shugaban ƙasar Jamhuriyar Nijar, Janar Abdourahamane Tiani, ya sanya hannu kan wata doka, da ta yi wa dokar kasafin kudin 2025 kwaskwarima, inda aka rage kwatankwacin kusan kashi tara da rabi cikin 100 na kasafin kuɗin da aka amince da shi a watan Disamban da ya gabata.

    Wannan dai na kunshe ne a cikin wata sanarwa da aka fitar a hukumance daga ofishin babban sakataren gwamnatin ƙasar.

    Sanarwar ta ƙara da cewa wasu abubuwa ne suka janyo zaftare wani kaso daga cikin kasafin kuɗi na shekara ta 2025.

    "An zaftare kasafin kuɗin daga CFA biliyan dubu uku zuwa CFA biliyan dubu 2,749," in ji sanarwar.

    Wani masani kan fannin tattalin arziki a ƙasar, Mohaman Chiroma ya ce gwamnatin ta yi haka ne saboda ta hango cewa ba za ta iya samun kuɗaɗen da take hankoron samu ba.

    Wannan dai na cikin alkawura da aka yi da asusun ba da lamuni na duniya IMF a lokacin wani bita da aka yi, in ji sanarwar da sakataren gwamnatin ƙasar ya fitar.

  3. 'Wasu muƙarraban Buhari sun ci amanar da ya ba su lokacin mulkinsa'

    Buhari

    Asalin hoton, Nigeria Presidency

    Wani tsohon ɗan majalisar wakilai, Dachung Bagos ya bayyana cewa wasu mutanen da marigayi tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya naɗa, sun ci amanar yardar da ya yi musu.

    Ya ce lamarin ya janyo taɓarɓarewar batun cin hanci da rashawa a lokacin mulkinsa.

    Bagos ya bayyana haka ne a cikin shirin siyasa na Politics Today na gidan talabijin na Channels ranar Talata, jim kaɗan bayan binne tsohon shugaban a garin mahaifarsa ta Daura.

    "Buhari ya naɗa mutane ne da ya yarda da su waɗanda kuma yake tsammanin za su taimaka mi shi lokacin mulki, amma suka ci amanarsa daga baya.

    "Buhari mutumin kirki ne kuma dattijo mai nagarta mai yaƙi da rashawa da son tabbatar da gaskiya - sai dai ba haka mutanen da ya naɗa suke ba, inda a yau za ka ga wasu da aka naɗa lokacin mulkinsa suna fama da shari'a kan zargin cin hanci," in ji tsohon ɗan majalisar wakilan.

  4. 'Birtaniya ta yaudare ni bayan sakin bayanan sirri na'

    Afghanistan

    Asalin hoton, EPA

    Wani ɗan ƙasar Afganistan da ya yi aiki tare da sojojin Birtaniya da ke yaki da kungiyar Taliban ya shaida wa BBC cewa yana tunanin gwamnatin Birtaniya ta yaudare shi bayan da aka fallasa bayanansa na sirri bisa kuskure.

    Yana daga cikin ƴan ƙasar Afghanistan kusan 20,000 waɗanda aka fallasa sunayensu da sauran bayanai, ciki har da adireshinsu, a wani lamari da ya auku shekara uku da suka gabata.

    Da yake magana a majalisar dokokin ƙasar, ministan tsaro na Birtaniya John Healey ya nemi afuwar waɗanda wannan lamarin ya shafa.

    "Wannan lamari ya auku ne shekara uku da suka gabata a karkashin gwamnatin da ta shuɗe amma yanzu a madadin gwamnatin Birtaniya ina neman afuwar duk waɗanda wannan abu ya shafa," in ji shi.

  5. Rasha ta kashe mutum biyu a wani hari a Ukraine

    Ukraine

    Asalin hoton, Getty Images

    Jiragen yaki marasa matuka na Rasha da makamai masu linzami sun kai hari a yankuna da dama na Ukraine da sanyin safiyar yau Laraba.

    An kashe mutum biyu a wani harin da jirgi mara matuki ya kai kusa da garin Kupiansk.

    A birnin Kharkhiv wanda shi ne birni na biyu mafi girma a Ukraine, an samu rahotannin aƙalla fashe-fashe 17 a wani hari da aka kwashe minti 20 ana yin sa.

    Gwamnan yankin ya ce mutane uku ne suka jikkata.

    Jiragen yaki da makamai masu linzami sun kuma lalata cibiyoyin samar da wutar lantarki da ruwan sha a yankin kudu maso gabashin ƙasar.

  6. Buɗewa

    Masu bibiyar mu barkan mu da safiyar Laraba.

    Ku kasance da mu a wannan shafi domin kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da kuma sauran sassan duniya.