Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Labaran wasannin BBC Hausa kai-tsaye na 12-18/07/2025

Wannan shafi ne da ke kawo muku muhimman abubuwan da ke faruwa a duniyar wasanni daga Asabar 12 zuwa18 ga watan Yulin 2025.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu da Muhammad Annur Muhammad

  1. WAFCON 2024: Najerya za ta fafata da Zambiya a matakin kwata fayinal

    A yau ne tawagar matan Najeriya za ta fafata da takwarta ta Zambiya a matakin kwata fayinal na cin Gasar Kofin Afirka ta Mata.

    Gasar - wadda ake gudanarwa a ƙasar Morocco - na ɗaukar hankalin masoya ƙwallon ƙafa.

    Najeriya ta kai matakin ne bayan ta yi ta farko a rukunin B, duk kuwa da canjarars da ta yi da Algeriya a wasan rukunin na ƙarshe.

    A nata ɓangare Zambiya ta ƙare a mataki na biyu a rukunin A, da maki bakwai bayan Morocco, wadda ta yi ta farko.

    Ita ma Zambiya ba a doketa ba a wasan rukuni, bayan da ta yi narasa biyu da canjaras guda.

  2. Man City ta ɗauki matashin ɗanwasan tsakiya Sverre Nypan

    Manchester City ta kammala ɗaukar ɗanwasan tsakiya Sverre Nypan daga Rosenborg kan fan miliyan 12.5.

    Matashin mai shekara 18 ya saka hannu kan yarjejeniyar sekara biyar, kuma magoya baya sun yi imanin kwalliya za ta biya kuɗin sabulu.

    Nypan ya buga wa ƙasarsa Norway wasanni a tawagaar matasa, ciki har da ta 'yan ƙasa da shekara 21, amma ana sa ran zai buga wasannin aro a wata ƙungiya a kaka mai zuwa.

    "Burin kowane matashin ɗanƙwallo shi ne ya zama ɗanwasan Man City domin taka leda tare da ƙwararrun 'yanwasa," in ji Nypan.

    "Har yanzu ni matashi ne sosai da ke son koyar abubuwa da yawa, amma damar da na samu ta aiki da mai horarwa Pep Guardiola za ta taimaka min wajen ƙara gogewa."

  3. Aubameyang ya bar Saudiyya

    Ɗanwasan gaba na Gabon Pierre-Emerick Aubameyang ya bar kungiyar Al-Qadsiah ta Saudiyya bayan kaka guda da ya shafe.

    A sanarwar da kungiyar ta fitar ta gode wa Aubameyang, amma ba tare da ta bayyana dalilin tafiyar tsohon ɗanwasan na Arsenal ba.

    Ɗanwasan mai shekara 36 ya ci wa kungiyar kwallo 21 a raga tare da taimakawa sau uku a ci a wasanni 36 da ya buga.

    Aubameyang ya taimakawa kungiyar zuwa matsayi na huɗu a teburin Saudi Pro League, tare da buga wasan karshe na lashe kofin Sarki wanda Al-Ittihad ta lashe.

  4. Real Madrid ta karrama Lucas Vazquez

    Real Madrid ta gudanar da bikin bankwana da Lucas Vazquez a ranar Alhamis An gudanar da bikin ne a filin da ƴanwasan ƙungiyar ke atisaye.

    Kylian Mbappe na cikin ƴanwasan da suka halarci bikin na Vazquez, ɗaya daga cikin ƴanwasan Madrid da suka fi yawan lashe kofi a tarihin ƙungiyar.

    Vazquez wanda ya fara taka leda tun yana shekara 16 a Madrid ya haska sau 400, kuma shugaban ƙungiyar Florentino Perez ya ba shi kyautar zinari tare da gode masa kan rawar da ya taka.

    Ɗanwasan mai shekara 34 ya lashe kofi 23 a shekaru kusan 10 da ya shafe a Madrid.

  5. An tantance ƴanwasa 30 da ke takarar lashe Ballon d'Or

    Kwamitin bayar da kyautar gwarzon ɗanwasan duniya ta Ballon d'Or ya kammala tantance ƴanwasa 30 da cikinsu za a zaɓi gwarzon shekara.

