Liverpool ta daina amfani da riga mai lamba 20 don tunawa da Jota
Liverpool ta ajiye riga mai lamba 20, domin tunawa da Diego Jota, wanda ya yi haɗarin mota ya mutu a Sifaniya, tare da ɗan uwansa, Andre Silva.
An cimma wannan matsaya ce, bayan da aka tuntuɓi matar Jota, Rute Cardoso da iayalansa, kenan riga mai lamba 20 ta zama mallakin Jota har abada a Liverpool.
Kenan ba a sake saka riga mai lamba 20 a Liverpool tun daga matasa da babbar ƙungiya da ta mata.
Jota ya koma Liverpool daga Wolverhampton a 2020, ya kuma ci wa ƙungiyar Anfield ƙwallo 65 a wasa 182 da ya buga mata.
Ya taka rawar da ta kai Liverpool ta ɗauki FA Cup da League Cup a 2022 - da na 2024 - da kuma Premier League a kakar da ta wuce.