Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 28/07/2024

Labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 28/07/2024

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Daga Abdullahi Bello Diginza da Ahmad Tijjani Bawage

  1. Mu kwana lafiya

    Mun zo karshen rahotanni a wannan shafi na labarai kai-tsaye.

    Sai kuma gobe da safe idan Allah ya kai mu.

    Ahmad Bawage ke cewa asuba ta gari.

  2. Me ke faruwa a cikin ƙwaƙwalwarmu idan muka zo mutuwa?

  3. Ana ci gaba da gwabza faɗa a Gaza duk da tattaunawar tsagaita wuta

    Yaƙin Gaza

    Asalin hoton, EPA

    Yayin da wakilai da tawagar masu shiga tsakani ke taro a birnin Rome na Italiya domin tattaunawa kan tsagaita wuta a Gaza, rahotanni na cewa ana ci gaba da gwabza faɗa a kudancin zirin.

    Tankokin yaƙin Isra'ila na ci gaba da dannawa garuruwa uku da ke birnin Khan Younis, inda dubban iyalai suka tsere daga muhallansu.

    Sun yi cincirindo a Al-Mawasi da ke arewaci, da kuma Darul-Bala'a da ke kudanci.

    A ɓangare guda kuma dakarun Isra'ila na fafatawa ta ƙasa da sama tsakaninsu da mayakan Hamas a arewacin ƙasar kusa da iyakar Rafah da Masar.

    Ma'aikatar lafiya da ke karkashin Hamas ta ce sama da Falasɗinawa 60 aka kashe cikin kwanaki biyu.

  4. Mutum 19 sun mutu a hatsarin jirgin ruwa a Habasha

    Hatsarin jirgin ruwa

    Asalin hoton, Getty Images

    Rahotanni daga arewacin Habasha na cewa aƙalla mutane 19 ne suka mutu sakamakon nutsewar da kwale-kwalensu ya yi a yankin Amhara na ƙasar.

    Jirgin ruwan ya yi hatsari ne lokacin da ya ke ƙoƙarin ketare kogin Tekeze.

    An yi amanna cewa mutum 26 ne a cikin kwale-kwalen lokacin da ya yi hatsari a jiya Asabar.

    An garzaya da waɗanda suka tsira zuwa asibiti, yayin da rahotanni daga kamfanin dillancin labarai na AMC a yankin na Amhra, ke cewa har da wani karamin yaro cikin waɗanda suka ji munanan raunuka.

    Babu tabbacin ko an gano ɗaukacin gawawwakin waɗanda suka rasu a haɗarin.

    Tun a watan da ya gabata ya kamata a ce an kammala aikin gadar da ta ratsa kogin na Tekeze, sai dai an samu tsaiko kamar yadda wani jami'i ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AMC.

    Hukumomin Habasha dai ba sa bari 'yan jarida zuwa arewacin ƙasar, yankin da a baya-bayan nan ya yi fama da tashin hankali tsakanin sojojin ƙasar da mayakan kabilar Amhara da aka fi sani da Fano.

  5. Ina goyon bayan masu shirin fita zanga-zanga - Peter Obi

    Peter Obi

    Ɗan takarar shugaban ƙasa a karkashin jam'iyyar Labour a zaɓen 2023, Peter Obi ya ce yana goyon bayan masu shirin fita zanga-zanga ranar 1 ga watan Agusta don adawa da tsadar rayuwa.

    Obi, wanda tsohon gwamnan jihar Anambra, ya ce kundin tsarin mulki ya bai wa ƴan ƙasa damar yin zanga-zanga.

    Sai dai, ya yi gargaɗi kan tayar da hankali, inda ya ce ya kamata a yi zanga-zanga yadda doka ta tanada.

    Ya ce yunwa da rashin madogara na cikin abubuwan da suka sa matasa ke shirin fita zanga-zanga, inda ya yi kira ga hukumomin Najeriya da su fito domin tattaunawa da matasan da kuma jin kukansu.