    Wata sanarwa da aka wallafa a shafin X na kyautar Ballon d'Or ta ce a ranar 7 ga Agusta ne za a sanar da ƴanwasan da ke takarar lashe kyautar a bana a ɓangaren maza.

    Kwamitin ya kammala tantance ƴanwasan ne bayan kammala gasar cin kofin duniya ta ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa da Chelsea ta lashe.

    A ranar 22 ga Satumba za a sanar da ɗanwasan da ya lashe kyautar ta Ballon d'Or a birnin Paris

    Kwamitin tantance gwarzon Ballon d'Or ya ƙunshi ƴanjarida daga mujallar wasanni ta Faransa da jaridar L’Equipe da suka zaɓo ƴanwasa 30.

    Ƴanjarida ne za su ƙada ƙuri'ar zaɓen gwarzon ɗanwasan duniya daga kasashe daga kasashe 100 bisa la'akari da ajin matsayi na ƙasashen a hukumar FIFA.

    Ana sa ran ƴanwasan PSG za su mamaye takarar da suka haɗa da Vitinha da Ousmane Dembele da Nuno Mendes da Achraf Hakimi da kuma Gianluigi Donnarumma bayan lashe kofi uku a kakar da ta gabata da suka ƙunshi har da kofin zakarun Turai da PSG ta lashe karon farko.

    Ana sa ran ƴan wasan Barcelona Raphinha da Lamine Yamal za su kasance sahun gaba bayan lashe kofi biyu a kakar da ta gabata da kuma ɗanwasan Chelsea Cole Palmer wanda ya lashe kyautar gwarzon ɗanwasan gasar cin kofin duniya ta ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa da aka kammala a Amurka bayan doke PSG 3-0.

  6. Man Utd ta nace wa Bryan Mbeumo

    Manchester United ta sake taya ɗanwasan gaba na Brentford Bryan Mbeumo, kunshin yarjejeniyar da ake ganin za ta kai kusan fam miliyan 70.

    Sai dai har yanzu Brentford ba ta ce komi ba game da tayin kuma ba ta tattauna da Manchester ba ko za ta sayar da ɗanwasan.

    United ta nace sai da karɓo Mbeumo inda take fatan ɗanwasan na Kamaru zai kasance cikin sabon zubin kocinta Ruben Amorim kafin soma wasannin share fagen kaka da za ta yi a Amurka.

    Mbeumo mai shekara 20 ya ci kwallo 20 a kakar da ta gabata a gasar Premier kuma ƙungiyoyi da dama ne ke ribibin ɗanwasan da suka haɗa har da Tottenham da tsohon kocinsa ke jagoranta.

  7. Liverpool na dab da kammala cinikin Hugo Ekitike

    Liverpool na dab da cimma yarjejeniya tsakaninta da Eintracht Frankfurt kan ɗanwasan gaba Hugo Ekitike

    Ana sa ran Liverpool za ta biya Frankfurt sama da fam miliyan 70.

    Tun da farko Frankfurt ta yi watsi da tayin Newcastle United na fam miliyan 70.

    Ana sa ran Liverpool za ta biya sama da fam miliyan 70 domin karɓo ɗanwasan kafin ƙarshen mako.

    Ekitike mai shekara 23 ya ci ƙwallo 15 a wasa 31 da ya buga wa Frankfurt tare da taimaka wa ƙungiyar zuwa matsayi na uku a teburin Bundesliga.

  8. Barcelona ta ba Lamine Yamal lamba 10

    Barcelona ta ba Lamine Yamal Lamba 10 ta Lionel Messi wanda ya fi yawan cin kwallaye a tarihin ƙungiyar.

    Barcelona ta tabbatar da matakin ne a ranar Laraba.

    Yamal ya gaji lamba 10 ne bayan Ansu Fati wanda ya gaji rigar bayan tafiyar Lionel Messi zuwa PSG.

    A ranar Lahadi ne Lamine Yamal ya yi bikin cika shekara 18 da haihuwa. Yanzu shi ne ɗanwasan da ke jan zarensa a Barcelona.

