Sai da safe
Nan za mu rufe wannan shafin, wanda ya kawo rahotonni kai-tsaye a yau Juma'a.
Za ku iya duba ƙasa domin karanta dukkan labaran da muka wallafa a yau ɗin.
Umar Mikail ne ke cewa sai da safenku.
Labaran abubuwan da ke faruwa da Najeriya da sauran sassan duniya 05/06/2024
Daga Abdullahi Bello Diginza, da Umar Mikail
Nan za mu rufe wannan shafin, wanda ya kawo rahotonni kai-tsaye a yau Juma'a.
Za ku iya duba ƙasa domin karanta dukkan labaran da muka wallafa a yau ɗin.
Umar Mikail ne ke cewa sai da safenku.

Asalin hoton, REX/Shutterstock
An tsawaita lokacin kaɗa ƙuru'a a zagaye na biyu na zaɓen shugaban ƙasar Iran sakamakon rashin fitowar masu zaɓe a kan lokaci.
Ana karawa ne tsakanin Sa'id Jalili mai tsattsauran ra'ayi, da kuma Mas'ud Pezeshkian mai ra'ayin kawo sauyi.
Ana sa ran za a bayyana sakamakon zaɓen a gobe Asabar.
Tawagar Isra'ila ta bar Qatar domin komawa ƙasarsu don yin nazari kan batutuwan da aka tattauna a wajen taron cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza.
An ci gaba da tattauwar ne bayan da Hamas ta gabatar da sabon daftarin yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza.
Ana sa ran Isra'ilar za ta sake tura wata sabuwar tawagar a mako mai zuwa domin cigaba da tattaunawar.

Asalin hoton, Getty Images
Fadar Sarkin Musulmi a Najeriya, Abubakar Sa'ad III, ta tabbatar da cewa Lahadi ce za ta zama 1 ga sabuwar shekarar Musulunci ta Hijira 1446.
Fadar ta bayyana haka ne sakamakon rashin samun rahoton ganin jaririn watan Muharram na farko a kalandar Musulunci.
"Sakamakon haka, Asabar [6 ga watan Yuni] ta zama 30 ga watan Zulhijja 1445...Lahadi kuma [7 ga Yuni] ta zama 1 ga watan Muharram 1446," a cewar shugaban kwamatin ganin wata na fadar sarkin Musulmi, Farfesa Sambo Wali cikin wata sanarwa.
A tsarin Musulunci, kowane wata kwana 29 ne amma idan aka kasa ganin jaririn sabon wata akan cika watan zuwa kwana 30.
"Sarkin Musulmi na taya Musulmin Najeriya murna [sabuwar shekara] da kuma roƙa musu alheri da taimakon Allah," in ji sanarwar.

Asalin hoton, Getty Images
Sifaniya ta yi nasarar tsallakawa zagayen kusa da na ƙarshe a gasar kofin ƙasashen Turai ta Euro 2024 bayan doke masu masaukin baƙi Jamus 2-1.
Wannan na ɗaya daga cikin wasannin da ake hanƙoron gani a gasar ganin yadda tawagogin biyu suka zama mafiya hazaƙa, kuma wasan bai ba wa 'yan kallo kunya ba.
Dani Olmo ne ya fara ci wa Sifaniya ƙwallo a minti na 51, inda har sai da ta kai saura minti biyu lokaci ya cika sannan F. Wirtz ya farke wa Jamus.
Kazalika, 'yan ɗaƙiƙoƙi ne suka rage a shiga bugun finareti bayan cikar zagayen ƙarin lokaci Mikel Merino ya lallaɓo ya cinye Jamus da ka bayan Olmo ya bugo ƙwallo a sama.
Yanzu Sifaniya za ta jira wanda ya yi nasara a wasan da Faransa take ɓarje gumi da Portugal yanzu haka a ɗaya wasan na zagayen kwata fayinal.

Asalin hoton, Media Niger
Shugabannin ƙasashen Nijar, da Mali, da Burkina Faso na shirin yin ganawarsu ta farko a yau Juma'a.
Shugaban mulkin soja na Nijar, Abdourahamane Tchiani ne ke karɓar baƙuncin takwarorin nasa a birnin Yamai.
Shi ne taro na farko tsakanin shugabannin mulkin sojan da suka hau mulki ta hanyar juyin mulki a ƙasashensu, wanda ake yi a jajiberin wani taro da ƙungiyar Ecowas za ta yi.
Ƙasashen sun fice daga Ecowas a watan Janairun da ya gabata bayan ƙungiyar ta raya tattalin arzikin Afirka ta Yamma ta dakatar da su saboda juyin mulkin.
A madadin haka, sai suka kafa gamayyar ƙungiyar ƙawancen yankin Sahel (Alliance of Sahel States), inda suke samun ƙawancen hulɗa da ƙasashen Rasha, da Turkiyya, da Iran.

Asalin hoton, Media Niger

Asalin hoton, NYSC
Shugaban hukumar yi wa ƙasa hidima ta NYSC a Najeriya ya nemi matasan su daina wallafa ayyukan da suke yi a sansanonin hukumar a kan shafukan sada zumunta.
Da yake magana yayin ziyarar da ya kai sansanin NYSC na Ede a jihar Osun, Birgediya Janar Yushau Ahmed ya ce wallafa irin horon da suke samu ya saɓa wa tsari da dokokin hukumar.
Ɗalibai a Najeriya kan je hidimar ƙasa da zarar sun gama karatun jami'a ko kuma babbar difiloma matuƙar ba su wuce shekara 30 ba da haihuwa.
"Muna ba ku wannan horo ne domin ku dogara da kan ku, saboda kada ku dogara da aikin gwamnati," in ji janar ɗin kamar yadda kamfanin kabarai na NAN ya ruwaito.