    "Abubuwa sun yi matukar wahala a ƙasar nan. Ya kamata mu saurari korafe-korafen ƴan Najeriya," in ji Obi.

    Ya yi kira ga jami'an tsaro da su bai wa masu zanga-zangar kariya, sannan kada su wuce gona da iri.

  6. An naɗa sabbin shugabannin Kano Pillars

    Kano Pillars

    Asalin hoton, Getty Images

    Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya amince da naɗin sabbin shugabannin ƙungiyar ƙwallon kafa ta Kano, Pillars.

    Pillars, wadda ake kira ''sai masu gida'' ba ta da shugabanni tun bayan da aka kori Babangida Little daga jagoranci.

    A wata sanarwa da aka fitar daga ofishin kwamishinan matasa da wasanni, Mustapha Rabiu Kwankwaso ta sanar da mutum 14 da za su ja ragamar Pillars.

    Ali Na Yara mai Samba shi ne sabon shugaba a matakin rikon kwarya na shekara ɗaya tare da Abubakar Isa Dandago a matakin jami'in yaɗa labaran ƙungiyar.

    Kano Pillars, wadda ta kare a mataki na 11 a gasar Premier League ta Najeriya da ta wuce, na fatan taka rawar gani a kakar 2024/25.

    Sabbin shugabannin za su yi aiki tare da ma'aikatar matasa da wasanni ta jihar da sauran masu ruwa da tsaki domin ka Pillars gaba.

    Za a fara gasar Premier ta Najeriya daga 31 ga watan Agusta, inda aka tanadi naira miliyan 200 ga duk wadda ta lashe kofin bana.

    A gefe guda, gwamnan ya kuma naɗa kaftin ɗin ƙungiyar kwallon kafa ta Najeriya (Super Eagles) Ahmed Musa, a matsayin jakadan wasanni na jihar.

    Jerin shugabannin Kano Pillars

    • Aliyu Nayara Mai Samba - Shugaba
    • Salisu Muhammad Kosawa - Mamba
    • Abubakar Isa Dandago - Jami'in yaɗa labarai
    • Ismail Abba Tangalash- Mataimakin Jami’in yaɗa labarai
    • Yusuf Danladi Andy Cole - Mamba
    • Muhammad Usman - Mamba
    • Ahmad Musbahu - Mamba
    • Umar Umar Dankura - Mamba
    • Rabiu Abdullahi - Mamba
    • Nasiru Bello- Mamba
    • Muhammad Danjuma Gwarzo - Mamba
    • Mustapha Usman Darma - Mamba
    • Muhammad Ibrahim (Hassan West) - mamba
    • Engr Usman K/Naisa- Mamba
  7. Ƴan sandan Kaduna sun gargaɗi matasan jihar kan fita zanga-zanga

    Ƴan sanda

    Asalin hoton, Getty Images

    Rundunar ƴan sandan jihar Kaduna ta gargaɗi masu shirin fita zanga-zanga kan tsadar rayuwa da aka shirya fara wa daga ranar 1 ga watan Agusta, da su guji yin hakan da kuma tayar da tarzoma.

    Wata sanarwa da mai magana da yawun ƴan sandan jihar ASP Mansir Hassan ya fitar, ta ce suna sa ido kan batutuwa da suka shafi fita zanga-zangar, inda ta ce yayin da wasu ke kiran a yi zanga-zanga mai lumana, wasu kuwa na kiraye-kirayen tayar da tarzoma a lokacinta.

    "Akwai mutanen da suka ce suna goyon zanga-zangar lumana, amma akwai masu son tayar da tarzoma, hakan ya sa shakku kan ainihin manufarsu ta yin zanga-zanga," in ji sanarwar.

    Rundunar ta yi kira ga ƴan jihar ta Kaduna da su guji tayar da fitina da kuma nesanta kansu da duk wata ƙungiya da ke son yin zanga-zanga.