    Yamal wanda a bara ya saka lamba 19 wadda Messi ya saka kafin lamba 10, yanzu ya shiga cikin tarihin zaratan ƴanwasan Barcelona irinsu Messi da Ronaldinho da Rivaldo da Maradona.

    Ɗanwasan ya lashe La Liga biyu da Copa del Ray da Supercopa na Spain a Barcelona kuma ya taimaka wa Spainb lashe kofin Turai

  9. Liverpool ta lissafa Osimhen cikin zaɓin da take da shi

    Liverpool tana nazari kan wasu ƴanwasan gaba da za ta iya karɓowa idan har haƙarta ba ta cimma ruwa ba kan Alexander Isak na Newcastle.

    Ana tunanin Liverpool za ta iya ɗauko ɗaya daga cikin ƴanwasa shida da take nazari da suka haɗa da Ollie Watkins da Victor Osimhen da Yoane Wissa da Hugo Ekitike da Rodrygo da kuma Marcus Rashford.

    Newcastle United ta nace cewa ɗanwasanta Isak ba na sayarwa ba ne kuma ga alama za ta sabunta kwangilar shi.

    Rahotanni sun ce Liverpool ta tuntubi Napoli kan Victor Osimhen da kuma Aston Villa kan Ollie Watkins idan har ta gaza ɗauko Isak.

  10. Sundaland na son ɗauko Granit Xhaka

    Sunderland ta nuna bukatar ɗanwasan tsakiya na Bayer Leverkusen Granit Xhaka kamar yadda kafar Sky Sports ta ruwaito

    Ɗanwasan mai shekara 32 ya shafe shekara bakwai a Arsenal tsakanin 2016 zuwa 2023 kafin ya koma taka leda a Leverkusen ta Jamus.

    Xhaka, wanda shi ne kaftin din Switzerland, ya yi haskawa 99 a kaka biyu da buga wa Leverkusen kuma ya taka rawa a kakar 2023-24 ƙungiyar ta lashe Bundesliga kuma ba a doke ta ba.

  11. Vazquez ya yi bankwana da Madrid

    Lucas Vazquez ya sanar da yin bankwana da Real Madrid, ba tare da bayyana makomarsa ba.

    Ɗanwasan wanda ya fara yi wa Madrid wasa tun yana ɗan shekara 16 a 2007 ya sanar da matakin ne a shafinsa na Instagram.

    Tun a ranar 13 ga Yuli ne kwangilar shi ta kawo ƙarshe a Madrid.

    "A yau bayan buga wasa 400, lokaci ne da zan yi bankwana da ƙungiyar rayuwata. Zan bar Real Madrid amma ba zan taɓa mantawa da Real Madrid ba, in ji ɗanwasan mai shekara 34.

    Vazquez ya ci kwallo 38 a bara, tare taimakawa a ci sau 61, kuma ya lashe kofi 23, da suka ƙunshi kofin zakarun turai biyar da kofin La Liga huɗu.

    Ɗanwasan ya gode wa Real Madrid da kuma magoya bayanta.

  12. Dalilin da ya sa na yi watsi da tayin Barcelona - Nico Williams

    Nico Williams ya bayyana dalilin da ya yaƙi komawa taka leda a Barcelona bayan ya sanya hannu kan sabuwar kwantaragi da ƙungiyarsa ta Athletic Bilbao.

    Barcelona ta yi ƙoƙarin ɗauko ɗanwasan da ake ganin yana da kusanci da Lamine Yamal amma ya yi watsi da buƙatar.

    Matashin ɗanwasan ya ce yaƙi zuwa Barcelona ne saboda burinsa ya lashe gasar zakarun turai a ƙungiyarsa ta Bilbao da ya fara taka leda tun ƙuriciyarsa.

    Ɗanwasan ya sanya hannu kan doguwar yarjejeniya ta shekara 10 da Bilbao inda zai ci gaba da murza leda a San Mames har zuwa 2023

    Sannan Williams ya ce yana son ya ci gaba da wasa tare da ɗan'uwansa Inaki wanda yanzu shi ne jagoran tawagar Athletic Bilbao.

