Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Gasar kofin duniya 2026: Ingila za ta kara da Mexico a zagayen ƴan 16

Takaitaccen Bayanin Wasa

Gasar Kofin Duniya
- Zagayen ƙasashe 32
England 2 , Congo DR 1 at Full time
Ingila
Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo
Full time
Hutun rabin lokaci Ingila 0 , Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo 1

Key Events

Ingila

  • H. Kane Goal 75 minutes, Goal 86 minutes

Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo

  • B. Cipenga Goal 7 minutes
Ba da ƙwallo a ci
Ingila,A. Gordon (75 minutes, 86 minutes)
Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo,C. Mbemba (7 minutes)

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu da taimakon AI

  1. , Ingila 0-1 DR Congo

  2. , Ingila 0-1 DR Congo

    Ingila ba ta ci wasa ko daya ba daga cikin 13 da aka fara cinta kwallo a gasar cin kofin duniya ta Fifa, tun lokacin da ta yi nasara a kan Jamus a ranar 30 ga watan Yulin 1966 a gasar cin kofin duniya.

    Wannan ba tarihi ne mai kyau ba a bangaren Ingila.

  3. , England 0-1 DR Congo

  4. , Ingila 0-1 DR Congo

    Tun farko abin da Ingila ke tsoro a fara zura mata kwallo, kuma abin da ya faru kenan - koda yake da sauran lokaci sosai za ta iya yin wani abin, wato ta farke ta kuma nemi karawa, amma da akwai kalubale a fara cinka a wasa.

  5. GOAL - England 0-1 DR Congo, Brian Cipenga

    Kwallo mai kyau da DR Congo ta ci ta hannun Cipenga da aka bugo daga dama zuwa hagu, daman yana cikin gidan Ingila ya take ya kuma sa kafar dama ya buga da karfi daf da turke ta fada ragar Ingila.

  6. , England 0-0 DR Congo

    Wasa hudu ne kacal da Ingila ba ta lashe ba daga 17 karkashin Thomas Tuchel da canjaras biyu da rashin nasara biyu.

  7. An fara wasan tsakanin Ingila da DR Congo, Ingila 0-0 DR Congo

    Za su fara buga minti 45 daga su je hutukanin nan akwai hutun shan ruwa saboda yanayin zafi daga nan a karasa zangon farko.

    Ana fara zuwa hutun shan ruwa daga bayan minti 20 da take leda koda wane lokaci alkalin wasa zai busa usar a je shan ruwa.

  8. , Ingila v DR Congo

  9. Daf ake da taka leda, Ingila v DR Congo (

    Daf ake da faran wasan - Wa zai kai zagayen yan 16 tsakanin Ingila da DR Congo? Lokaci dai

  10. Ana taken kasa da kasa, Ingila v DR Congo

    Tuni yan wasa suna tsakiyar fili ana take kasashen biyu daga nan yan wasa su gaisa a tsakaninsu, sannan a take leda.

  11. An fara yayyafin ruwa, amma saman filin wasan Atlanta a rufe yake, Ingila v DR Congo

    Saman filin wasa da ke Atlanta yana rufe kenan babu matsalar zubar ruwa ko iska, ana sa ran za a gara leda yadda ya kamata.

  12. Yadda DR Congo ta samu zuwa matakin ƴan 32?, England v DR Congo

    DR Congo ta kai zagaye na 32 a gasar cin kofin duniya ta 2026 ta hanyar kammala a matsayin daya daga cikin tawaga mafi kyau ta uku da maki hudu a rukunin 11, inda ta tsira daga manyan abokan hamayya a Uzbekistan da Colombia da kuma Portugal.

    Leopards ta fara ne da 1-1 da Portugal, sai ta yi rashin nasara 1-0 a hannun Colombia, sannan ta doke Uzbekistan 3-1 a karawar karshe a cikin rukuni.

    ɗaya daga cikin rukunin da aka fi so kuma sun sami maki mai mahimmanci.

  13. Ta yaya Ingila ta kai zagaye na 32?, England v DR Congo

    Ingila ta kai zagaye na 32 a gasar cin kofin duniya ta 2026 ta hanyar lashe rukunin 12 da maki bakwai.

    Three Lions ta fara da nasara mai ban sha'awa 4-2 a kan Croatia, wasan.