    "Duk da cewa muna mutunta hakkin da kundin tsarin mulkin ya bai wa ƴan ƙasa na yin zanga-zanga ta lumana, sai dai muna nanata cewa yin ta a wannan lokaci bai dace ba ganin cewa ƙungiyoyin ɓata gari za su iya shiga su sauya manufarta.

    "Muna gargaɗi ga duk wata ƙungiya da ke shirin wargaza ƙasar nan da kuma ɓata gari da ke son jirkita zanga-zangar zuwa tarzoma da su guji yin hakan. Ba za mu lamunci kisan mutane babu gaira ba dalili ba, lalata wuraren jama'a ko kuma satar kayan mutane a wuraren kasuwancinsu," a cewar sanarwar ta ƴan sandan Kaduna.

    Domin samar da zaman lafiya, rundunar ƴan sandan ta buƙaci ƙungiyoyi da ke shirin yin zanga-zanga da su gabatar da bayanai da suka kamata ga kwamishinan ƴan sandan jihar domin a ba su kariya yayin zanga-zangar.

  8. Shugaban Venezuela ya kaɗa ƙuri'a a zaɓen shugaban ƙasar

    Shugaban ƙasar Venezuela, Nicolas Maduro, ya kaɗa ƙuri'arsa a Caracas, babban birnin ƙasar, a zaɓen shugaban ƙasar mai matuƙa muhimmanci.

    Mista Maduro ya ce zai tabbatar an kiyaye tare da amincewa da sakamakon zaɓen da hukumar zaɓe za ta fitar.

    Akwai zargin cewa hukumar zaɓen ƙasar cike take da abokansa.

    An hana mafi yawan 'yan takarar adawa tsayawa takarar, kuma miliyoyin 'yan ƙasar da ke zaune a ƙasashen ƙetare ba su samu damar rajista don kaɗa ƙuri'unsu ba.

    Ƙuri'ar jin ra'ayin jama'a ta nuna cewa ɗan takarar jam'iyyar adawa, Edmundo Gonzalez na gaba da mista Maduro.

    Akwai dogayen layuka a rumfunan zaɓe, masu sharhi na ganin cewa yawan fitowar masu zaɓe zai iya taimaka wa 'yan adawa.

  9. Tottenham ta ɗauki ɗan wasan Koriya ta Kudu Yang

  10. Tsohon ma'aikacin BBC Hausa Lawal Saulawa ya rasu

    ..

    Asalin hoton, Family

    Tsohon ma'aikacin BBC Hausa Lawal Yusufu Saulawa ya rasu a gidansa da ke unguwar Badikko da ke Kaduna.

    Marigayin ya yi aiki da sashen Hausa na BBC daga 1973 zuwa 1976, sannan ya riƙe muƙamin kwamishinan yaɗa labaran tsohuwar jihar Kaduna a shekarun 1980.

    Ya riƙe manyan muƙamai a hukumomin yaɗa labarai irin su VON da FRCN, sannan ya yi shugaban gidan radiyon Nagarta a jihar Kaduna.

    Marigayin ya rasu ya bar matan aure da 'ya'ya da jikoki da dama.

  11. Za a fara taron tsagaita wutar yaƙin Gaza a Italiya

    Masu shiga tsakani a birnin Rum na Italiya, na dab da fara zama domin tattauna batun tsagaita wutar yaƙin Gaza da za ta kai ga sakin Isra'ilawan da ake tsare da su.

    Tuni shugaban Hukumar Leƙen Asirin Amurka ta CIA, Walliam Burns ya isa birnin domin ganawa da firaministan Qatar, Sheikh Mohammed bin Abdulrahman Al Thani, shugabannin hukumomin leƙen asirin ƙasashen Masar da Isra'ila.

    Akwai faragabar kasa cimma matsaya a tattaunawar, yayin da firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu ke ƙoƙarin ɓullo da dabarun inganta tsaro domin hana mayaƙan Hamas shiga arewacin Gaza.

    An shafe watanni ana tattauna batun tsagaita wutar yaƙin ba tare da cimma matsaya ba.