  13. Darajar Isak ta kai fam miliyan 130

    Rahotanni sun ce darajar ɗanwasan gaba na Sweden da Newcastle Alexender Isak ta kai fam miliyan 130.

    Liverpool na cikin ƙungiyoyin da ke farautar ɗanwasan yayin da take neman ɗanwasan gaba.

    Sai dai Newcastle ta nace cewa ɗanwasanta ba na sayarwa ba ne.

    Alexender Isak ya ci wa Newscatle kwallo 23 a raga a wasa 34 da ya buga a kakar da ta gabata kuma idan har Liverpool ta karɓo ɗanwasan zai kasance danwasa mafi tsada a tarihin ƙungiyar.

  14. Yadda magoya bayan Crystal Palace suka yi zanga-zangar adawa da matakin Uefa

    Magoya bayan Crystal Palace sun gudanar da zanga-zangar adawa da matakin hukumar kwallon kafar turai na dawo da kungiyar karamar gasar turai ta Conference League.

    Uefa ta dauki matakin ne saboda saba ka'idar hukumar ta hana kungiyoyi sama da daya su buga gasar turai karkashin mallakin mutun daya.

    Palace ta yi nasarar samun gurbin buga Europa league bayan lashe kofin FA a Mayu - kofi na farko da ta lashe. Sai dai kuma wanda ke da kungiyar, shi kuma yake da kungiyar Lyon ta faransa wadda ita ma ta samun gurbin buga gasar.

    Yanzu Nottingham Forest, da ta kare a matsayi na bakwai a teburin Premier za ta maye gurbin Palace a Europa Leaguer, amma Palace ta ce za ta daukaka kara.

  15. Liverpool ta yi watsi da tayin Bayern Munich kan Diaz

    Liverpool ta yi watsi da tayin fam miliyan 58.6 da Bayern Munich ta yi kan ɗanwasan gabanta Luis Diaz.

    Bayern Munich ta tuntuɓi Liverpool a farkon wannan watan amma ta ce ɗanwasan ba na sayarwa ba ne.

    A ranar Talata, Liverpool ta yi watsi da tayin ɗanwasan wanda kwangilar shi za ta kawo karshe a 2027 lokacin bazara.

    Ya jefa kwallo 22 a ƙungiyarsa da kuma kasarsa Colombia, 13 daga ciki a gasar Premier.

    Diaz ya ja hankalin Manchester City da kuma kungiyoyin Saudiyya.

    Liverpool ta shiga kasuwar neman ɗanwasan gaba kuma tuni ta nuna sha'awar ɗanwasan gaba na Sweden da Newcastle Alexander Isak.

  16. Real Madrid ta dauko Álvaro Carreras daga Benfica

    Real Madrid ta ɗauko ɗanwasan baya na Benfica Álvaro Carreras kan yarjejeniyar shekara shida.

    Real Madrid ta ɗauko ɗanwasan ne kan yuro miliyan 50.

    Álvaro Carreras mai shekara 22 ya fara taka leda ne a makarantar kwallon kafa ta Madrid kafin ya tafi Manchester United a 2020.

    Carreras na cikin sabbin zubin ƴanwasan Madrid bayan ɗauko Dean Huijsen da Trent Alexander-Arnold.

    Real Madrid ta kammala kakar da ta gabata ba tare da lashe kofi ba kuma karon farko tun 2021.

  17. Jordan Henderson ya dawo gasar Premier

    Kusan shekara biyu bayan ya bar Liverpool zuwa Saudiyya, Jordan Henderson ya dawo taka leda a gasar Premier ta Ingila a ƙungiyar Brentford.

    Henderson Ya tafi Al-Ettifaq ne kan fam miliyan 12 ƙarƙashin jagorancin tsohon kaftin din Liverpool Steven Gerrard kafin ya koma Ajax a farkon kaka bayan yin wata shida a gasar Saudiyya.

    A shekarunsa 12 a Anfield, Henderson ya lashe kofin Premier - kofin farko da ƙungiyar ta lashe a shekara 30 - ya kuma lashe kofin zakatun Turai da FA da kofin duniya na ƙungiyoyin ƙwallon kafa da kofin Super na Turai da Community Shield.

