Kwamitin bayar da kyautar gwarzon ɗanwasan duniya ta Ballon d'Or ya kammala tantance ƴanwasa 30 da cikinsu za a zaɓi gwarzon shekara.
Wata sanarwa da aka wallafa a shafin X na kyautar Ballon d'Or ta ce a ranar 7 ga Agusta ne za a sanar da ƴanwasan da ke takarar lashe kyautar a bana a ɓangaren maza.
Kwamitin ya kammala tantance ƴanwasan ne bayan kammala gasar cin kofin duniya ta ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa da Chelsea ta lashe.
A ranar 22 ga Satumba za a sanar da ɗanwasan da ya lashe kyautar ta Ballon d'Or a birnin Paris
Kwamitin tantance gwarzon Ballon d'Or ya ƙunshi ƴanjarida daga mujallar wasanni ta Faransa da jaridar L’Equipe da suka zaɓo ƴanwasa 30.
Ƴanjarida ne za su ƙada ƙuri'ar zaɓen gwarzon ɗanwasan duniya daga kasashe daga kasashe 100 bisa la'akari da ajin matsayi na ƙasashen a hukumar FIFA.
Ana sa ran ƴanwasan PSG za su mamaye takarar da suka haɗa da Vitinha da Ousmane Dembele da Nuno Mendes da Achraf Hakimi da kuma Gianluigi Donnarumma bayan lashe kofi uku a kakar da ta gabata da suka ƙunshi har da kofin zakarun Turai da PSG ta lashe karon farko.
Ana sa ran ƴan wasan Barcelona Raphinha da Lamine Yamal za su kasance sahun gaba bayan lashe kofi biyu a kakar da ta gabata da kuma ɗanwasan Chelsea Cole Palmer wanda ya lashe kyautar gwarzon ɗanwasan gasar cin kofin duniya ta ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa da aka kammala a Amurka bayan doke PSG 3-0.