  12. Netanyahu zai gana da ministocin tsaron Isra'ila don mayar da martani kan harin Majdal Shams

    ..

    Asalin hoton, AFP

    Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu zai gana da ministocin tsaron ƙasar don tattauna yadda ƙasar za ta mayar da martani harin da aka kai garin Majdal Shams da ke ƙasar.

    A ranar Asabar ne Netanyahu ya katse ziyarar da yake yi Amurka bayan harin wata roka da aka kai tuddan gola da Isra'ila ta mamaye, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar matasa 12.

    Isra'ila ta zargi ƙungiyar Hezbollah da kai harin, zargin da ƙungiyar ta musanta.

    Netanyahu ya ce Hezbollah za ta ɗanɗana kuɗarta kan wannan harin.

    Ministocin Isra'ila - waɗanda suka halarci jana'iza a garin Majdal Shams - sun fuskanci suka daga mutanen garin saboda abin da suka kira ''kasa kare yankin''.

  13. An goge shafin Facebook na mawaƙi Dauda Kahutu Rarara

    ..

    Asalin hoton, Dauda Kahutu Rarara/Instagram

    Bayanai na cewa an goge shafin fitaccen mawaƙin siyasar nan Dauda Kahutu Rarara daga dandalin Facebook

    Hakan na zuwa ne bayan da aka yi zargin cewa wasu masu amfani da dandalin ne suka riƙa kai ƙorafin shafin nasa ga kamfanin na Facebook,(reporting) bayan ya wallafa wata sabuwar waƙa a shafin nasa da ake zargin ba ta yi wa matasan daɗi ba.

    A 'yan kwanakin nan ne dai mawakin ya fitar da wata sabuwar waƙa da ya wallafa a shafukansa na sada zumunta.

    Waƙar dai ta ƙunshi yabo ga shugaban Najeriya, Bola Tinubu kan wasu ayyukan da mawaƙin ke iƙirarin shugaban ya samar wa ƙasar.

    An ji yo Rarara cikin wasu baitocin wakar na cewa:

    "Tinumbu ya gama mana aiki ba batun ɓoyo".

    "Kananan hukumomi ruhinsu ya dawo".

    ''Yanzu talauci ƙyaram, yunwa ƙyaram,

    kana security daram-dam-dam, ƴanci daram".

    ''Sannu farin cikin ƙasa Tinubu, sai godiya, baba makanike wajen gyara lamba ɗaya''.

    Sabuwar waƙar na zuwa ne a daidai lokacin da wasu matasan ƙasar ke shirin gudanar da zanga-zangar tsadar rayuwa da yunwa da rashin tsaro da ƙasar ke fama da su.

    Wannan dalilin ne ya sa suke kallon waƙar tamkar izgili ko zolaya mawaƙin ke yi wa 'yan ƙasar, lamarin da ya sa suka ɗauki matakin gangamin kai ƙorafin shafin nasa zuwa ga kamfanin Facebook, domin buƙatar kamfanin ya goge shafin.

    Bayan kamar kwana biyu da fara gangamin, Facebook ya goge shafin - mai mabiya fiye da miliyan guda - daga dandalin.

  14. ‘Tsaikon fito da man fetur daga jiragen ruwa ne ya janyo ƙarancinsa a Abuja da Legas’

    .

    Asalin hoton, OTHER

    Babban kamfanin mai na Najeriya NNPCL, ya ce tsaikon da aka samu wajen fito da man fetur daga jiragen dakon man da ke bakin teku ne ya haddasa ƙarancin man a biranen Abuja da Legas.

    Cikin wata sanarwa da kamfanin ya wallafa a shafinsa na X ya ce tsaikon fito da man ya janyo cikas wajen rarraba shi zuwa wasu sassan biranen Abuja da Legas.

    Kamfanin ya kuma ce yana ƙoƙarin tuntuɓar masu ruwa da tsaki don ganin ya shawo kan matsalar, ta yadda za a riƙa fito da man a kan lokaci, domin ci gaba da rarraba man zuwa yankunan.