    Wasan na biyu, 0-0 da Ghana, Sannan ta yi nasara 2-0 a kan Panama a karawar karshe

  14. Ana zafi a birnin Atlanta, amma ba zai hana a kalli wasan ba, England v DR Congo

  15. Tuchel na fatan kafa tarihi a gasar kofin duniya, England v DR Congo

    Ingila ba ta yi rashin nasara ba a dukkan wasa 11 da ta buga a karkashin Thomas Tuchel (ta lashe 10 da canjaras daya).

    Ron Greenwood, ya ja ragamar wasa 16 ba tare da an doke Ingila ba tsakanin 1977 zuwa 1980, da Roy Hodgson, wanda ya ja ragamar wasa 14 tsakanin 2012 zuwa 2013, sune kan gaba a yawan jan ragamar Ingila ba tare da rashin nasara ba, amma banda bugun fenariti.

    Nasara a kan DR Congo zai sa Tuchel ya tsawaita wasa 12 a jere kenan ba tare da rashin nasara ba.

  16. Kane na fatan kafa wani tarihin a gasar kofin duniya, Ingila v DR Congo

    Harry Kane ya riga ya zama dan wasan Ingila da ya fi kowa zura kwallaye a tarihin Gasar Cin Kofin Duniya ta FIFA, inda ya ci 11. Sai dai yana da damar kafa wani sabon tarihi idan ya zura kwallo a wasan da Ingila za ta buga da Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo (DR Congo).

    Idan Kane ya ci kwallo a wannan wasa na zagayen ƴan wasa 32, zai yi kan-kan-kan da tarihin Geoff Hurst na cin kwallaye hudu a wasannin ziri daya kwale (knockout stages) a Kofin Duniya.

    Dan wasa guda daya ne kawai ya fi su yawan cin kwallaye a irin wadannan a Ingila, wato Gary Lineker, wanda ya zura shida a raga.

    Tambayar ita ce: Shin Harry Kane zai kara habaka tarihin cin kwallayensa a Kofin Duniya ta hanyar zura kwallo a karawar da DR Congo? Idan ya yi hakan, zai kara kusantar karya wani muhimmin tarihi a tawagar Ingila a gasar.

  17. , England v DR Congo

    Tawagar Ingila ta yi canjin yan wasa ukun da suka fuskanci Panama a wasan karshe a cikin rukuni, cikin waɗanda ta saka a karawa da za ta yi da DR Congo sun hada da Djed Spence da Declan Rice da kuma Noni Madueke.

    Jarell Quansah yana jinya, an ajiye Morgan Rogers da kuma Bukayo Saka.

    Ƴan wasan Ingila 11 da za a fara wasa da su: Pickford; Spence, Konsa, Guehi, O’Reilly; Rice, Anderson; Madueke, Bellingham, Rashford; Kane

    Shi kuwa, Sebastien Desabre canji daya ya yi a tawagar DR Congo da ta fuskanci Uzbekistan.

    Ngal'ayel Mukau ya shiga ya kuma maye gurbin Cedric Bakambu.

    Ƴan ƙwallon DR Congo 11 da za a fara wasan da su: Mpasi, Masuaku, Tuanzebe, Mbemba, Wan-Bissaka, Sadiki, Moutoussamy, Mukau, Cipenga, Wissa, Mbuku.

  18. Kane da sauran tawagar Ingila sun isa filin waa, Ingila v DR Congo (17:00 BST)

  19. , Ingila v DR Congo

  20. Labarai da dumi-dumi, , Ingila v DR Congo

    Ana sa ran kociyan tawagar Ingila, Thomas Tuchel zai fara wasan da Djed Spence daga gefen dama a matakin mai tsaron baya, saboda raunin da Reece James da kumaJarell Quansah suka ji.

    Ana sa ran za a fara fafatawar da Declin Rice, bayan da ya murmure daga dan karamin rauni, yayin da Noni Madueke zai maye gurbin Bukayo Saka daga gefen dama daga gaban fili.

    Ana sa ran Marcus Rashford zai ci gaba da taka leda daga gefen hagu daga gaban fili.

    Ƴan Ingila 11 da ake sa ran fara wasan da su a fili: Pickford; Spence, Konsa, Guehi, O’Reilly; Rice, Anderson; Madueke, Bellingham, Rashford; Kane