Abubuwan da ke faruwa da Najeriya da sauran sassan duniya 05/06/2024

Labaran abubuwan da ke faruwa da Najeriya da sauran sassan duniya 05/06/2024

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Daga Abdullahi Bello Diginza, da Umar Mikail

  1. Labarai da dumi-dumi, Starmer ya isa fadar Buckingham don karɓar takardar kama aiki

    ..

    Firaministan Birntaniya mai jran gado, Sir Keir Starmer ya isa fadar Buckingham domin karɓar takardar kama aiki a a mtsayin sabon Firaministan Birtaniya a hukumace,

    Hakan na zuwa ne jim kaɗan bayan da tsohon Firaministan ƙasar Rishi Sunak ya bar fadar bayan miƙa wa Sarki takardar murabus ɗinsa.

    Mista Starmer ya isa fadar ne tare da matarsa domin miƙa gaisuwarsa ga Sarki Chareles III, wanda zai ba shi damar kafa gwamnati.

    Jam'iyyar Labour ta Mista Starmer ce ta yi nasara a zaɓen ƙasar da aka gudanar ranar Alhamis.

  2. Lauyoyin Aminu Ado Bayero sun fice daga shari'ar dambarwar masarautu

    ..

    Asalin hoton, Facebook

    Lauyoyin Sarkin Kano na goma sha biyar, Alhaji Aminu Ado Bayero, sun fice daga shari’ar dambarwar masarautar Kano wanda ake yi a babbar kotun jihar.

    Lauyoyin sun ɗauki matakin ne a zaman da kotun ta yi ranar Alhamsi, bayan kai ruwa rana tsakanin ɓangarorin da ke shari'a da juna.

    A lokacin zama kotun lauyan Aminu Ado Bayero, Abdul Muhammed, ya fara da shaida wa kotun cewa akwai takardar shaidar ta ke tabbatar da cewa sun ɗaukaka ƙara kuma an shigar da bayanan a gaban kotun, inda ya nemi kotun kada ta ci gaba da sauraron shari’ar har sai an saurari ɗaukaka ƙarar da suka yi.

    Lauyan ya kuma buƙaci kotun ta ƙara musu lokaci don mayar da martani kan wasu takardu da ya ce an ba su ranar Laraba.

    To sai dai ɓangaren masu ƙara sun soki waɗannan buƙatu, inda babban lauyan gwamnatin Kano da majalisar dokokin jihar, Eyitayo Fatogun ya ce babu waɗannan bayanan a kotun.

    Inda ya shaida wa kotun cewa ba haka ake yi ba, yana mai cewa dokokin babbar kotu sun ce idan kana so ka shigar da wasu bayanai a gaban kotu nema ake yi ba kawai ka kawo wata takarda ba.

    Bayan sauraron duka ɓangarorin biyu, Mai shari'a Amina Adamu Aliyu ta ce buƙatun da lauyan Aminu Ado Bayero ya gabatar ba su da karfin da za su hana ci gaba da sauraron shari’ar don haka ta yi watsi da su.

    Inda ta bayar da umarnin ci gaba da sauraron shari'ar da ke gaban kotun

    To sai dai wannan hukunci bai yi wa lauyoyin Aminu Ado Bayero daɗi ba, inda Barrister Sanusi Musa ya mike ya shaida wa kotun cewa sun fice daga wannan shari’a, sannan ya ce za su koma su sanar da wanda suke wakilta don ya nemi wanda zai wakilce shi, sannan suka fice daga kotun.

    Bayan ficewarsu ne, kuma sai mai shari’a Amina Adamu Aliyu ta ci gaba da sauraron karar, inda lauyan sarakunan da gwamnatin Kano ta ce ta sauke wato Bichi da Rano da Gaya da kuma Karaye, Hassan Tanko Kyaure ya buƙaci a ƙara masa lokaci don ya yi nazari akan takardun da aka ba su.

    Sannan ya kuma buƙaci kotun ta rushe sabuwar dokar masarautun Kano ta 2024, amma mai shari’ar ta ce ba zai yiwu a ƙara musu lokaci ba, saboda ta bayar da odar cewa ba za ta ƙara lokaci ba.

    Daga ƙarshe Mai shari’a Amina Adamu Aliyu ta ɗage zaman kotun zuwa ranar 18 wannan wata don yin hukunci a kan buƙatun da kowanne ɓangare ya nema.

  3. Sunak ya bar fadar Buckingham bayan miƙa wa Sarki takardar murabus

    .

    Firaministan Birtaniya Rishi Sukan ya fice daga fadar sarki ta Buckingham bayan miƙa wa sarki takardar ajiye aiki.