Asalin hoton, Getty Images
Ƙungiyar manyan ma'aikatan jami'a a Najeriya ta Senior Staff Association of Nigerian Universities (SSANU) ta yi barazanar shiga yajin aiki faɗin ƙasar.
Kazalika, ƙungiyar ta ce za ta gudanar da zanga-zangar ƙasa baki ɗaya a ranar Talata mai zuwa domin matsa wa gwamnatin tarayya ta biya mata buƙatunta.
Ƙaungiyar da takwararta Non-Academic Staff Union of Educational and Associated Institutions (NASU) na tattaunawa da gwamnatin Najeriya game da albashinsu na wata huɗu da suke bin ta, wanda yanzu ta ba da wa'adin mako biyu domin biyan mambobinta.
"A matsayinmu na shugabanni, mun yanke shawarar zuwa Talata 9 ga watan Yuli rassanmu za su shirya zanga-zanga a ƙasa baki daya domin faɗa wa duniya irin matsalolin da ake fuskanta, kuma za a yi a dukkan makarantu," in ji shugaban SSANU Mohammed Ibrahim yayin hirarasa da Channels TV a yau Juma'a.
Ya ƙara da cewa "daga baya kuma za mu ci gaba da tattaunawa, sai kuma mu sake yin babbar zanga-zanga a Abuja ranar 18 ga watan Yuli, inda za mu yi wa ma'aikatun ilimi da ƙwadago tsinke".

Jim kaɗan bayan rantsar da shi a matsayin sabon firaministan Birtaniya, Keir Stamer ya bayyana mutanen da ya naɗa a matsayin ministocin gwamnatinsa.
Fadar Downing Street ta bayyana sunayen wasu daga ciki kamar haka:
An fito da gawar wata mata daga cikin wata mesa a ƙasar Indonesiya.
Duk da cewa ba kasafai mesa kan haɗiye mutane ba, amma wannan ne karo na biyu da aka samu irin haka a ƙasar.
Hukumomi na cewa lalata dazuka ne ke tursasa wa macizai yin farautar mutane.

Mataimakin Shugaban Najeriya Kashim Shettima ya ƙadammar da shirin gina rukunin gidaje da makarantu da asibitoci da aka yi wa laƙabi da Pulako a garin Tudun Biri da ke jihar Kaduna.
Yanki ne da sojojin ƙasar suka kai wa hari ta sama bisa kuskure a bara, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane da dama.

Wakilin BBC da ya halarci bikin ya ce tuni aka kusa kammala masallaci a garin tare da cibiyar koyar da sana'o'i, waɗanda mataimakin shugaban ƙasar ya buɗe a lokacin bikin.

Gwaman Kaduna Uba Sani ya ce gwamnatinsa ta kashe fiye da naira miliyan 270 domin tallafa wa al'umomin garin na Tudun Biri tun bayan faruwar iftila'in na bara.

Taron ya samu halartar gwamnan jihar jigawa, da wakilan gwamnonin jihohin Kano da Katsina, da wasu 'yan majalisar dattawa da na wakilai, da sauran manyan baƙi.


Asalin hoton, AFP
Rahotanni daga ƙasar Habasha na cewa wasu mutane ɗauke da makamai sun sace ɗaliban jami'a da dama a yankin Oromia da ke fama da rikici a ƙasar.
Yankin Oromia ya kasance filin fafatawa tsakanin sojoji da 'yan tawaye.
Daliban na kan hanyarsu ta komawa gda bayan tashi daga makaranta a yankin Amhara na arewacin Habasha, lokacin da masu ɗauke da makaman suka tare su.
Sauran ɗaliban da suka tsakkale rijiya da baya a harin sun ce ‘yan bindigar, sun yi garkuwa da mutane fiye da 100.
Wani da ya ce ‘yar uwarsa na cikin waɗanda aka kama ya shaida wa BBC cewa ‘yan bindigar sun buƙaci a ba su dubban daloli domin a sako ta.
Jami’ar daliban ta ce ta samu rahoton sace ɗaliban amma ba ta bayar da cikakken bayani ba.
Satar mutane domin neman kuɗin fansa ya ƙaru a Habasha.
Hukumomi ba su ce komai ba kan lamarin.

Asalin hoton, Reuters
Mutanen da ke sa ran samun muƙaman ministoci a sabuwar gwamnatin Birtaniya ƙarƙashin jagorancin sabon firaminista Sir Keir Stamer na ci gaba da hallara a fadar gwamnatin.

Asalin hoton, Reuters
Ana sa ran nan ba da jimawa ba Mista Stamer zai sanar da manyan ministocinsa ciki har da sakataren Shari'a da Tsaro da na lafiya.

Asalin hoton, Reuters
Shabana Mahmood 'yar jam'iyyar Labaour na daga cikin sabbin ministocin sabuwar gwamnatin

Asalin hoton, Reuters

Asalin hoton, POOL
Yvette Cooper na daga cikin na gaba-gaba a jam'iyyar Labour da ke fatan zama sabuwar minista

Asalin hoton, Getty Images
Sir Keir Starmer ya zama sabon Firaiministan Birtaniya bayan jagorantar jam'iyyar Labour zuwa ga gagarumar nasarar da ta samu a zaɓen da aka gudanar a ƙasar.
Keir ya maye gurbin Jeremy Corbin a matsayin jagoran jam'iyyar Labour ne shekara huɗu da suka gabata, kuma tun wancan lokacin ne ya yi ta fafutikar ganin jam'iyyar ta ƙara samun goyon baya daga al'umma.
Jam'iyyar Labour ta kwashe shekara 14 ba tare da ta jagoranci gwamnati ba a Birtaniya.