    Henderson ba ya cikin tawagar Gareth Southgate a gasar Euro 2024 inda bai buga wa Ingila wasa ba tun 2023.

    Bayan naɗa Tuchel a matsayin kocin Ingila a Janairu, Henderson ya taka leda a haskawa uku ƙarƙashin kocin ɗan ƙasar Jamus.

  18. Za a binciki Lamine Yamal kan bikin cika shekara 18

    Hukumomin Spain za su gudanar da bincike kan ɗanwasan gaba na Barcelona Lamine Yamal bayan rahotannin cewa ya gayyato wadanni a wajen bikin murnar cika shekara 18 da haihuwa.

    Ma'aikatar kare haƙƙin al'umma a Spain ce ta buƙaci ofishin babban mai gabatar da ƙara ya gudanar da bincike kan ɗanwasan.

    Lamine Yamal ya gudanar da bikin ne a ranar Lahadi a wani gidan da ya karɓi haya a garin Olivella da ke kusa da Barcelona, inda ya gayyato baƙi da dama da suka haɗa da abokan wasansa da waɗanda suka yi fice a YouTube da kafofin sada zumunta na Intanet.

    Ana zargin Lamine Yamal da ɗauko hayar wadanni domin nishaɗantar da baƙinsa, wani abin da ƙungiyar da ke kare su ta ce "ba za a amince ba a wannan ƙarni na 21."

    Rahotanni sun ce har ƙungiyar ta ADEE ta shigar da ƙara.

    Amma hukumomin Spain sun ce za a gudanar da bincike ne domin tabbatar da ko ɗanwasan ya saɓa doka da kuma saɓa ƴancin masu buƙata ta musamman.

    Barcelona dai ba ta ce komi ba game da zargin da ake yi wa ɗanwasanta, amma ta ce za ta yi nata bincike

  19. Luka Modric ya koma AC Milan

    AC Milan ta tabbatar da ɗauko Luka Modric daga Real Madrid.

    Ƙungiyar ta Seria A ta ce ɗanwasan ya sanya hannu ne kan yarjejeniyar shekara ɗaya tare da zaɓin ci gaba da taka mata leda a shekara ta biyu.

    Modric mai shekara 39 zai yi ƙoƙarin farfaɗo da AC Milan bayan fuskantar ƙalubale a kakar da ta gabata.

    Tuni ɗanwasan na Croatia wanda ya taba lashe kyautar gwarzon ɗanwasan duniya ya isa Milan inda kuma aka diba lafiyarsa.

    A watan Mayu Modric ya sanar da cewa zai bar Madrid bayan shafe kaka 13 a Spain. Ya lashe kofuna 28, da suka haɗa da kofin Turai shida da kofin duniya na ƙungiyoyin ƙwalon ƙafa guda shida da kofin Super na Turai biyar da kofin La Liga huɗu da Copa del Ray biyu da kuma kofin Super biyar na Spain.

    AC Milan dai ta ƙare ne a matsayi na takwas a teburin Seria A a kakar da ta gabata kuma ba ta samu gurbin taka leda ba a gasar Turai.

  20. Chelsea ta kafa tarihi a Ingila

    Chelsea ta zama ƙungiya ta biyar kuma ta farko a Ingila da ta ci kofuna fiye da ɗaya na hukumar ƙwallon ƙafa ta duniya , bayan da ta doke Zakarun Turai a gasar World Club Cup na Fifa da ci 3-0 a New Jersy, Amurka ranar Lahadi.

    Real Madrid ita ce ta farko a wannan bajinta da kofi shida, sai Barcelona mai uku, sai Bayern Munich mai kofi biyu kamar yadda ita ma ƙungiyar Corinthians take da biyu.

    Cole Palmer na Ingila ne ya jagoranci caccakar da Chelsean ta yi wa PSG da ƙwallo biyu sai kuma ya sa sabon cefane Joao Pedro ɗan Brazil a hanya shi ma ya zura ta uku.

    da wannan nasara yanzu wasu magoya bayan Chelsea na ganin sai an yi da gaske a kansu a gasar Premier ta kaka mai kamawa.