    Najeriyar dai kan shigo da man da take amfani da shi daga ƙasashen ƙetare ta jiragen ruwa.

    A 'yan kwanakin biyun nan dai an riƙa ganin layukan ababen hawa a wasu gidajen man birnin Abuja.

  15. Mutum tara sun mutu sakamakon turmutsitsi a gidan rawa a DR Kongo

    Hukumomin Lafiya a Jamhuriyar Dimokraɗiyyar Kongo sun ce aƙalla mutum tara sun mutu, bayan wani turmutsitsi da ya auku a wani bikin rawa cike da dandazon mutane.

    An gudanar da bikin rawar ranar Asabar - wanda mawaƙi Mike Galambay ya cashe - a babban filin wasan ƙwallon ƙafa na Kinshasa, babban birnin ƙasar

    Rahotonni sun ce da dama daga cikin waɗanda suka mutun, ƙananan yara ne, yayin da aka kai da dama asibiti bayan aukuwar lamarin.

    Cikin wata sanarwa da gwamnan Kinshasa, Daniel Bumba, ya fitar, ya ɗora alhakin faruwar lamarin kan ''yawan dandazon jama'ar da suka halarci bikin''.

    An jibge tarin jami'an tsaro a lokacin bikin.

    Masu shirya bikin, sun ce lamarin ya faru ne sakamakon yunƙurin da jami'an tsaron suka yi na kama waɗanda suke zargi da ƙoƙarin tayar da yamutsi a bikin, abin da ya kai ga rasa rai.

    Mutum 30,000 ne suka halarci bikin na ranar Asabar a filin wasan da ke ɗaukar mutum 80,000, kamar yadda masu shirya bikin suka bayyana.

    A shekarar 2022 ma wani turmutsitsi da ya auku a wannan fili ya yi sanadin mutuwar mutum 11.

  16. An dakatar da 'yar wasan Najeriya daga gasar Olympics bayan gwajin ƙwayoyi

    ,,.

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Ogunsemilore ta wakilci Najeriya a gasar Olympics ta Landan a 2022

    Hukumar da ke yi wa 'yanwasa gwajin ta'ammali da ƙwayoyi ta duniya, ta ce an dakatar da 'yar wasan damben Najeriya, Cynthia Temitayo Ogunsemilore, daga wasanni gasar Olympics da ke gudana a birnin Paris, sakamakon saɓa wa dokar amfani da ƙwayoyi.

    Cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar ta ce sakamakon gwajin da aka yi wa 'yar wasan ya nunacewa ta yi amfani da wasu ƙwayoyin da aka haramta.

    An dai yi wa 'yan wasan gwajin amfani da ƙwayoyi ranar Talata kwana guda kafin fara gasar.

    A ranar Litinin ne aka tsara Ms Ogunsemilore mai shekara 22 za ta fara nuna bajintarta a gasar, inda za ta fafata a ajin masu nauyin ƙasa da kilogiram 60.

    To sai dai bisa wannan dakatarwar 'yar wasan ba za ta shiga gasar ba, ko taimaka wa abokan wasanta ta kowane hali.

  17. Gwamnan Osun ya gayyaci jagororin zanga-zanga da masu ruwa da tsaki domin tattaunawa

    Ademola Adeleke

    Asalin hoton, Ademola Adeleke/X

    Gwamnan jihar Osun da ke kudu maso yammacin Najeriya, Ademola Adeleke, ya gayyaci jagororin zanga-zangar tsadar rayuwa da ake shirin gudanarwa da sauran masu ruwa da tsaki daga jami'an tsaro da ƙungiyoyin fararen hula domin tattaunawa game da batun a gobe Litinin.

    Cikin wata sanarwa da kakakin gwamnan jihar, Mallam Olawale Rasheed, ya fitar, ya ce gwamnan ya umarci wata tawagar wakilansa ta tuntuɓi wakilan ƙungiyoyin fararen hula da na ɗalibai domin zaman tattaunawa kan halin da tattalin arzikin ƙasar ke ciki.