    Mista Sunak ya fice daga fadar ne a matsayin tsohon Firaministan Birtaniya.

    A yanzu kuma ana jiran sabon Firaministan ƙasar, Keir Starmer na jam'iyyar Labaour ya isa Buckingham domin karɓar takardar kama aiki daga wajen Sarkin.

  4. Sunak ya isa fadar Buckingham

    .

    Asalin hoton, PA

    Firaminitan Birtaniya Rishi Sunak tare da mai ɗakinsa, Akshata Murty sun isa fadar Buckingham.

    Mista Sunak ya je fadar ce da nufin miƙa takardar sauka daga matsayinsa a hukumance ga Sarki Charles III, bayan da jam'iyyarsa ta Conservative ta sha kaye a zaɓen ƙasar.

    Cikin wani jawabi da ya yi wa magoya bayansa jim kaɗan kafin ficewarsa daga fadar gwamnati, Mista Sunak ya gode wa abokan aikinsa da mai ɗakinsa da kuma 'ya'yansa.

    Ya ce ba zai manta da irin gagarumar gudunmowa da suka ba shi wajen bauta wa ƙasarsa ba.

  5. Labarai da dumi-dumi, Rishi Sunak ya fice daga fadar gwamnati

    ..

    Firaministan Birtaniya mai barin gado Rishi Sunak ya fice daga fadar gwamnatin ƙasar bayan kayen da jam'iyyarsa ta sha a zaɓen ƙasar da aka gudanar ranar Alhamis.

    Cikin wani taƙaitaccen jawabi da ya yi kafin fitarsa daga fadar, Mista Sunak ya ɗauki alhakin rashin nasarar da jam'iyyarsa ta Conservative ta yi a zaɓen.

    "Na fahimci fushi da rashin jin daɗin da kuke cikin kan sakamakon zaɓen nan,amma na ɗauki alhakin wannan rashin nasarar da jam'iyyarmu ta samu,'' in ji firaministan.

    Rishi Sunak ya kuma gode wa duka 'yan takarar jam'iyyar da tawagar yaƙin neman zaɓen jam'iyyar kan ƙoƙarin da ya ce sun a zaɓen.

    Haka kuma ya bai wa 'yan majalisar jam'iyyarsa da suka rasa kujerunsu a zaɓen.

    A yanzu Rishi Sunak ya nufi fadar Sarki Charles III, ta Burkingham domin miƙa takardarsa ta murabus daga matsayinsa na Firaministan Birtaniya a hukumance.

    ,,

    Asalin hoton, PA Media

    Bayanan hoto, Rishi Sunak lokacin da yake ficewa daga fadarsa tare da mai ɗakinsa
  6. Gwamnatin Najeriya ta gargaɗi jihohi 18 kan fuskantar ambaliya

    ..

    Asalin hoton, NEMA

    Gwamnatin Najeriya ta gargaɗi jihohin ƙasar 18 kan barazanar ɓarkewar cutar Kwalara saboda barazanar fuskantar ambaliya, sakamakon ci gaba da ruwan sama da ake yi a jihohin.

    Ministan ruwa da tsaftar muhalli na ƙasar, Joseph Terlumum ne ya bayyana damuwar a lokacin da yake jawabi ga taron manema labarai ranar Alhamis a Abuja.

    Ya ce kawo yanzu mutum 63 ne suka mutu sakamakon ɓullar cutar, yayin da aka samu mutum 1,102 da ake zargi sun kamu da cutar.

    Mamakon ruwan sama da ake samu a baya-bayan nan a wasu jihohin ƙasar na ƙara fargaba a zukatan jama'a kan ƙara bazuwar cutar, lamarin da ya sa ministan ya yi kira ga jihohin da su ƙara ƙaimi wajen tsaftace magudanar ruwa, don kauce wa ambaliya.

    “Muna kira ga jihohi da ƙananan hukumomi su ƙara ƙaimi wajen tsaftace muhalli domin kauce wa ambaliya da sauran bala'o'in da ke tattare da ambaliya, kamar cutar kwalara''.

    Jihohin da ministan ya ce suna fuskantar barazanar ambaliyar sun haɗa da; Akwa Ibom da Anambra da Adamawa da Benue da Bayelsa da Cross River da Delta da Edo da Jigawa da Kogi da Kebbi da Kaduna da Niger da Nasarawa da Ondo da Ogun da Rivers da Taraba da luma birnin tarayya Abuja

  7. Rishi Sunak ya ɗauki alhakin kayen jam'iyyar Conservative

    ....