    Gwamna ya kuma buƙaci shugabannin hukumomin 'yansanda da sauran jami'an tsaro su halarci zaman, inda za a bai jagororin zanga-zangar damar bayyana irin damuwar da ke zukatansu.

    “Zaman zai bayar da dama ga duka ɓangarorin su bayyana matsalolinsu da abin da suke so gwamnatoci a matakai daban-daban su yi domin magance matsalolin''

    “Za kuma mu ɗauki abin da muka tattauna a zaman domin kai wa jagororin gwamnati, kama daga ni kaina a a matsayina na gwamna zuwa shugaban ƙasa a Abuja domin aiki da shi'', kamar yadda sanarwar ta ambato gwamnan na bayani.

    Mista Adeleke ya kuma ce zaman zai bai wa gwamnati damar bayyana wa al'umma abin da take yi don magance matsalar tattalin arziki da ƙasar ke fuskanta.

  18. Al'ummar Venezuela na kaɗa ƙuri'a a zaɓen shugaban ƙasa

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Al'ummar Venezuela sun fara kada kuri'a a zaben shugaban kasa da ake gani mafi jan hankali a kasar.

    'Yan ƙasar sun ɗauki zaɓen da muhimmanci sosai saboda samar da sauyi kan matsalolin da ƙasar ke fuskanta.

    Shugaba Nicolas Maduro mai ra'ayin gurguzu na neman tazarce ne wa'adi na uku.

    Ƙuri'ar jin ra'ayin jama'a ta nuna shi ne zai lashe zaɓen fiye da abokan hamayyarsa Edmundo Gonzalez.

    Sai dai ƙasashen duniya na bayyana damuwa game da tabbatar da adalci a zaɓen

  19. 'Yan tawayen Abzinawa sun ce sun kashe sojojin Mali da yi wa dakarun Wagner lahani

    ..

    Asalin hoton, AFP

    'Yantawayen Abzinawa a arewacin Mali sun ce sun yi wa dakarun gwamnatin ƙasar da sojojin hayar Rasha lahani.

    Sun ce sun kashe sojojin da dama da kama wasu a kwana biyu da suka yi artabu a kusa da kan iyaka da Algeria.

    Sai dai rundunar sojin Mali ta ce sojojinta biyu ne kawai aka kashe a faɗan, inda ita ma ta yi iƙirarin kashe 'yantawayen da dama.

    Ƴantawayen dai na faɗa ne domin tabbatar da ƴancin arewacin Mali.

    Sojojin Mali da suka kwace mulki shekara uku da suka gabata sun ƙarfafa danganta da Rasha tare da alwashin murƙushe 'yantawaye da masu iƙirarin jihadi a arewacin ƙasar

  20. Trump ya alƙawarta ƙarfafa harkar kirifto idan ya ci zaɓen Amurka

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Ɗan takarar shugabancin Amurka, Donald Trump ya shaida wa taron kuɗin intanet na Bitcoin cewa zai karfafa Kirifto idan har ya lashe zaɓen shugaban Amurka a watan Nuwamba a mai zuwa.

    A baya, Mista Trump ya taɓa yin watsi da kuɗin na intanet - da ya kira a matsayin 'zamba', amma a yanzu ya nemi goyon bayan manyan 'yan kirifto.

    Yayin da yake jawabi a wani gangamin yaƙin neman zaɓensa a Minnesota, tsohon shugaban ƙasar ya caccaki Kamala Harris, inda ya ce ba alheri ba ce ga Amurka.

    Mista Trump ya ce mataimakiyar shugabar kasa ce da ta gaza, gwamnatinsu ta gaza Amma a nata gangamin a Massachusetts, Kamla Harris ta ce sukarta da Trump ke yi - wani abin mamaki ne.

    Ƙuri'ar jin ra'ayin jama'a ta nuna farin jinin Trump ya ragu tun lokacin da Kamala Harris ta zama wadda ake ganin za ta yi wa Democrat takara.