    Asalin hoton, Reuters

    Firaminista mai barin gado Rishi Sunak na jam'iyyar Conservative ya ce ya ɗauki alhakin shan kayen jam'iyyarsa.

    Ministan tsaron ƙasar Grant Shapps, wanda ya rasa kujerarsa, ya kuma alaƙanta kayen da taƙaicin masu kaɗa ƙuri'a kan fafatawa a cikin gida da kuma rarrabuwar kawuna a cikin jam'iyyar.

    Nasarar jam'iyyar Labour ta zo ne shekaru biyar kacal bayan ta sha kashi mafi muni a zaɓen da Brexit ya mamaye.

    Sai dai da alama rinjayen manyan jam'iyyun Biritaniya biyu na raguwa.

    A karon farko cikin ƙarni guda, ana hasashen jam'iyyun Conservatives da Labour gaba daya za su samu ƙasa da kashi sittin cikin dari na dukkan ƙuri'un da aka kaɗa.

    Nigel Farage na jam'iyyar Reform Party ya ba da shawarar cewa ana ci gaba da daidaita hakki a siyasar Burtaniya.

  8. An tsamo gawawwakin baƙin haure 89 daga tekun Atlantika

    ....

    Asalin hoton, Reuters

    Jami'an tsaron gaɓar tekun Mauritaniya sun tsamo gawawwakin baƙin haure 89 daga teku, waanda kwale-kwale ya kife da su a ranar Litinin.

    An ceto mutum tara da suka hada da yarinya ƴar shekara biyar, amma wasu da dama sun ɓata.

    A cewar waɗanda suka tsira, kwale-kwalen da suke ciki—ya taso ne daga yankin iyakar Senegal da Gambiya a makon jiya ɗauke da mutu 170.

    Jirgin ruwan ya kife ne a gaɓar tekun kudu maso yammacin ƙasar Mauritania.

    Ƙasar Mauritaniya dai ta kasance wata muhimmiyar hanya da bakin hauren da ke yunƙurin isa Turai daga yammacin Afirka ke amfani da ita.

    Dubban kwale-kwale ne ke tashi daga kasar kowace shekara, inda tsibirin Canary, wani bangare na Sifaniya, ya kasance wurin da aka fi zuwa.

    A bara, kusan baƙin haure 40,000 ne suka isa tsibirin Canary, a cewar gwamnatin Spain inda adadin ya nunka na shekarar da ta gabata.

    Kungiyar agaji ta Caminando Fronteras ta yi ƙiyasin cewa sama da baƙin haure 5,000 ne suka mutu a yunƙurin shiga ƙasar Sifaniya ta teku a cikin watanni biyar na farkon shekarar 2024.

    A watan Afrilu, Tarayyar Turai ta bai wa Mauritania tallafin Yuro miliyan 210 kwatankwacin dalar Amurka miliyan 225, inda aka ware kusan Yuro miliyan 60 don yaƙi da ƙauran ƴan ci rani zuwa Turai ba tare da izini ba.

  9. An fara kaɗa ƙuri'a a zaɓen shugaban ƙasa zagaye na biyu a Iran

    .

    Asalin hoton, AFP

    An fara kaɗa kaɗa ƙuri'a a zaɓen shugaban ƙasar Iran zagaye na biyu, da za a fafata tsakanin mai ra'ayin riƙau, Saeed Jalili da mai ra'ayin kawo sauyi, Masoud Pezeshkian.

    An samu ƙarancin fitowar masu kaɗa ƙuri'a a zagayen farko, duk da kiran fitowa zaɓen da jagoran addinin ƙasar, Ayatollah Ali Khamenei ya yi.

    Sai daia a wannan karon ma jaogran addainin ya sake nanata kiransa na fitowar masu zaɓe a zaɓen zagaye na biyun.

    A makon da ya gabata ne dai aka yi zaɓen zagayen farkon, inda duka 'yan takara suka gaza samun kashi 50 cikin 100 na ƙuri'un da aka kaɗa.

    Zaɓen na zuwa a daidai lokacin da ƙasar ke fama da jerin takunkuman karya tattalin arziki daga ƙasashen Yamma da kuma halin da yankin Gabas ta Tsakiya ke cikin, musamman yaƙin Gaza.

  10. Assalamu alaikum

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye, barkanmu da safiyar wannan rana ta Juma'a da Hausawa ke yi wa kirari da Haji babbar rana.

    Abdullahi Bello Diginza ke jan ragamar shafin a daidai wannan lokaci, domin kawo muku irin wainar da ake toyawa a faɗin duniya.

    Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta, domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa